BAKI BIYU COMPLETE HAUSA MUSICNOVELS

BAKI BIYU COMPLETE HAUSA MUSIC

Anwar na son k’annenshi, duk da ake cewa, Anwarah ba babansu d’aya ba, wanda shima ya san da cikon labarin ne a bakin Aunty zuwairah, amma yana jin cewa itama k’aunarshi ce, sai dai wasu abubuwan da take yi ne, ke bashi haushi da ita wanda baya so, saboda tun tanayi ita kad’ai, har ta koyama Humairah tana yi, shiyasa har ya shigo garin Abuja ya koma, ba zasu had’u ba, irin halinshi na k’yaluwa, ita har ta dameshi ta shanye.

Kwalliya ce baya son ganin sunayi, domin shi ya d’auki masu yin kwalliya a matsayin karuwai, ita kuma Anwarah ba ta san ta yadda zata bar kwalliyaba, a matsayinta na ‘ya mace ba. Makaranta kawai ke hana Anwarah kwalliya idan zata je, amma wallahi bata ga ta yadda zata zauna ba, bata shafa janbaki ba a bakinta, wannan d’aya daga cikin abinda ta tashi taga momynta nayi shine gyaran jiki da kwalliya, don haka itama ta yadda da ta zama ‘yar kwalliya.

Da hakan suke samun matsala dashi idan ya shigo part d’insu, wanda ko gaisheshi Anwarah tayi, baya Amsawa da mutunci, ita kuma Humairah ya san ba laifinta bane yimata ake yi, wanda idan ya ganta da ita yakan korata ta gogeta, ita mai yin ko ganinta ba zai yi ba.

★★★★

Shekarar Anwar d’aya a india, Anisa ta k’arasa secondry school nata, inda Anwarah kuma a lokacin ta shiga S.S 2, Humairah kuma a lokacin take J.S.3, don hakan yanzu sun rage had’uwa da Anisa, dama a mota suke had’uwa idan za’a kaisu, ita akaita tata makarantar, su kuma a kaisu tasu, yanzu kuma sun fi kowa jin dad’in hakan.

ANWARAH: Yarinya ce mai hankali, domin natsuwarta kawai na saka a kirata da mai girman kai, Anwarah ba fara bace, kuma ba ka kirata bak’a ba, Anwarah ko a school bata son tarkacen k’awaye, k’awarta k’waya d’aya ce Suhaila, Suhaila halinsu ne ya zamo d’aya, sannan duk yadda zaka so kaji kansu ba zaka ji ba.

Irin d’an boys friends d’innan da ake yi, kwata-kwata ba zaka sameshi garesu ba, domin Anwarah bata yadda da kowa sai kanta kad’ai, shima ba duka ta yadda dashi ba. Yarinyar ta taso mai mugun wayau, hakan yasa kwanyarta take da kaifi a karatu, ga shegen farin jini, amma ko kad’an bata aminta da kowa.

Anwarah ta kasance mai mugun son kwalliya, ko a school tasha kashi a kan faruttanta da ke da sauran lalle, amma bata dainawa, hakan suka gaji suka shareta.

Year d’inda su Anwarah sukayi graduate, year d’in baffa ya mai da Humairah boarding school, wanda Anwarah bata so hakan ba, domin zata yi zaman kad’aici kafin ta wuce wata school d’in, amma Anwarah haka ta hak’ura da hukuncin baffa a lokacin da ya bata hak’uri akan hakan.

Ganin kad’aicin nata ita kad’ai a gida, sai baffa ya nema ma Anwarah admission a wata LEADERSHIP UNIVERSITY da ke nan Abuja, makarantar ko wanda ke k’asar waje, ba zaya nuna musu karatu ba, domin suma turawa, ke yi musu lectures, makarantar masu ji da fad’a ce.

Fara zuwan Anwarah, Baffa ya siya ma Anwarah mota, domin gudun reni ga abokan karatunsu, domin ganin yadda yadda yaran manya ne ke school d’in, momy ta yi fad’a, amma ya ce babu ruwanta, yasan me yake yi.

Anwarah tayi murna da addu’a iri-iri, wanda sai da baffa ya zubar da hawayenshi a ‘boye. Momy haka ta hak’ura, saboda tasan yana yima Anwarah so na tsakani da Allah.

Tunda Anwarah ta fara driving, sai kyawonta ya k’ara fitowa, domin komai nata a natse take yinshi, sai dai rashin magana da batayi da kowa, hakan ta matsama iyayen Suhaila da su kaita itama a cen, hakan kuwa akayi, wanda tare suke zuwa kuma su dawo tare, hakan yasa duk wasu samari ba nasu bane, amma kowa son Anwarah yake yi.

