BAKI BIYU COMPLETE HAUSA MUSIC

Faisal tun yana university Allah yayi mishi mugun son ganin ‘yan matan birni, kasancewarshi ya na da kyau, shiyasa baya shan wuya a soyayya da ko wace macce. Faisal k’wararre ne a iya kalaman baki, wanda ko uwar da ta haifeshi ya zabga ma zance, wajibi ne ta yadda da zancen Faisal, domin sunanshi ne ya dace da shi wato, Faisal.
K’are service nashi ke da wuya ya samu aiki (pension office) in da babu wuya ya samu d’aukaka, sai kuma kyau da shiga gari ya k’ara yawa, tunda kud’i suna shigoshi kamar hauka.
Nan take ya koma gidansu ya gyara ma mahaifanshi gidansu, ya mayar da k’annenshi makaranta, inda suka tsaya bakin secondary, sannan ya kyautata mahaifanshi, kamar yadda suka taimaka mishi, har sai da ya kasance garin baki d’aya, babu gidan da yafi gidan mahaifanshi wadata, abinci iri-iri kana gani a gidansu Faisal. Hakan yasa mahaifanshi murna, domin komai sai babu hak’uri ake ganin k’urewar lokaci.
Tunda iyayen Faisal suka ga ya mallaki arzik’i, sai suka fara bijiro mishi da zancen ajiye iyali, wanda mahaifiyarshi ta turashi gidansu Binto d’iyar k’anwarta.
Ba musu yaje yaga Binto, Binto komai ta mallaka, domin babu macen da zata nuna ma Binto kyawo, sai dai da sauran Binto a irin ‘yan matan da yake burin so ya aura, sai dai babu yadda zai yi, tunda mahaifiyarshi ta bashi Umurni, amma shi wallahi bai tashi yin aure yanzu ba, don ba ya da burin ajiye iyali yanzu, shi burinshi kawai ayi rayuwa, kafin auren ya zo da kanshi.
Hakan ya bama mahaifiyarshi shawarar a mayarda Binto makaranta, kuma shi zai d’auki nauyin karatun nata, ba musu iyayenshi da nata iyayen suka yarda, amma da sharad’in a d’aura musu aure, wallahi faisal yak’i yarsa, domin yarinya ce k’arama, shi kuma big one’s yake so.
Suka aminta aka mayar da Binto makaranta, kuri gurin Binto ba’a cewa komai, domin za’a yi karatu, kuma ayi aure Birnin kaduna, domin a cen faisal yake. Binto na son Faisal kamar ranta ya fita, wanda hakan yasa aka sai mata waya su dinga gaisawa.
Wasa-wasa Binto girma yana shigota, kyawonta na fitowa, Duk Faisal ya shigo garin, sai yaje wurinta, wanda a hankali sonta ya fara shiga zuciyarshi, sai dubara ta fad’o mishi cewa,
‘Ai ya samu garkuwa ma a rayuwarshi, ita zai barta a matsayin matarshi ta sunnah, wadda zai killaceta, ba tare da kowa ya ganta ba, ya barta anan garin nasu, hakan shi zai sa ya faranta rayuwar iyayenshi da kuma ya samu mata a cikin sauk’i.
Da hakan ya yarda da Binto A matsayin matarshi, amma baya so har yanzu a d’aura auren, sai next year idan ya gyara gidanshi na nan garin, domin nan zai ajiyeta.
Irin sonda Faisal ke nuna ma Binto a bayyane, shi ke saka binto mutuwa a sonshi, domin ko yaushe burinta taga ranar da zasu kasance a matsayin ma’aurata, domin ita ba zatayi kunyar nan irin tasu ba, ta ‘yan k’auye, wayewa za’ayi.
Ko yaushe Faisal ce mata yake yi, son da yake yi mata, wallahi babu macen da zai iya yi ma shi a rayuwar duniya, kuma ita ce uwar ‘ya’yanshi, babu macen da zata kai gareta. Binto ta hau Furuncin Faisal na BAKI BIYU ta zauna, sai dai ita nata BAKI BIYU d’in mai sauk’i ne tunda zai aureta, sauran matan fa?
A irin wannan rayuwar ce, Faisal ya kasance a fagen Rabkama ‘yan mata Baki Biyu. Duk macen da ya gani, idan dai sukayi arba da juna, wajibi ne ta soshi, sai in idan tagano halinshi, sannan ta ke kama gabanta, idan har bai gama lalabe jikinta baki d’aya ba.
Shifa Faisal, ko ba shauk’in son mace a zuciyarshi, to wallahi da yayi arba da ita, ta fad’a sonshi, sai yaji sai anyi rayuwa irinta ta turawan da yake kallo a t.v, wato a rungumi juna, k’arshe a shafi juna, idan ma mace zata aminta su hau gado d’aya, to Faisal zai yadda.
