BAKAR WASIKA 8

“Na fasa zuwa shopping din take me home”
Sai a lokacin ya kalleta tare da kiran sunanta.
“Leila…”
Ta kalleshi Irin duban nan na fusata, sai dai kwarjininsa ya hanata nuna masa fushinta.
“I’m not your driver, and this should be the last time da zaki umarce akan wani abu”
“Amman ni dazun ka cilasta ni na bawa Baaba hakuri bayan kuma bata cancanci haka ba”
Ta fada idonta na cika da kwalla.
“Me ka dauke ni ne Talba? Baiwa?”
Be amsa ta ba, ya juya motar zuwa gida, kamin su isa hawaye da ya wanke mata fuska ya fi a kirga, yana yin farkin ta bude motar ta fita tana share hawayenta. Sai a lokacin ya juyo da fuskarsa yana kallonta har ta danna door bell din aka bude mata ta shige, sannan ya maida dubansa gurin Daddy dake tsaye jikin motarsa yana magana da Momy da gaba daya hankalinsu yake kan Talba.
Bude motar yai ya fito ya rufe ya nufi gurin da Daddy yake tsaye yana wata irin tafiya kamar baya son taka kasa, kamin ya karasa ya zuba hannayensa aljihu kana ya sadda kansa kasa.
“Ranka ya dade baka burge ni ba, da baka tura Leila gida gurin Gwaggo ba”
Daddy ya fada yana kallon dansa, sai Talba ya kalli Daddy, kamin ya maida dubansa gurin Momy wanda hakan kr tabbatar masa da cewar Momy ta fadawa Daddy abun da yai ma Leila kenan.
“Momy ba zamu iya yin abu a tsakaninmu ba har sai Daddy ya ji?”
“Yes, ya kamata ya ji ne, saboda kana kokarin wuce guri”
“Just because…”
“It’s just because? Tun ba yau ba Talba kana treating Leila kamar ba yar gidan nan ba, ya kamata ka sani ita ma tana da right fa!”
“Miyasa karamin Abu zai bata miki rai Momy?”
“Kai kaja komai, wacan yar aikin ma dana kora saboda kai na koreta Talba, saboda kana nuna kamar ta fi Leila gata a gidan nan, and now kana son na kori Baaba ko? Ka cigaba”
Tana kaiwa nan ta nufi hanyar da zata sadata da bangarenta, daga Daddy har Talba kallonta suke har ta shige, sannan Daddy Talba ya ce.
“Ka saba da halin Momy ka ba tun yau ba, kar hakan ya dame ka”
Talba yayi murmushi.
“Daddy fita zaka yi?”
“Yeah zan je gaisuwar Galadima ne”
“Lemme drive you”
“No tare da direba zamu je, go and rest”
Murmushi ya sake yi ya dan ja baya, ya budewa Daddy motar sai Daddy ya shiga yana fadin.
“Ance an kai hari Galadi, ya kamata A shirya wani abu a kai musu, mutanen nan suna cikin matsi”
“Inshallah Daddy, ban ji ba two days ban duba news ba”
“Sai na dawo”
“Allah ya kiyaye”
Ya fada yana rufe masa motar, sannan yaja ya tsaya har sai da driver ya ja motar Daddy suka fice daga gidan. Sannan ya nufi bangarensa, daga shi har Faruq da part dinsa yake kusa da nasa a kasa dakunansu suke, tsabanin bangaren Daddy da Momy da akai yi ma upstairs.
Dakin da yake aje tardunsa ya nufa ya bude ya shiga cikin natsuwa ya zauna a kujera ya bude system dinsa ya cigaba da wani aikin da be karasa ba, be bar dakin ba sai kusan 6pm.
Freezer ya nufa ya bude ya dauko ruwa ya zuba a cup ya surka da wasu sannan ya sha, bayan ya ajr cup din ya nufo kofar fita yana duba agogon hannunsa. Kai tsaye bangaren Momy ya nufa domin ya san izuwa yanzu ta huce fushin da take. Door bell din ya danna, yana dauke hannunsa Amal ta bude masa da sauri hawaye na sauko mata.
“Lil Sis?”
“Na’am?”
“Me ya same ki?”
Ya tambaya a yayinda ya saka kafarsa cikin falon yana dubanta.
“Baaba ce…”
Sai kuma tai shiru, shi dai kallonta kawai yake, as she knows ba zai sake tambayarta ba sai ta soma labarta.
“Tana mopping sai ruwa ya zame ta ta fado…”
Wani irin kallo tsoro yai mata.
“Ta fado ina?”
“Daga sama ta fado kasa!”
“You’re kidding me”
“No Wallahi da gaske nake”
“Ina take? Ta ji ciwo?”
