BAKAR WASIKA 9

“Rafi’a Allah ya shirya ki”
Ya furta cikin yanayin dake nuna alamar be jidadin daya sami gidan a haka ba, babu abun da ya fi bakanta masa rai ma kamar tararda ita da be yi ba a gidan, ko da yake halinta ne ko da ba zuwa unguwa ba takan fita makota tai taje can tana hira ko ta rika musu aiki alhalin ga nata aikin na gidanta ta bari, sai dai shi ya kasa sabawa da wannan halin, domin duk mai mata baya son ya shigo gida ya tarar matarsa bata cikin gidan idan ba da wani dalili ba, babu irin fadan da be mata ba amman bata canja ba, har ya gaji ya saka mata ido.
Gadon ya fara gyarawa sannan ya kwashe kayan data bari ya aje su a guri daya, ya gyara shimfidar Sultan ya dauko tsintsiya ya share dakin har zuwa falo, sannan ya zauna saman kujera ya daga kansa sama yana tunanin halin damuwar daya samu mahaifiyarsa a ciki, kusan kullum uwarsa bata rabuwa da damuwa domin idan babu na abinci akwai na rashin lafiyarta, sai dai a yanzu ta fi shiga damuwar fiye da koyaushe, a da tunanin na yadda zamu samu abun da za su sakawa bakinsu ne ko kuma na maganinta tsabanin yanzu da tunanin aurarda yarta wanda kanwace a gurin Faruq ya hanata sakat, ba Mahaifiyarsa kadai ba, idan aka fasa auren nan shi kansa zai shiga damuwa balle kuma ita kanwar tasa, domin mijin yace ya gaji da daga auren da ake ta yi, su kuma ba su da wani abun aurar da ita a yanzu, sadakin da suka karba da dadewa Mama ta saka shi a cikin kasuwancin da take ta zimmar zata dan juya ko zata samu riba, sai gashi ba wan ba kanen wato ba uwa balle kuma riba, daman sana’ar talaka sai Allah, balle kuma irin nata sana’ar da ake ci ciki.
Bayan matsalar kanwarsa ga matsalar kudin hayan da ke jiransa next week, gashi ba shi da mafitar kudin a halin yanzu, dan aikin da yake ta applying shi ma shiru kamar wanda ya zagi gobnati.
“Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un”
Ya furta yana dafe kansa.
“Allah ka kawo min sauki Allah ka yi min mafita”
Ya fada yana mikewa tsaye ganin har goma ta kusa matarsa bata dawo ba, duk yawunta bata wuce tara na dare sai idan biki ake ko kuma wani abu ke saka ta kai dare, ko da makota ta shiga bata wuce 9pm.
‘Ina tunanin tafiya nijar zai fi min gurin ginar zinari, sai dai shi ma ai dole sai ka samu kudi, samun wanda zai baka rance ma a yanzu ai aiki ne’
Ya nufi kofa yana ta sake-sakensa da tunanin inda zai samu mafita. Babu waya a hannunsa balle ya kira ya tambayi inda take domin ya bada wayar jingina tun shekaran jiya ya karbo musu abinci, hakan yasa ya fara nufar gidansu Maman Amira makociyarsu domin Baturiya tafi zuwa can ta wuni saboda suna da rufin asiri daidai gwargwado, ba shi ma ko mutanen unguwar sun shaidi Baturiya da son shigewa masu kudi, idan ka ga tana shiri sosai da mutum to mai rufi asiri ne.
Cikin almajiran dake zama bakin kofar gidan ya kira daya ya aike shi cikin gidan ya kira masa Rafi’a, almajirin na shiga ya fito dauke da Sultan dake bachi ya mikawa Faruq.
“Ance wai bata nan, tun dazun da ta shigo bar Sultan tace zata je kasuwa bata dawo ba, kuma ta kira wayarta a kashe”
Cikin fargaba Faruq ya karbi dansa ya juya yana yi ma almajirin godiya ya koma gida, kwantar da shi yai ya fito waje zuwa gurin mai shagon daya bada jinginar wayarsa.
AMINATU POV.
