BAKI BIYU COMPLETE HAUSA MUSICNOVELS

BAKI BIYU COMPLETE HAUSA MUSIC

Bee²Ta Masoya
[10/31, 8:56 PM] ®Bëë Bëë Tâ Māsôyä????????: ????????????????????????????????????

___________________
♦BAKI BIYU♦
___________________

® REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS P.M.L????????????

ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ

WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM

IG PML WRITERS

https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035

©®
Khadija bee bee
Khadijabellobuhari@gmail.com@gmail.com

★★★★★★★★★
Page…7⃣
★★★★

2 month ko yaushe Faisal sai ya kira Anwarah amma bata d’auka, idan tayi blocking d’in layinshi zai changer wani layi, har ta kai da ta d’auka take kashe wayar ko wane lokaci.

A lokacin ne momy ta fara fahimtar abinda ke saka Anwarah kashe waya, domin bata so a kirata, momy ta shigo d’akinta ta zauna da cewa,

“Anwarah me yasa ki ke son ki dinga wulak’anta mutane akan sun nuna suna sonki? Jiya ina jinki kina fad’ama wani magana a waya son ranki. Shin Anwarah baki san kin kai lavel d’in da za’a ce kin fara saurarar samari ba? Ai a lokacin da muka hanaki sauraronsu, saboda baki isa ba, amma Anwarah 18years ai kin isa ki kawo ma wanda kike so ba sai An ce miki ba. Ba muda burin da ya wuce hakan a garemu, ni da baffan ku, da duk wani mai k’aunar ki Anwarah, wanda ya wuce a yanzu muga ranar Aurenki, ko ace muga kin kawo wanda shine za’binki, don haka ki daina rashin saurararsu, sai dai ki san wad’anda zaki saurara, domin tsira da mutuncinki, da kuma namu mutuncin na matsayin iyaye a gareki.”

Anwarah ta sunkuyar da kanta k’asa tana sauraron momynta, wanda ita ma burinta bai fi taga tayi abinda zata faranta ran mahaifan nata ba. Cikin kunya ta d’ago kai ta ce,

“Momy ni bana wulak’anta kowa wallahi, kawai ina yin hakan ne, domin na gano wanda ke so da gaskiya a cikin masu kiran nawa, shi yasa kawai nike k’in d’aukar wayar Amma babu komai momy.”

“Yauwa! Anwarar baffa, kin ga kuwa idan har kika samo mana mai hankali, zamu fi kowa murna da farin ciki. Allah ya tabbatar da Alkhairi yarinyata, zamu ta yaki da Addu’a, insha’Allah Anwarah ba zaki ta’be ba.”

Murmushi sukayi dukansu, wanda sai da Anwara ta rungume momyn nata suna dariya.

Tun daga lokacin Faisal bai k’ara kiranta ba, sai dai kiran Yaya Abdallah da ke shigo ta, wanda shi kuma Abdllah, har yanzu bai fara nuna ma Anwarah irin sonshi ba a gareta ba, saboda har yanzu bata amsa mishi kalmar amsar son shi d’in ba, don haka duk ya kirata, za su gaisa da kuma nuna mata Alamar son jin amsar shi, ita ba zata bashi ba, shi kuma ba zai daina tambayar ba, wanda ke ‘bata ran Anwarah kai tsaye, har taji lallai tafiyarsu da Abdllah ba zata kai ba. Ita miskilanci, shi kuma girman kai, don yana ganin kamar shima ya kai namijin da ko wace mace zata so, don haka Anwarah bata k’arfafa sonshi a matsayin mijin aure, sai a matsayin yayan suhailah, itama kuma yayanta.

Naci babu kamar Faisal, kira da text kamar banza, wanda wasu kalaman na text d’inshi Anwarah bata ta’ba jin irinsu ba sai a gareshi. Anwarah tun bata dubawa, har takai tana duba text nashi kuma suna yi mata d’ad’i a karantawa.

Wata d’aya suna a hakan, idan yayo mata text tana dubawa, idan Suhailah na kusa kuma sai ta bata ta duba, sai ta tambayi Suhailah cewa, ko ta san mai wannan number d’in? Suhailah ta Amsa mata da bata sani ba, domin ta san ba yayanta bane.

Sai a wani text Anwarah taga sunan da aka rubuto mata da cewa,

“Babban masoyinki, wanda kin ta’ba ganinshi, amma kin k’i ki amsa mishi so da k’aunar da idan ya rasa ta, zai iya shan guba ya mutu. NAKI FAISAL TAHIR JIGAWA”

Anwarah na yawan maimaita kalmar sunan, amma kuma bata san mai sunan ba, domin bata ta’ba yadda ta d’auki kiran da ba tasanshi ba, amma tana sauraron text nashi, ta hakan take d’an ji a ranta, wannan ya taka mataki na d’aya acikin matakan da ta ke son mijinta ya zama, wato gwanin iya soyayya da kalamai, don haka ta kai matakin da ita ke jiran text nashi ya turo ta ji me zai ce?