“Momy ta dauke ta sun tafi asibiti tare da Ya Leila tun dazu ba su dawo ba”
“Yaushe abun ya faru?”
“Lokacin da Daddy ya fita”
Ya juya da sauri ya fita zuwa bangarensa domin a can ya baro wayarsa, yana shiga ya koma dakin karatunsa ya dauki wayar ya kira Momy, ringing tai sai da ta kusa tsinkewa sannan ta daga.
“Momy kuna ina?”
“Gamu hanyar dawowa gida”
“Ina Baaba?”
Dan Jimm Momy tai kamin ta amsa masa.
“Yaranta sun zo sun dauketa, sun tafi da ita, daman ciwon ba sosai ba ne”
“Amman…”
Be karasa ya lumshe idonsa sosai jin Momy ta katse wayar, hakan nan jikinsa ya ba shi kamar ba iya haka ba ne. Idan har ba babban abu ba ne, babu yadda za ayi Momy ta kaita asibiti da kanta, kuma har Leila ta bi ta su tafi tare.
AMINATU POV.
Tun safe take ta wanke tufafin Baba da nata har kusan daya da tabi, abun ka da marar aiki da kuzari, bata da kuiyar aiki kam amman bata da sauri, sai wuni ta kwana tana abu daya.
Bayan ta wanke su fes ta matse ya daurewa ta soma sha shayawa, sannan ta bi tana kwashe wadanda ta shanya da farko suka bushe tana ninkewa, sai ta dora akai da haka har ta gama kwashe ta kai su daki, sannan ta fito ta shanya sauran. Ta dauke kayan da tai aikin da su cike da gajiya ta aje a inda suka saba ajewa.
“Inna tashi ki yi sallah”
Ta fada tana doso dakin, har zata shiga sai kuma ta juya ta dauki butar Inna ta cika da ruwa sannan ta nufo dakin, bata sake ce ma Inna komai ba har sai da jera tufafin Baba a inda ta saba saka masa sannan ta nufo inda Inna take zaune ta sadda kai kasa ta.
“Inna…”
Jin bata amsa ba yasa ta risina a hankali ta leketa, sai ta ga idonta a rufe, da sauri ta taba ta abunka da wanda yai nisan bachi sai ta zabura da karfi ta bude ido, da wanin irin karfi Aminatu ta hade yawu ta sauke ajiyar zuciya.
“Inna anyi sallah, yi hakuri na tashe ki da karfi tsoro na ke ji”
Sai Inna tai mata murmushi, sannan ta fara yunkurin tashi Aminatu ta kama ta ta mike tsaye, da taimakon Auta ta fito waje ta shiga bandakin, bayan ta fito ta rika mata butar tai alwala, sannan shimfida mata tabarma da abun sallah ta dauko mata hijabi.
“Allah ya miki albarka”
“Amin”
Ta amsa tana kokarin rikata ta zaunar da ita, domin a zaune take sallah, saboda bata iya dadewa a tsaye. Sai da Inna ta fara sallah sannan ta dauki butar ta shiga bandaki bayan ta fito tai alwala ta zo kusa da Inna ta yi sallah, babu komai a cikin addu’ar sai nemawa Inna lafiya, domin shi ne abun da yafi komai tsaya mata a rai a yanzu.
Kamar kullum bayan ta gama ta dora girki, sannan ta matsawa Inna furarta ta jiya ta bata. Baba be shigo ba sai bayan sallah isha’i.
“Sannu da zuwa Baba”
“Yauwa”
Ya amsa yana sauke gajiya, kamar wanda ya wuni yana aiki, daman can haka yake tun da tsufa ya kama dan abu kadan sai gajiya ta tarar masa. Aminatu ta tashi da sauri ta dauko masa abinci da ruwa ta aje masa.
“Allah ya miki albarka”
“Amin Baba”
Ta amsa tana jindadi albarka da suke yawan saka mata, ta san ko ba yau ba wata rana albarka nan zata bita.
“Baba na wanke kayanka fes na ninke maka”
“Eyeee Auta gayyar aiki, Allah kara miki albarka yar Baba”
“Amin”
Ta amsa tana murmushin data manta rabon da ya ziyarci kumatunta, Inna ma murmushin take tana kai hannu ta rage hasken fitilar dake kusa da ita.
“Yau da wuri za’ayi bachi ko? Dan a san akwai gajiya”
Cewar Inna tana kallon Aminatu, fuskarsa sai haske take duk da kasancewar dare ne, sai dai dan hasken farin wata daya haska ta da kuma fitilar dake kusa da ita yasa duk wanda ya kalleta zai yi arba da yadda fuskarta take ta haiba.
“Jikina yau Alhamdulillah ji nake kamar ba ni ba”
Baba yayi murmushi yana kallon Aminatu wanda ita ma murmushin take.