Tunda yayan Suhailah, Abdallah ya d’aura idonshi ga Anwarah, sai kuma zancen ya sauya salo, wanda ko mai zaiyi, sai yaga fuskar Anwarah a ciki, sonta ya zamar mishi sark’a, wanda sai da ya sanar da suhaila, bata tsaya jin komai ba, ta sanar da Anwarah, amma sai Anwarah ta ce mata, ta daina wannan zancen, idan har tana so, su dinga gaisawa mai yawa, hakan yasa Suhailah jaye maganar da sauri, domin tasan Halin Anwarah babu kyau a irin hakan, kaifi d’aya ce, duk da tana son abinda take so, amma ta share zancen. Shi kuma ko yaushe yaga Anwarah kamar ya mutu.

Motar da Anwarah ke hawa, ita tayi ma Anisa bak’in ciki, domin masu ganinta da mota, sun san cewa Anisa ta girmeta, amma ita ko keke bata da ita, wanda suke yi mata d’aukar ita ce yaya ga Anwarah d’in, kuma suna yi mata d’aukar duka babansu d’aya, a dalilin motar nan, zasu iya yarda da ita bare ce ba’a sonta.

Ta matsama Auntyn ta, amma ta kasa wani yunk’uri, sai ce mata take yi, nesa ta zo kusa,tayi hak’uri.

Anisa Baffa, haka take sakawa kamar yadda sauran yaran ke sakawa, Anisa fara ce tas! Sai dai babu sauran kayan da ‘ya’ya maza ke kwad’ayin samu a mace, domin ta girmi Anwarah sosai, amma Anwarah tafita cikar mata. Anisa bata son kwalliya ko kad’an, shiyasa ko yaushe, cikin k’ananan kaya take da acuci maza a k’irjinta, wanda ta hakan za’a iya kiranta da k’irjinta ne.

Kowa da renon part d’insu ya tashi, don Haka Anisa da renon Auntynta ta shi, domin wai su wayayyi ba’a kwalliya, sai dai idan an shafa mai, to anyi wuta kenan idan anyi wanka.

Anisa sai ta wuni a gidan batayi wanka ba, wanda ba’a ganewa anyi ko ba’ayi ba, saboda ko yaushe hakan ake.

Anyi nasarar raba Anisa da Nuraddeen, wanda har yayi aure a This year, ita kuma tana nan suna soyayya da Anwar a waya, da zancen babu wadda yake so, ko ya aura sai Anisa, don haka itama hankalinta ya natsu da soyayyar Anwar, amma da BAKI BIYU.

Anwarah Hankalinta kwance take karatunta, domin bata kawo kowa a rayuwarta ba, saboda haushi ma mutun yake bata idan yace yana sonta, domin ganin take yi ita yarinya ce k’arama, duka This year ta cika shekaru 18 da haihuwa, kawai falalace ta ubangiji da ya hore mata kayan manya, amma kuma sai ayi ta kiranta da wani zancen love cen? Ta tsani love, da ma mai furtashi, shiyasa ta d’auke k’afarta da zuwa gidansu Suhaila akai-akai.

 *Dalilin soyayyar Anwarah da Faisal.*

Washhh! Hannuna ya yi ciwo wallahi, page d’in jiya da yau ne guri d’aya, bani son muyi delay ne, ina son muje da sauri, tarin nishad’in na gaba, ku dai ku bini a hankali, Ta kun ce, wato TA MASOYA Insha’Allah! Zaku samu nishad’i.

Bee²TA Masoya
[10/27, 10:20 PM] ®Bëë Bëë Tâ Māsôyä????????: ????????????????????????????????????

___________________
♦BAKI BIYU♦
___________________

® REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS P.M.L????????????

ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ

WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM

IG PML WRITERS

https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035

©®
Khadija bee bee
Khadijabellobuhari@gmail.com@gmail.com

★★★★★★★★★
Page…6⃣
★★★★

FAISAL TAHIR: ‘Dan asalin garin jigawa ne, a cikin wani k’auye da ake kiranshi ka zaure, Mahaifan Faisal talakawa ne sosai, domin su kan kasance ko abinda za su ci, sai mahaifiyar Faisal tayi surfe.

Duk da cikin wannan wahalar da suke ciki, mahaifin Faisal baya wasa da karatun yaranshi a makarantar gwamnati da ke cikin k’auyen nasu. Faisal shine babba a gidansu, ya na da k’anne hud’u, maza biyu, mata biyu.
Kasancewar garin nasu da yarinya ta taso ake yi mata miji, ya saka k’annenshi mata babu wadda tayi karatun boko sai na allo,shima din ba nisa akayi ba, akayi aure.

Faisal nada k’ok’ari sosai, shiyasa duk abinda za’ayi a makarantarsu yake samun ci gaba. Ta hakan ya samu d’aukaka a duk makarantar da yaje, da kuma taimakon filayen mahaifinshi da na mahaifiyarshi aka samu yayi karatun bokon baki d’aya.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button