BAKAR WASIKANOVELS

BAKAR WASIKA 8

“Ai na ga alama ga annuri nan a fuskarki”

Ta sake fadada fuskarta da murmushi tana amsa sallamar da Isah yai, kusa da Baba ya zauna sannan ya aje mata ledar yalo a gabanta.

“Ga tsarabar kasuwa”

“Allah ya maka albarka”

“Amin”

Ya fada kamin ya dora da amsa tambayar da Baba yake masa.

“Wallahi kasuwa Baba taki ta koma kamar da, kowa a tsorace yake, saboda ana ganin mutanen nan kamar za su iya dawowa, kasan idan suka saka gari agaba sai sun ga bayansa, musamman garin da da suke da dade suna dafafe, tun da ba a taba shigo mana ba sai yanzu, gashi daman yan saka kai na yankin nan sun sha kashe mutane suna da haushin garin nan sosai”

“Allah dai ya tsare, abun da Bashiru yake ta ce min kenan kullum, ga shi tsohuwar ta ku ta ki yarda mu bar nan”

Cewar Baba.

“Ku bar ni na mutu inda uwaye na da kakanina suka mutu, ai ba a tsirewa mutuwa”

“Amman inna idan mu ka bar garin nan ke kanki hankalinki zai fi kwanciya fiye da nan”

Amina ta fada, a karon farko kenan da ta saka bakinta a maganar. Sai Inna ta girgiza kai.

“Babu inda zanje, kina ganina ko tafiya bana iyawa miya rage min Allah na tuba”

“Mai ciwo da mai lafiya, duk daya ne a gurin Allah, sai kaga mutuwar ta dauke mai lafiya ta bar mai ciwo ai”

Ta daga ma Baba hannu.

“Dan Allah ku daina min maganar nan, ni ban hana ku tafiya ba, amman ni kam ba zan bar garin nan ba”

“Allah ya kyauta”

Duk suka amsa da Amin har ita. Ko da goma tai duk sun kwanta Inna da Aminatu suna daki, Isah da Baba kuma suna waje saboda garin akwai alamun hadari hakan yasa zafi ya tsananta, sai dai hakan be saka Inna fitowa ta kwanta waje, Aminatu kuma duk inda Inna take tana nan. Kowa yayi bachi ban da Aminatu dake ta tunanin abubuwa da dama ciki har da wasikar ta ta karshe da ta bawa Maniru shi ma ya bata, babu yadda be yi ba akan yana son tai masa iso gurin iyayenta ta hana shi saboda tana jin tsoro, ashe ba rabon gaisuwa da shiga tsakaninsa da iyayenta. Sai a yanzu take jin zafin mutuwarsa, kuma take ganin laifin kanta na hana shi ganin Babanta da tai. Ba shiri tai firgigit ta tashi zaune sakamakon kara bindigar da taji, a da can yan saka na yanki su kan harba bindiga idan dare yai, shi ma kuma ba kullum ba, sai dai tun bayan harin da aka kawo musu aka kashe wasu wasu suka tarwatse sai aka daina harbawar, ba ta hadda karar wacan bindigar da kuma ta yan ta’adda ba, balle ta iya banbanci ta su da kuma ta yan sa kai, sai dai yanayin yadda take ta jin tashin bindigar babu kakkautawa yasa hankalinta ya tashi sosai.

“Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un”

Daga waje ta ji muryar Baba yana neman agajin Allah. Kamin su soma jiyo hayaniyar mutane da alama gudu tsiratar da rai suke, Baba ya shiga dakin da sauri ya haske fitilarsa ya bude inda yake ajiyar kudi ya kwashe su ya saka aljihu.

“Aminatu rikata tashi mu tafi yan ta’adda ne”

Kamar an zare mata lakka haka Inna ta ji, sai jikinta ya kara nauyi, Aminatu ta shiga kokarin rikata da sauri amman ta kasa.

“Tu tafi Malam, ku gudu ko dan saboda Aminatu”

Aminatu ta girgiza mata kai da sauri tana kuka.

“Ba zan tafi na barki ba Inna…”

Ta shiga kama Inna da dukan karfinta tana jin kamar ace tana da karfin da sata iya daukarta ta dora akai, sai gashi tsaye ma ta kasa mikar da ita sai da Baba ta rika mata dayan bangaren, sun mikewa tsaye suka ji harbin kamar a bayan dakinsu, wani kuma a cikin gidansu.

“Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un”

Baba ya fada yana sako fitsari a wando sai kuma ya fara rawa yana tsalle kamar wanda ya tabu.

