BAKAR WASIKANOVELS

BAKAR WASIKA 9

              ***       ***        ***

MONDAY MORNING 9:21am.

“I wonder what wrong with our country? Kashe mutane ya zama kamar abinci?”

Cewar Kabir yana kallon hotunan da aka turo na harin da aka kai a garinsu Aminatu, abun ya kazanta kuma yayi muni sosai, musamman harin nan na biyu yafi na farkon ma, domin a yanzu an bar garin ba kowa, tun a lokacin da abun ya faru suka kashe na kashewa suka tafi da wasu, sauran da sukai rai suka gudu zuwa wasu garuran gudun Hijira!
Talba ya kalleshi yana kokarin gyara agogon hannunsa. Ba al’adarsa ba ce yin breakfast a bangaren a week days sai dai weekend, idan har zai karya to sai dai ya karya bangaresa ya sha tea ko kuma ya tafi office dinsa ya karya, sai dai ya zame masa al’ada shigowa ya gaisa da Momy kamin ya tafi aikin, sanadin hakan yasa suka sabu da Baaba idan ya shigo tana masa kirari ko da ba zai amsa mata ba zai mata murmushi ya gaishe ta sannan ya fita.
Yau sai ya ji dabam domin ya saba idan ya shigo zai tarar ita take shirya abun karyawa sai idan weekend ne Momy take tayata su hada komai a tare.

“Wai ya ake son talaka yayi ne? Su fa suke noma, yanzu an hana su noma wadanda sukai kuma a kone kuma a ashe su a dauke matansu kai jama’a wannan abun yayi yawa, nan gaba abinci ma sai yayi wahala”

Momy ta kalle tana kokarin aje flakes din ruwan zafi a dinning.

“Shiyasa ga su nan sun bi sun cika mana gari da bara kamar za su kwata da karfi”

“Haba ai dole Momy, ki duba yadda mutumem kauye yake alfahari da noma amman su bar komai nasu su dawo inda babu kowa suna bara, abun tausayi ne Wallahi”

“Su ma ai sun so, tun da su suka fara kashe Fulanin”

“No wannan ba hujja bace Momy idan ma da gaske ne”

Tabe baki tai ta cigaba da abun da take, har suka ci suka shude Talba be ce komai ba, daman shi ba komai ke saka shi magana ba, ko da kuwa abun ya dame shi.

“Momy zan tafi aiki”

“Yau da wuri?”

Ya daga mata kai.

“Allah ya tsare”

“Ameen”

Ya amsa sannan ya fito daga bangaren yana wani irin kamshi turare mai jan hankali yan mata da saukar da natsuwar mai shakarsa. Kai tsaye bangaren Daddy ya nufa sai da yai knocking sannan ya tura kofar sai ya jita a rufe, door bell din ya danna sannan yaja ya tsaya. After few minutes aka bude masa kofar. Sai da suka gaisa da Amal da ta bude masa kofar sannan ya karasa can ciki gurin Daddy. Sai ya same shi zaune rai a bace yana kallon wayarsa, domin labarin harin da aka kai ya karadi kafofin sada zumunta musamman Facebook.

“Wa’alaikassalam”

Daddy ya dago yana amsa masa sallamarsa, Talba ya zauna kusa da shi yana karantar bachin ran daya bayyana a fuskarsa.

<<<<<<
Sauran page daya mu gama free page, if you want to subscribe pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank and sent the evidence via 08036126660. Yan nijar kuma za ku biya ta wannan number +227 90 16 59 91 sai na yi adding dinku a group.


Na zo muku da albishir guess what? A have alot of kayan mata masu kyau gaske, akwai na infection, akwai maida tsohuwa yarinya, akwai set din da ake hadawa for matan da basa gane kan mazajensu, akwai na mallaka kala kala, muna kaza mai magani, tantabaru, akwai kaza mai Yasin, akwai na mallaka sirrine mai karfin gaske. Ina masu son zama madubi a gurin mazanje su? Ina matan dake cewa na gwada ban dace ba? Muna da gumba da garin magani kala kala da na tsarki ga Humra da turarunka kala kala amman fa na kayan mata.
Ga masu bukata za su iya tuntubar number na 08036126660 zan saka miki a mota na aika miki har inda kike da yarda Allah.

Serious Buyers please, idan ba ki shirya ba kar mu batawa juna lokaci.

Previous page 1 2 3

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button