BAKAR WASIKANOVELS

BAKAR WASIKA 6

“Yayanka sun fika jarumta Malam”

“Wannan ba maganar Jarumta bace, magana ce marar dadi, kuma da na san abun da zaki fada kenan da ban shigo gidan nan yanzu ba”

Ya karasa yana kai hannunsa aljihu ya ciro wayarsa dake ringing. Ya kara wayar a kunne tare da sallama sai dansa Bashiru ya amsa ta dayan bangaren…

BATURIYA POV.

Tana tsugune gaban murhu tana suyar naman kajin suka ji an kwankwasa gida. Ta kalli danta shi ma ya kalleta.

“Ko Abba ne?”

A take ta daka masa tsawa.

“Ban ce ka daina cewa Abbah ba?”

Sultan yayi saurin rufe bakinsa.

“Daddy”

“Good”

Ta mike tsaye tana mita.

“Wata kila ma yaran nan su Saifu sarakan kwadayi tun da sun ji an soyar abu kamshi ya kawo musu, shiyasa zama irin wannan area ta talakawa sai dole Wallahi”

Ta kai hannu ta bude kofar sai arba tai da kawarta Ramlee, a take ta washe baki, Ramlee ta sakar mata murmushi tana wani irin kamshin turare irin na manyan masu kudi.

“Yau gidanmu?”

“Sai kace ban saba zuwa gidanmu ba”

Ta fada a yayinda Baturiya ta kauce mata ta shigo.

“Ki ce yau na shigo a sa’a kaji ma kuke ci, lallai Faruq yayi abun kai”

Ta fada ta zigar zolaya da bugun ciki tana kallon Baturiya. A take Baturiya da bata shaye rada ta tsire baki tace.

“Kina magana kamar baki san wa nake aure ba, Faruq din ne zai kawo min kaji?”

“Ah gaskiya idan fa yana da shi yana yi”

“Idan yana da shi kika ce, ke dai zauna na kawo miki ruwa”

Baturiya ta mika mata kujerar da take zaune dazun, ita kuma ta karba ta zauna tana karewa gidan kallo kamar bakonta, ko gaisuwar da Sultan yake mata bata ji.

“Baturiya kenan duk kyau nan naki kika kare a gidan nan”

Baturiya ta aje mata ruwan a cup tana fadin.

“To ya iya, kaddara rayuwa ta kawo ni nan”

“Kika dai kawo kanki, ke kika so ai”

“Hmmm Wallahi Ramlee babu irin cin mutunci da ban masa ba, amman yaki ya sake ni”

“Ina ko zai sake ki, tun da be da kudin auro wata, kuma ya san yadda kike da kyau nan kina cika idda wani mai kudi zai aureki”

“Da gudu ma, ni Wallahi ban taba zaton zan yi rayuwa a haka ba, bawan Allah nace masa idan mun yi aure zan cigaba da karatu yace ya yarda zai dauki nauyin komai, sai gashi abincin ma wannan wahala yake mana”

“To miya hana shi?”

“Ai lokacin da na aureshi karatu yake, ni na dauka, yana gama karatu zai samu aiki mu fancama yadda muke so, ashe ashe wahala ce ke kirana, gashi gurin auren ma sauki aka masa tun da auren gida ne, kawaye da muka gama secondary school a tare daga mai aure wani shege sai mai aiki a guri kaza ni ina nan zaune a wani shegen gidan duk yabi ya rugube, kuma na haya”

Tana kai aya Ramlee ta saka mata dariya.

“Ke kika so Baturiya, tsabar kyau fa Baturiya ake ce miki, gashi manyan mutane suna son farar mace, Wallahi ba ki ga yadda mutumen ya haukace daga ganin hotonki ba”

Baturiya ta nufi namanta ta juya tana fadin.

“Ke ni fa Ramlee duk iskancina ba zan iya zina ba”

“Su kuma manyan mutane ai sun fi son matan aure saboda sun fi Sirri, wasu kuma ba sai kin fada musu cewar kina da aure ba, ki ga abun da be wuce 30-1hour ba an baki kusan 500k ko 300k”

Baturiya ta juyo tana kallonta tana zaro ido.

“Da gaske wai?”

“Wallahi kuwa, ke auren ma ba rufi asiri ba ne a gareki, wanda ta haihu har wani tsoron fadawa maza take ma, kara ma budurwa ace ko dan gaba, amman ke fa? Kuma ko kudi aka ganki da shi za a ce na mijinki ne”

“Tab humm ai sun san bakiri nake aure, shi kansa idan ya gan ni da wannan kudi sai ya tambaya ina a samo”

“Ki ce tallafi ne kika samu, daga nan sai ki kirkiri sana’a ki fara yi, kin ga idan ma wasu sun shigo ba za a zarge ki ba, Wallahi cikin Shekara daya Fee’ah har makka sai kin je, kuma duk abun da kike so zaki siya a duniyar nan”

Baturiya ta dawo kusa da ita ta zauna.

