BAKI BIYU COMPLETE HAUSA MUSIC

Lokacin da Faisal ya gane cewa, Anwarah ta kamu da sonshi sosai, shine ya nemi izininta da su had’u, inda suka had’u, har suka ga juna.
★★★★★★
Bayan Anwarah sun rabu da Faisal ne, ta kamo hanya ta dawo gida, duk jikinta a mace, don haka sai ba ta biya gurin Suhailat ba.
Son Faisal ya shiga zuciyar Anwarah sosai, wanda take jin a yanzu zata iya sanar da kowa irin son da take yi ma Faisal. Don haka a yanzu bata tsoron kiran Faisal ya shigo wayarta ko a gaban su baffa ne, sai dai ta d’auki wayar tayi sama da gudu tayi wayarta.
**********
Soyayya mai tsanani ke tsakanin Anisah da Anwar, domin suma ko yaushe suna tare a waya, wanda ko yaushe Anwar ji yake yi babu wata mace bayan Anisah, ita ma tana jin hakan, duk da son nata kamar da BAKI BIYU take yi mishi shi, amma kuma tana jin zatayi al-fahari da auren matashin saurayi mai kyau, kuma mai tashen kud’i, kuma sai gashi a jerin mazan da take so su zama nata, wato yayi karatu a India, kuma ya dawo Nigeria a cikin daular mahaifinshi idan ya mutu. Don haka take jin Anwar d’in yanzu a zuciyarta, domin duk son da take yima Nuraddeen, a yanzu bata jinshi kamar Anwar d’in.
Anwar ya k’ara kyau, domin dashi da d’iyan Indiawan, banbamcin kad’an ne, shima sai in an ambaci daga Nigeria ya fito, Anwar akwai kyau sosai, domin shi fari ne tas! Hakan yasa yake son Anisah, domin itama fara ce tas! Kamarshi, don haka yake ganin zasu samu flowers babys idan sunyi aure.
Soyayya a ‘bangaren masoyan Hud’u tanata yad’uwa, inda ko wanne daga cikinsu ke nuna k’aunar abokin soyayyarshi, sai dai biyu don Allah suke yi, biyu kuma da BAKI BIYU suke nuna nasu son.
Watan Faisal 7 a Abuja, ko da waiwaye bai waiwaya garinsu ba, ko yaushe cikin yi ma matarshi k’arya yake yi da baya k’asar, an turashi waje yin wani aiki, amma ya kusa gamawa zai dawo.
Faisal na son Anwarah so mai tsanani, sai dai tashi soyayyar yafi sonta da rayuwar turawa, domin in son samunshi ne, ko yaushe ya rink’a rik’a hannun Anwarah, har ta saba dashi, ta hakan sonshi zai dinga k’arfi a zuciyarta, har takai tana yadda dashi kamar yadda ya so, daga nan ma zai aureta, sai ya ajiyeta anan kaduna, ta yadda ba kowa na danginshi zasu sani ba, kuma shima ba zai sanar da ita cewa ba, yana da mata.
Lokacin da su Anwarah suka samu hutu ne a makaranta, sai fita tayi mata wuya, indai ba suhailah bace ta zo, ita kuma suhailah tunda ta gane cewa, Anwarah ta kamu da son Faisal, sai ta daina yi mata maganar yayanta, kuma babu ruwanta da zancen faisal ko kad’an bata shiga. Anwarah tayi bata hak’uri akan hakan, amma suhailah ta ce ba zata iya goya mata baya ba. Don haka sai Anwarah ta shareta da zancen Faisal d’in.
Akwai ranar da Faisal ya kira Anwarah suna waya, yake rok’onta da tazo ganinshi masaukinshi, domin bayada lafiya sosai, Anwarah taji duk babu dad’i, amma kuma gaskiya ba zata iya zuwa masaukinshi ba, domin ba girmanta bane, kuma ba girman mahaifanta bane, amma zata iya aika driver da sak’o ya kai mishi, ita ba zata zo ba.
Faisal yayi jiran Anwarah, amma Anwarah bata je ba, sai dai ta aika da kayan jinya iri-iri a mota aka kaimishi, domin taci sa’a ranar momynta na duty night, Baffa kuma ba a part d’insu yake ba, bayan ta aika mishi da kayan jinya irin na soyayya, sai ta rufe part nasu tayi part d’in Mama, wato mahaifiyar Anwar ta kwana.
Faisal baiji dad’in wannan sak’on nata ba, amma kuma ya nuna mata yaji dad’i, wanda ta ce ya yanke time d’in da zai zo gidansu, domin ita ba zata k’ara zuwa inda yake ba.
Bai yi musu ba ya kar’ba, da yanke cewa, next week zai zo insha’Allah!.