Sai da yamma lis ta farka, ta dade da farkowa daga suman da tai sakamakon ruwan da suka zuba mata ga kuma zafi rana dake dukanta. Kana kallon kwayar idonta zaka karanci gajiya, da wahala dake tattare da ita. Gaba daya jin take kamar babu mararta zuwa kasan cinyoyinta, ko motsasu ta kasa yi, hakoranta kuma sun dantse gam kamar a hade aka haliccesu, a kwance take amman jiri sai dibanta yake tana ganin hadarin dake haduwa yana juyawa. Ba ita kadai ce a cikin wannan halin ba, sai dai wasu sun fita juriya domin suna da aure wasu kuma sun yi har sun fa ra warkewa. Kamar jira suke ta farko sai wani yaja hannunta ayayinda sauran jikinta yake kasa zuwa gurin turken da suke daure matan, a kafa duka daureta kamar sauran matan, sai dai har lokacin a kwance take ta lumshe ido tana sauraren yadda numfashinta ke fita a hankali, babu tunanin komai a kanta tana son tai tunanin amman ta kasa, tana tai kuka ta kasa sai a yanzu ta gane ashe yin kuka ma wani babban gata ne, yin tunani ma wata baiwa ce, yau ta rasa ta ina zata fara tunani balle ya gayyato kukanta.
Sama sama take jin kafarta na mata zogi, saboda tafiyar data sha da kuma Ƙayoyin da suka taka, ba ita kadai ba kusan kowa yana fama da ciwon kafafuwan wasu sun taka kusa wasu kaya, sai dai basa jin zafi a lokacin sai a yanxu, wasu kuma daurin da akai musu ne yake musu ciwo, domin na da wasa suke daure mutum ba.
Kamar dazu da safe haka aka biyo su ana ba su abinci a hannu cibi biyu wasu uku, kowa aka zubawa sai yai sauri ya cinye saboda yunwa ta ci su har ta galabaitar da su, daman idan suka ci cibi biyu ko uku da rana ba za su sake ci ba sai kuma dare, wani lokaci ma ci daya ake a rana.
Komai tsananin zafin rana ko sanyi ko ruwa ba a basu abun rufa ko gurin fakewa, sai dai sanyi ya kare akansu, haka ma idan ruwa ne sai dai ayi ruwa a gama ya jika musu kaya kuma tufafin ya bushe a jikinsu, idan rashin lafiya ta same su sai dai su mutum domin babu zancen basu magani balle kuma akai su asibiti.
“Dan Allah ku kwance mu yi sallah magariba ta yi”
Daya daga cikin mutanen dake daure ya fada, kusan wannan shi ne karo na barkatai da yake rokon su barshi yai sallah. Sai wasu kananan samari suka nufo inda yake suka kwance shi suka ware shi gefe suka saka bulala mai kyau suna dukanshi.
“Wato kai shege ko, baka daddaraba”
Duka suka masa ba na wasa ba, daman jikinsa da sauran bulala da suka masa dazun saboda yace su bar shi yai sallah, a kullum sai yayi magana kuma a kullum sai sun masa duka.
(As I’m writing this mutumen da yake cewa su bar shi yai sallah is no more, Wallahi sun kashe shi neighbor din mu ne, and they sent his friend wanda aka kamasu tare ya fadawa iyalinsa bayan an biya kudin fansar karbo shi)
Bayan sun gama dukansa suka maida shi gurin da yake suka sake daure shi yana ta kuka, ga wahalar yunwa ga na dukan dazu dana jiya ga shi yanzu kuma sun kara masa da wani.
Ana gama sallah magariba ruwa ya fara sauko, ta yanayin garin suke iya gane magariba ko azahar da la’asar domin babu masallaci balle su ji kiran sallah balle kuma agogo. Yan bindigar ne suke ta gudu suna neman gurin fakewa, mutanen da aka ma kuma suna daure aka fara ruwan kama da bakin kwarya yana sauka a kansu, iyakar abun da suke shi ne su dukar da fuskarsa saboda kar ruwan ya taba fuskarsu, wasu kuma su saka hannu su kare fuskar tasu, sai dai hakan be hana ruwa ya jika su.
A cikin mutanen da ruwan saman ya jika har da Aminatu, dake kwance galabaice kamar sauran matan da basa da kuzarin yin komai, abincin da aka bata ma bata karba ba, komai ganinsa take kamar ba shi ba, har yanzu bata yarda mutanen da suka kashe mata uwaye da yan’uwa suka kawota daji suka keta haddinta yan’adam ne masu zuciya da jini a jikinsu ba. Ta kasa yarda a duniyar da ta sani take, gani take kamar daukarta akai aka jefata a wata duniyar ta dabam mai cike da azzalumai, kuma marasa tausayi da tsoro Allah.
Haka suka kwana a cikin sanyi cikin kwabon ruwa har safe, sam ita ko yunwar bata ji, sauran da suka dade nan kuma suna fama da yunwa domin sun sabu da gurin ya zame musu kamar gida, wasu sun yi wata uku wasu biyu wasu hudu har biyar ma.