“Amman su wani irin kudin banza ne da su haka?”

“Masu kudi fa aka ce miki Baturiya, kina irin wannan area ko’ina kwata ai dole ki yi mamaki, da zaki yarda zan hada ki manya manyan yan kasuwa da yan siyasa, kuma ba haka nan ake zuwa musu ba ai, sai an gyara ki an shirya, ta yadda zai ji kamar be taba kusantar wata mace ba”

“To shi zunubin zaki daukar min?”

Baturiya tai mata tambayar rainin wayo. Sai Ramlee tai murmushi tana mikewa tsaye.

“Baki ji matsi ba ne yarinya, kin san da Allah kika chat da maza a facebook? Har kina haduwa da su kina karbar kudinsu”

“Wannan ai dabam, ban aikata ba sai dai na yi musu dadin baki”

“To yayi kyau ki cigaba”

Ta saka hannunta a jaka ta ciro 10k ta mikawa Sulta.

“Sultan a siye minti ka ji, ni bari a dauki naman tun da ba za a min ta yi ba”

Ta karasa gurin naman ta saka hannu ta dauka ta kai bakinta, Baturiya ta yi murmushi.

“To ai ke dince kika dauke min hankali ”

Bata sake ce mata komai ba ta nufi kofa, Baturiya sai kallo tsadadden lace dinta take, sai da ta fita sannan ta juyo.

“Ni baki ma fada min ina kika samu nama ba, ko wani aka yaudara”

“Wannan karon roka na yi”

“Uhm wata rana dai zasu roki abun da baki so”

“Ai da zarar na ga mutum da ruwan haka, sai na zubar da shi na kama wani”

Ramlee ta yi dariya ta juya ta kama Hanya Baturiya kuma ta rufe gidan ta nufo gurin yaronta Sultan ta karbe kudin da Ramlee ta bashi.

“Karka fadawa Daddy ka ji?”

“Toh”

Ya amsa ta yana kai hannu ya dauki cinyar kaza. Sai bayansa sallah isha’i Faruq ya shigo gidan, ba laifi ya samu masu haske har ya hada 500, tun da ya ji kofar gidan a bude ya tabbatar matarsa na cikin nishadi, domin idan tana jin rashin mutunci wani lokacin rufe gida take saboda yai ta wahalar kwankwasa a waje.
Bayan ya shigo ya maida kofar gidan ya rufe, kamin ya karasa falon ya so ma jin waka ya tashi, ko kwankwato babu matarsa na cikin nishadi a yau. Sallama yai ya shiga ta amsa masa kamar ba ita ba.

“Sannu da zuwa”

Ya dan tsaya kallonta kamin ya amsa.

“Yauwa, ya gidan”

“Alhamdulillah”

Ya zauna saman kujera yana kallonta.

“Mun samu wani abu ne kike ta nishadi haka?”

‘Tun da a sanadinka aka samu ai za a sammaka’

Ta fada a ranta a fili kuma sai ta mike tsaye tana fadin.

“Uhm wasu yan kudi ne na samu shi ne na siyo kaji na soya mana”

Daki ta shiga ta debo masa a platecikin wanda ta soya ta kawo masa ta aje a gabansa.

“Ina kika samu kudi?”

Ya tambaya yana kallon naman da zai rabin kaza.

“Allah ya ba ni”

Ta amsa masa bayan ta zauna.

“Haka kawai Allah zai baki kudi daga sama ba ta dalilin wani ba?”

“Allah ne ya ba ni”

“Ki dauke namanki, ki kawo min abinci, ba zan ci abun da ban san inda aka samo shi ba”

“Matsalar talaka kenan ai, ga talauci ga girman kai, yaushe rabon da mu ci nama a gidan nan?”

“Ba mu kadai ne a cikin wannan halin ba Rafi’ah, mutane da yawa suna ciki, mutane da yawa a da da kika san suna ci uku a wuni wssu yanzu biyu suke wasu daya, amman idan muka yi hakuri komai zai wuce, na san kina cikin hali Rafi’a, saboda kina ganin yan’uwanki da kawayenki a ciki wadata, hakan ba yana nufin Allah ya manta da ke ba, da ya ga dama da sai ya aura miki wanda yafi kowa kudi a duniya, amman ya jarrabaki miyasa ba zaki yi hakuri ba?”

“Faruq kenan, yanzu duk hakurin da na yi na shekara biyar baka gani ba?”

“Kin yi hakuri na sani, amman fadar sirrin gidana yafi komai yi min ciwo, idan na ci ko ban ci ba wani ya sani abun na min ciwo, bana son ki fada wani hali saboda halin da muke ciki dan Allah ki yi hakuri”

Previous page 1 2 3 4Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button