Yana acikin haka ne, ya koma gida aka d’aura aurenshi da garkuwar Matarshi wato Binto, anyi shagali iya shagali, wadda ango ya tare a gidan matarshi binto, an gyara ko ina, gidan nasu yayi kyau, domin ginin zamani, sannan kayan ciki ma, kamar na zamani.
Daren farkonsu, binto ta gamu da jarabta irin ta jarababbe d’an duniya, sannan bai kwanta da ita ba, sai da ya bata magani ta sha, domin yasan baya da wuyar sakin ciki a jikin mace, wanda yasan hakan ta hanyar zubar da cikin da ya bada kud’i akayi ba kad’an ba, kuma ya yadda binto matarshi ce, kuma uwar ‘ya’yanshi, amma ba yanzu zasu haihu ba, sai an k’ara lokaci.
Yawan bin umurninshi da binto ke yi, kesa yana jin sonta a ranshi, amma ba zai iya yadda cewa ita kad’ai ce, yake jin sonta a ranshi ba.
Bayan yaci amarcinshi, ya kamo hanyar zuwa kaduna, inda aka turashi aiki Abuja na tsason wata goma sha biyu (1year).
Kasancewar aikinshi akwai wuya, saboda ko yaushe cikin aiki yake yake yi, hakan yasa ya rage ganin ‘yan mata akai-akai, sai in ya je inda zai gansu, wanda yake ji a rayuwarshi ma, zai iya daina kula ko wace mace, ya tsaya ga garkuwar matarshi, amma kuma sai yake jin kamar da wuya ya daina yin Baki Biyu, domin anan yafi k’wari.
★★★★★★
Da sanyi marece ranar monday, a Leadership university Abuja(L.U.A) makarantar su Anwarah kenan. A ranar Anwarah tayi marece a school d’in, domin kasancewar ranar anyi ruwan sama, kuma gashi sai da suka shiga practical, sannan aka fara ruwan. Bayan sun k’arasa ne, ta nemi suhailat ta rasa ganinta, wanda ta d’aga waya domin kiranta, kuma bata d’aga ba. Hakan ya bama Anwarah gano laifin da tayi ma Suhailah, don haka murmushi tayi da d’auko hand bag d’inta da littafanta ta fito gurin da suke parking d’in motoci, har zata saka key ta bud’e motar, sai ta ji k’arar shigowar text a wayarta, hakan yasa ta bud’e motar ta jefa littafanta, da zaro wayar a jikkarta, dubawa tayi, sai taga contact d’in Suhailah, da sauri ta bud’e tana murmushi ta fara karantawa kamar hakan;
“Wallahi kin bani mamaki Anwarah, ban ta’ba tunanin cewa, akwai abinda zan nema a gareki ba na rasa, nayi tunanin ko sharri ne nazo miki dashi zaki yadda ki aminta dashi, bare kuma yaya nah, tunda har ba kya son sa, to nima ba kya sona wallahi, daga yanzu zan dinga tsayawa wurina, kema ki tsaya naki wurin, gudun kada na rink’a ganin bak’in ki, wanda bana so wallahi, sai dai ki sani da ni ce kika kawo ma naki yayan, ba musu zan kar’ba, domin nasan ba zaki cuce ni ba, don haka daga yau ba zan k’ara shiga motarki ba, yaya na zai dinga zuwa d’aukata, ko driver.”
Murmushi Anwarah ta sakai da cewa, “sai kace da gaske zata iya rabuwa dani, suhailah ba ki gane nufina da ma’anar hakan da nike yi, wallahi baki………..”
Bata k’arasa fad’in abinda take fad’a ba, kawai taji saukar ruwan dake kwance a kusa da inda ake ajiye motoci, ruwan saman da akayi suka kwanta, sune suka wanke mata fuska da kayan jikinta baki d’aya, da wayar da ke hannunta, wanda ruwan laka ne jajaye, dole ta kasa ganin gaban wayar ta-ta, hannunta ta saka da mayafinta fari ta goge fuskarta, anan ta hango motar da tayi mata mugun aikin nan a jikinta.
Jefa wayar tayi a mota, da rufe marfin motar ta-ta, ta jingina da nad’e hannuwanta a k’irjinta tana jiran fitowar wanda yayi mata wannan cin mutuncin, hango shi tayi ya bud’e gaban motar ya fito da sauri, domin ba ta hak’uri, sai ta juyar da fuskarta gefe domin cin mutuncin yayi yawa wallahi.
Faisal ko ganin fuskar Anwarah bai yi ba, amma wallahi zuciyarshi ta gama kamuwa da yanayin k’irar jikinta da hango, nan take ya fara murza idonshi, domin ya tabbatar da abinda yake gani aciki. Da sauri ya matso gurin da robar ruwa a hannunshi yana cewa,