BAKI BIYU COMPLETE HAUSA MUSIC

“Don Allah kiyi hak’uri! Wallahi wallahi ban kula da ramin bane, shi ya saka motar ta fad’a aciki har hakan ta faru, sorry please! Ga ruwa ki wanken fuskarki.”
Da sauri Anwarah ta juyo ta kalleshi, ta watsa mishi wata shegiyar harara, sannan ta bud’e motar ta, ta fad’a da danna key nata ta kunna, wanda ko kallomshi bata yi ba ta fara driving ta tafi ranta a ‘bace.
Faisal yayi mutuwar tsaye, domin ganin fuskarta kawai ya sakashi d’imauta, hak’ik’a bai ta’ba cin karo da halittar da ta firgitashi ba kamar wannan budurwar, gaskiya duk wanda ya sameta a rayuwa ya more sosai, da wannan yanayin ya juya ya tafi, domin yin abinda ya kawo shi.
Anwarah da fushi tayi driving har ta kawo gida, kwaso littafanta da wayarta da ta sha ruwa tayi a mota, sannan ta fad’a mik’i hanyar part nasu jiki duk kwancin jirwayen ruwan cha’bo. Karo taci da Anisa ta gefen hanyar da zata sadata da part nasu. Dariyar k’eta ta azama Anwarah da cewa,
“Yau kuma marainiyya ji da kai d’in ya had’aki da wanda yayi miki wanka da ruwan cha’bo? Kad’an kika gani, idan dai wulak’anci abin yi ne, kada ki daina ki yi ta yi, sai tak’ama da gidan wasu.”
Da yawa Anisa na fad’ama Anwarah irin wad’annan maganganun, amma bata gane me take nufi, ita dai ta san nan ne gidan ubanta, kuma tasan ita bata wulak’anta kowa a rayuwarta, kawai abinda wasu suke yi ne, ita kuma baya burgeta, yin soyayya da samari barkatai, shi yasa ko an tareta take share su. Amma yau kalaman Anisa sun tunzura rayuwarta, wanda wajibi itama ta fad’a mata kamar yadda momy tace ta dinga bata amsa idan ta k’ara ce mata hakan d’in.
Murmushi Anwarah tayi, kamar ta wuce part nasu, kuma sai ta juyo ta tsaya ta ce mata,
“Ai da ganin bare an sanshi, domin ni kowa yasan baffa na sona, inma shi ya haifeni ko bashi ya haifeni ba, kowa yasan yana sona so na gaskiya, sannan zancen ji da kai da kika kira, ai mace marar aji ce, ita ke amsa gayyatar namiji nan take idan yayi mata, ba macen da ke manne da jiran a sota ba, Ni Anwarah na sha gaban wani yayi mini watsin ruwan cha’bo, sai dai yayi by mistake, kuma ganina kawai ya isa ya bani hak’uri, don haka kin sa’ba wannan mummunan tunanin naki, ki sake kawo wani nan gaba, Anwarah ta wuce nan, ke babba ce, ki kama girmanki, kamar yadda na ba ki shi a farko, in ba haka ba komai zaki iya ji a gareni nan gaba.”
Anisah ta sha jinin jikinta, wanda sai da taji tsoron zancen Anwarah, ‘hmmm! Bari na ja girmana, kada yarinya k’arama ta galla mini mari, inaji ina gani, ko na rama ai tasha dani.’
Anwarah ta wuce ranta fes! Domin ta san ta aikama Anisa mai zafi. Duk iya kare kanta da take yi dasu, sai sun samu hanyar had’uwa da cin mutunci, hakan yasa bata shiga part d’in Aunty zuwairah baki d’aya, part d’in mama kawai take shiga, mahaifiyar Anwar kenan.
Ko d’akin momy bata shiga ba, ta zarce d’akinta, inda ta cire kayanta da kuma shiga wanka, bayan ta fito ta duba wayarta, wadda ruwa duk sun shiga cikinta ko motsi bata yi, ranta ya ‘baci sosai, don haka ta cire sim nata baki d’aya ta ajiye wayar kawai.
*************
Sati biyu da yin hakan, ko yaushe Faisal sai yaje makarantar, amma da d’ai rana bai ta’ba ganin Anwarah ba, ya rasa menene sunanta, fuskarta kawai zai iya gani ya gane cewa ita ce wadda suka had’u, gashi kuma bai ganta ba.
Anwarah ta shawo kan k’awarta Suhailah, nan take suka shirya suka koma yadda suke ada, har take bata labarin wanda ya ‘bata mata jiki da ruwa. Suhailah taci dariya, sannan ta kalleta tace, “Rashin son yaya na ne Anwarah, gashinan kinsha ruwan cha’bo.”
Ta yi mata dariya sosai, sannan suka mik’e zuwa gida.