Faisal baki d’aya ya daina kiran Anwarah, sai dai ko yaushe sai yaga Anwarah a school nasu. Hakan yake sakashi rubuta mata text a ko wace rana kusan sau biyar, Anwarah tun tana karantawa, tana gogewa ba reply, har ta fara mayar da reply da cewa,

“Wai ko ma wanene kai, kana ganin zaka iya dasa soyayyarka a zuciyar Anwarah ne? Wad’anda suka fito fili ma na gansu basu burgeni ba bare kai na ‘boye. Ina son ka sani, ba da irin wad’annan kalaman banzar da kake yi mini ba za ka rud’ani har sonka yayi winning a zuciyata ba. Don Allah ka daina damuna hakan, ni karatu nike yi ban shirya kar’bar soyayyar kowa ba.”

Anwarah na tura mishi ya duba yayi murmushi, sannan ya maidar mata da cewa,

“Love comes when manipulation stops; when you think more about the other person than about his or her reactions to you. When you dare to reveal yourself fully. When you dare to be vulnerable my lovely beauty.”

Faisal na murmushi ya tura mata text d’in, a lokacin yana a masaukinshi na nan Abuja a kwance yana hutawa. Text d’in na shigowa Anwarah tana d’aki kwance itama, sai ta samu kanta da son bud’e text d’in, domin abun ya zamo mata kamar game, tana dubawa tana murmushi har ta k’arasa karantawa tana cewa,

“Wannan mutumen da abun dariya kake wallahi, wannan game d’in taka har ta fara burgeni.”

Ajiye wayar tayi ta sauka domin rik’ama momynta aiki, saboda yau Humairah zata dawo hutu, shi yasa ake shirya mata liyafa.

Bayan dawowar Humairah hutu da kwana biyu, sai taga auntyn ta-ta, ta changer, ko yaushe da waya a hannu, wanda ko shigowa tayi d’akinta fira, sai ta ga hankalinta yana wani wuri, har saida Humairah ta fara k’orafi akan ta daina yin fira da ita.

Momyn ma haka, ta lura da Anwarah sosai. Anwarah ta kasance ko yaushe tana jiran text d’in Faisal. A rana d’aya sai ya shareta bai turo mata ba,nan take sai taji duk babu dad’i, hakan yasa ta d’auki wayarta da danna number d’in da ake yi mata text da ita ta kira.

Karo na farko kenan da Anwarah ta ta’ba kiran wani, ba ‘bata lokaci Faisal ya d’auki kiran amma baiyi magana ba, hakan ya saka Anwarah yin magana cikin sanyin murya da cewa,
“Don Allah wai da waye nike magana? Maza da yawa, idan suka kira sau biyu ko ukku, idan na korasu basa dawowa, meyasa kai ka nace a sona?”

Ba musu Faisal ya amsa mata da cewa,

“Saboda son da suke yi miki, duk na k’arya ne, ni kuma akanki zan iya rasa rayuwata, domin tun ranar da na had’u dake, na kasa aikata komai a rayuwata, sai kallonki a ‘boye, sai tunaninki. Don Allah Anwarah ki soni.”

Sabon yanayi Anwarah ta fad’a, jin muryarshi kawai ta saka Anwarah fad’uwa kwance, tana sauraronshi tana raya wani zance a zuciyarta.

‘ Ikon Allah! Wallahi naji zuciyata na karaya da bawan Allah d’in nan, me ke shirin faruwa da zuciyata? Naji kalmar bakinshi kawai ta soma had’uwa da zuciyata, ya salam! ’

Zancen zucin Anwarah mai tare da sabon yanayi, sai kuma salon bayaninsu a waya ya sauya, ko yaushe Anwarah da waya a hannunta, har humairah ta gama hutunta ta koma, bata samu wata doguwar fira ba da yayar ta-ta, haka ta koma school domin taga sabuwar rayuwa take yi.

Ko yaushe Anwarah da Faisal ana manne a waya, wanda idan Anwarah ta bashi izinin zuwa gidansu, sai ya ce mata, zai zo amma ba yanzu ba.
Anwarah bata iya tilastashi yin komai, don haka sai ta dinga share zancen son ganin nashi.

Iya yanzu son Faisal ya kama Anwarah, domin babu abinda tafi k’auna a rayuwarta, kamar taji muryarshi a waya, a nan soyayyar Faisal tayi k’arfi a zuciyar Anwarah sosai, wanda take jin babu wani d’a namiji da zata so bayan Faisal d’in.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button