Anwarah taji dad’i sosai, domin tun ranar take shirye-shiryen zuwan sahibinta, wanda har sai da ta bama mama labarin Faisal d’in cikin jin kunya, mama tayi murna sosai da jin hakan, ita ma ta bata ta-ta gudumuwar a taron surukin na su, sannan ta yaba da hankalin Anwarah d’in.
Bata rufe ma momyn ta-ta komai ba, ta sanar da ita zuwan Faisal d’in, itama taji dad’i, domin tana son duk abinda ‘yar ta-ta ke so. Hakan yasa momyn ta sanar da Baffa duk abinda ke faruwa a gidan, Baffa ya nuna murnarshi, amma kuma bata kai ciki ba, domin ba haka ya so ba, amma baya son ya dinga ‘bata ma momy d’in da Anwarah shirinsu, domin Al-k’awarin da ya d’auka tun farko, zai dinga basu duk abinda suke so.
Ya sanar momy cewa, ayi duk abinda ya kamata na taron bak’on, amma yana son yaga yaron duk ranar da yazo, momy ta amsa mushi da jin dad’i, sannan ta sanar da Anwarah yadda sukayi da Baffa.
Anwarah tayi murna sosai, sannan ta sanar da Faisal d’in abinda iyayen nata suka ce. Gaban faisal ya fad’i, sai dai ba zai iya rasa wannan damar da ya samu ba, zai zo suma ya sakar musu tasu bayanin dai-dai yadda ya so fitarshi a bakinshi, shi fa baya rasa burinshi ta ko wane hali ne, sai ya mallaki, zuk’ek’iyar yarinyar cen da yake so, don haka ya aminta da zuwan, da kuma ganin mahaifin nata.
Ranar da zaizo, ta kira suhailah da itama tazo, amma Suhailah tak’i zuwa, Anwarah ta tabbatar da Suhailah na taya yayanta kishi ne, amma ko ma yaya ne dai? Ita fa tana son Faisal d’inta sosai.
Lokacin da Faisal ya yi alk’awarin zuwa na cika, shi kuma ya na shigowa layin da akayi mishi kwatance, tambaya d’aya kawai yayi aka nuna mishi gidan Alhaji Muktar Ahmad Baffa. Tunda Faisal ya hango get d’in gidan yasan cewa, Anwarah ba ‘yar k’ananan mutane bace, ma’ana; ba irin d’iyar k’ananan masu kud’i bace a garin Abuja. Gaban Faisal ya fad’i, kamar Faisal ya juya da motarshi, amma kuma sai ya tuna da kaifin Harshenshi da bakinshi, sai ya tura kan motarshi ya iso bakin get d’in da yin hon da k’arfi.
Mai gadin gidan na zaune da redio a hannunshi, da sauri ya bud’e get d’in Faisal ya shigo cikin gidan. Mai gadi na rufe k’ofar get d’in, ya rugo da gudu da gaishe da shi. Faisal ya bud’e motarshi shima ya fito da cire wayarshi a aljihu yana kiran layin Anwarah.
Anwarah na gaban madubi ana d’aura d’ankwalin atamfar jikinta, tayi kyau sosai, sai kiran Anwar ya shigo wayarta, da sauri ta d’auka da cewa,
“Sannu da isowa d’an k’aramin gidanmu sahibi na.”
“Yauwa! Sahibata, gani ina jiran isowarki gareni.”
“Kafin na fito, ga Asabe nan zata shigo da kai a d’akin da na tanada domin ajiye sahibina.”
“Okey! Ina jira.”
Duk wayar da suke yi, Anwarah na sama tana kallon Faisal, yayi mugun kyau sosai, wanda sai da tayi minti biyar tana kallonshi, bata k’ara katsewa ba, sai da ta hango shi ya bama mai gadin gidan kud’i masu yawa a hannunshi, nan take Anwarah ta k’ara jin cewa, ta samu mijin da ta dad’e tana buk’atar son ta aura. Ashe ranar da suka had’u a restaurant bata tsaya ta kalleshi da kyau bane, domin tsoron da ke zuciyarta, amma Faisal d’inta mai kyau ne, kamar yadda zuciyarta ke raya mata.
Asabe ce ta shigo da Faisal a wurin da ake sauke bak’i na musamman, wurin kawai ya isa ya tabbatarwa da Faisal cewa, Anwarah ‘yar gata ce a gidan, domin an k’awata wurin da kayan gyaran d’aki, sannan d’aki ne, amma kuma mai kama da wurin shan iska.
Banda k’amshi babu abinda wurin ke yi, don haka Faisal ya samu wuri ya zauna tare da jawo wayarshi da ke aljihunshi na gaba. Faisal bai k’arasa kallon wurin ba, sai ga kayan ci da sha ana shigowa da su, wad’anda aka jera wurin zamansu a wani makeken center table, duk wasu kayan dad’i da kasani, akwai shi wannan wuri a jere.