“Allah ka batar da ni, Allah ka batar da ni kar su gan ni”

A take cikinsa ya murda sai zawo, abun ka da mai tsoro sai yai cikin tufafinsa na sakawa ya tura kansa sauran jikin a waje, ga wandonsa sharkat da zawo da fitsari. Inna kam gaba daya hankalinta yana gurin Aminatu. Da hannu ta nunawa Aminatu karkashin gadon karfi alamar ta shiga domin bata ko ina magana. Da gudu Aminatu ta nufi karkashin gadon kamin ta karasa shigewa suka shigo dakin rike da magayen makamai, ga wata uwar fitila mai dan karen haske da suke haska ko’ina da ita kamar gulub. Dayan ya turo Isah cikin dakin da karfi, sannan ya karasa karkashin gado ya daga daga katifar ya jefar can gefe, sai ga Aminatu dunkule.

“Fito ko na halbe ki”

Dayan ya fada, da Aminatu ake sai dai tsabar tsoro yasa Baba ya ji kamar da shi ake, sai ya cire kansa cikin jakar kayan ya rarafo kusa da Isah yana ta kuka da karanta addur’ar da ta zo masa.

“Yanarukuna bardan wassalamu ala ibrahim”

Daga nan ya dora ta ayatul kursiyu, kamin su daka masa tsawa ya kama bakin ya rike jikinsa ta ko’ina rawa yake. Wani irin rawa jikin Aminatu yake tana ganin komai kamar ba gaske ba, yadda take fita da shigar da numfashinta kadai ya isa ya bayyana irin tsoron da take ji.

“Dan Allah karku taba ta, ku kashe ni ita ku kyale ta”

Inna ta fada, sai dayan ya saka bakin bindigarsa ya buga mata a kai, take gurin ya fara zubar da jini.

“A kyale ta ita tafi sauran yaya ne? Kuna son ta kuka ja mata masifa ba kuri kuke ku kuna da jarumai a gari ba? Yayanka sai kashe mu suke duk inda suka ga bahillace sai ku kashe shi, Wallahi yau ko wa ba mu bari garin nan”

Cewar wani tsukaken a cikinsu yana rike da ak47. Ko kamin ya karasa maganar har wani ya fara yaga tufafin Aminatu, a take ta fashe da kuka tana kiran sunan Inna tana jin kamar ace Inna ko Baba wani zai iya taimakonta.

“Dan Allah ku kashe ni, ba zan iya ganin wannan abun ba…”

Inna ta fada a rikece tana kallon Aminatu take ta kuka suna kokarin rabata da zanenta.

“Kai bata giďa”

Wani ya fada a take na kusa da kofa ya dauke ta da bindiga har harbi hudu. Wani irin ihu Aminatu ta saka jikinta na rawa idonta kamar zai zubo tana kallon gawar Inna dake kwance tana zubar da jini ido a bude, tassss wani ya dauke ta da mare wanda ya saka ta a take ta manta inda take, duniya ko lahira? Ba suma tai ma, sai dai jinta yayi karanci kamar yadda idonta suke ganin haske wutar marin da akai mata, sai dai ko kadan hankalinta be yi nisa da jikinta ba.

“Bar shi ya fara yi”

Dayan ya fada yana nuna Baba da ke jiran ace masa mutu ya mutu. Baba ya kalli Aminatu dake kwance tsirara sai kuma ya kalli mutane kamar be gane yarensu.

“Tashi ka yi aka ce ko mu kashe ka”

“Ya… Ya… Ya…ya…. Ya… Ta ce… Ce.. ”

Daker ya furta, sai dayan ya saka bindigar ya halbe Isah dake gurfane kamar mai neman gafara yana kuka, halbi biyu yai masa a kai.

“Ko ka yi ko mu kashe ka, ina ruwanmu da yarka ce, mu be dame mu ba…”

Aminatu ta runtse idonta da sauri tana jin kamar ta bude ta ganta a wata duniyar…!


Na zo muku da albishir guess what? A have alot of kayan mata masu kyau gaske, akwai na infection, akwai maida tsohuwa yarinya, akwai set din da ake hadawa for matan da basa gane kan mazajensu, akwai na mallaka kala kala, muna kaza mai magani, tantabaru, akwai kaza mai Yasin, akwai na mallaka sirrine mai karfin gaske. Ina masu son zama madubi a gurin mazanje su? Ina matan dake cewa na gwada ban dace ba? Muna da gumba da garin magani kala kala da na tsarki ga Humra da turarunka kala kala amman fa na kayan mata. Akwai dan wata bakwai, muna da kwalli mai karfin gaske (Mujarrabun sadidan) Akwai na farin jini for yan mata da Zaurawa. Akwai wanda ba a bawa mai kishiya, akwai na mazajen da kr neman mata, muna da rantse baki da kishiya, muna da back to virgin, for yan matan da kaddara ta fadawa, ko Zaurawan dake son zama yan mata, akwai jigida mai kyau, muna da man ayu 100% natural. Akwai na maza masu hannun Dambe.
Hajiya sai n gwada akan san na kwarai, ba cuta ba cutarwa, duk wanda kika siya sai kin dawo.

Previous page 1 2 3 4Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button