Yau Faisal a bakin motar ya tsaya, tun lokacin da ya hango shigarta school d’in. Ganin isowarsu ya mik’e da sauri tare da isowa gurinsu da sallama.
Anwarah na ganinshi ta gane shi, don haka ko kallonshi bata yi ba. Suhaila ta tsaya da sauraronsa inda yake ce mata,
“Don Allah ki bata hak’uri, wallahi a kuskure ne hakan ya faru, kuma ko yaushe ina son na ganta na bata hak’uri amma ban ganta ba sai yau, don Allah ki ce ta yafe mini, in kuma zaki taimaka mini da number d’inta to ki taimaka mini, ni zan bata hak’uri.”
Suhailah ta ce yaje kawai zata hak’ura, domin ba tada matsala. Ba haka Faisal ya so ba, ya so ya ga Anwarah d’in, amma kuma bai samu ba, domin yasan kaifin bakinshi akan ‘yan mata, duk wacce ya hau, sai ta kar’ba, amma ko yanzu wallahi sai tarkonshi ya kai inda yake so, aje zuwa dai.
Tunda hakan ta faru ko yaushe sai Faisal ya zo ya tsaya a inda zaiga Anwarah, ko yaushe jin sonta yake yi na shiga zuciyarshi, hakan yasa duk matarshi binto ta kirashi, yake jin duk ta isheshi da shegen surutun tsiya, wani lokaci har cewa yake yi, ” ‘yar k’auye kawai.” Sannan ya amsa kiranta, ya sakar mata Baki Biyu d’inshi na soyayya ta hau ta zauna da murna miji na ji da ita.
Watan Faisal Biyu yana biyar Anwarah amma bai samu ko da minti d’aya ya ganta ba, bare kuma ta yarda su gaisa, hakan ya dami Faisal sosai, wanda sai da ya tambayi wasu d’alibbai maza da mata akan ko sunsan halinta? Anan suka shaida mishi cewa, tunda ta shigo makarantar ai ba tada saurayi ko k’awa, sai mutun d’aya, wadda yake ganinsu tare kullum, ai mugun d’aukar kai gareta.
Faisal na jin hakan ya tabbatar da wannan zata yi mishi wuyar kamu, domin ba irin wad’anda ya saba gani bane, dubara ta fad’o mishi akan inda zai samu number d’inta.
Wurin admission office nasu, zai iya samu tunda ya san wanda ke basu. Nan take ya nemi sunanta da department nasu, ba musu suka bashi.
Bai sha matsala ba, a gurin samun Number dinta ba, babu abinda ke yi mishi dad’i irin sunanta, ya na burgeshi sosai. Tunda ya samu number dinta, ko yaushe ya kira switch off, saboda lalacewar da wayar tayi, sai wata rana da aka changer mata waya tana zaune a falo ya kirata.
Ganin bata san number d’inba, ya saka ta k’i d’aukar wayar, sai da akayi kira biyar sannan ta d’aga.
Jin muryar namiji ya ambaci sunanta, sai gabanta ya fad’i, domin shine kira na farko da aka yi mata kuma bata san number din ba.
Mik’ewa tayi da sauri ta haye sama, domin ta samu sakewa wurin jin ko wanene hakan? Shigarta d’akin ta amsa sallama d’in da cewa,
“Da waye nike magana?”
Shiru ta ji anyi, sannan ta k’ara tambaya, “hello! Wai waye ne?”
“Aminci ya tabbata a gareki ya mai kyakkyawar sura da halitta, masoyinki ne na hak’ik’a, Faisal Tahir kuma wanda ke burin ya……..”
Anwarah ba ta tsaya ya k’arasa zancenshi ba, ta katse kiran da kashe wayar baki d’aya, tana jin haushin kanta ma da ta tsaya sauraronsa wallahi, don haka sai ta fara tunanin, ‘shin ko waye ne hakan? Kuma ko a ina ya samu number ta?’
Zancen zucin Anwarah kenan da take yi, har ta ji ta tsani tunanen ma ta fita abinta.
Faisal ya ga wadda ta fishi iya rainin wayau, wato duk hanyar da za’a biyo mata, tana iya hukunta mutun da irin yanayinshi, ita wannan ko son jin muryar maza bata yi kenan?
“Wallahi k’arya ne ace Tarkon Faisal bai kama ba, wallahi Anwarah sai kin aminta dani, aminta ta kasancewarmu ta har abada, ina sonki, kuma sai kin amsa, na fi k’arfin mace ta wahalar dani, Take na ne, na BAKI BIYU na daki cen, na daki nan, kuma dole a aminta dani wallahi, saboda na kai duk yadda ake so, Anwarah muje zuwa………….”
Muma gamu biye daku Faisal, ko ya za’ayi wannan rikicin mai taken BAKI BIYU Zai kasance? Muje zuwa kawai.