BAKI BIYU COMPLETE HAUSA MUSIC

Ringing d’in wayar Faisal ya shigo, inda ya ga sunan matarshi Binto ne ‘baro-‘baro a wayar shi yana yawo, tsaki Faisal yaja da cewa,
“Wannan yarinyar akwai ‘yar bak’in ciki da shegen nacin tsiya, son take yi ta jawo mini tsiya, na ga samu naga rashi.”
Datse kiran yayi, da tura mata text cewa, “muna meeting ne, idan muka k’arasa zan kiraki.” ya tura ma Binto, sannan ya rufe layukkan nashi baki d’aya.
Sallamar Anwarah yaji a bakin k’ofar shigowa, wanda sai da ya sakar mata murmushi irin na jan hankalin yaudara, sannan ya Amsa sallamar. Murmushi Anwarah ta saki wanda sai da dimple point d’inta ya fito. Faisal ya yi mutuwar zaune, domin a yau ta fi ko yaushe kyau, ji yake yi kamar ya taso ya rungumeta, amma kuma tsoro yake ji kada ya sa’ba number, domin yasan Anwarah ba irin ‘yan matan shi ba ce, amma kuma shifa yafi gane ana kusa-kusa.
Anwarah ta samu wuri ta zauna kujerar da ke kallon kujerar da Faisal yake zaune, tare da gaisheshi cikin jin kunya, domin tunda ta shigo ita yake kallo, duk sai taji kunya ta kamata. Amsa mata yayyi tare da tambayarta mutanen gidan, Anwarah ta amsa mishi kowa k’lau yake.
Bayan sun d’anyi firarsu ta soyayya kamar yadda suka saba, sai Anwarah ta gabatarma da Faisal da kayan ciye-ciyen da akayi domin shi. Faisal ko kallon kayan bai yi ba, domin akwai wata manufa da yake son yayi da hakan. Anwarah duk taji babu dad’i, domin a ganinta ko bata burgeshi da wannan girke-girken da akayi ba, domin tasan wannan ko gidan shugaban k’asa sai hakan, amma shi yayi ko oho da kayan abincin. Anwarah tayi k’arfin hali tace,
“Habibi na! ga fa ruwa nan kasha.”
Kallonta ya yi, sannan ya d’aure fuska yace,
“Hmmm! Ni fa kallonki kawai ya isa ya k’osar dani, amma kuma zan iya shan abin sha ne, idan har ki ka taso da kanki ki ka bani na sha, My Anwarah ko kin manta ni ne mijin da zan aureki? Wallahi ina sonki so na gaske, amma kuma sai nake ganin kamar ba zaki iya shagwa’bani ba kamar yadda mama na ke yi mini ba, idan ina a gabanta, ba zata barni na yi komai da kaina ba, domin son da take yi mini.”
Anwarah na sauraronshi, amma kuma ta kasa d’aga idonta ta kalleshi, sai dai ta samu zuciyarta da bata umurnin ta shi ta bashi duk abinda yake so.
Murmushi yayi da yaga Anwarah ta matso kusa dashi, babu abinda ke jan hankalinshi kamar k’irar halittar da Allah ya yi mata, kuma idan zai samu hali, to zai kai hannunshi zuwa ga jikin nata, amma tsoro yake ji.
Anwarah ta fara zuba mishi drink, sannan ta jawo snacks d’in da ke gurin iri-iri ta matso da k’aramin tabale d’in ta aza mishi, da mik’o mishi jus d’in da ta zuba a cup, k’in kar’ba ya yi, sai dai ya jawo hannunta ya zaunar da ita gefen kujerar da yake zaune da turo mata bakinshi Alamar ta bashi yasha.
Ba musu Anwarah ta bashi sau d’aya, sannan ta ce mishi ya kar’ba, saboda hannunta da ke hannunshi take son ta kar’ba, saboda kallon da taga yana yi mata, shi ke firgita ta.
Wani salon rik’a hannu taji, yatsanshi d’aya a cikin yatsanta d’aya, sai ta ji jikinta duk babu dad’i kamar irin ranar nan da suka fara had’uwa. Kar’bar glass cup d’in yayi ya ajiye a kan table d’in sannan ya rik’e hannuwan nata duka biyun da hannunshi ya kalleta ya yi murmushi yace,
“Ganinki kawai yafi mini dukkan wad’an nan kayan dake gabana Anwarah, idan ina tare da ke, nakan ji komai nawa baya aiki, sai na ganki kusa dani, hakan ya sa nake jin da wuri zan turo iyayena domin ayi mana baiko ki fara zama tawa Anwarah.”
Anwarah taga nawar ya saketa ta tashi a gurin, domin bai kamata ba a ganta a hakan ba, ita da shi, bayan ba aure sukayi ba, gashi k’irjinta kawai yake kallo, cikin sauri Anwarah ta ce,
“Zan shiga na sanar da Baffa isowarka, domin yace idan ka zo na sanar dashi.”
Anwarah ta k’wace hannunta ta fita d’akin jikinta na rawa, domin duk tsoro ya kamata, irin kallon da Faisal d’in ke yi mata, gashi bata saba da irin hakan ba, dole taji daban.
Directly d’akin Baffa ta nufa da yin sallama, yana falonshi zaune, ya bata izinin shigowa. Suka gaisa kamar yadda suka saba duk lokacin da suka shiga d’akin nashi, ya amsa mata cikin jin dad’i, sannan Anwarah ta sanar dashi zuwan Faisal d’in.
Baffa yace ta yo mushi jagora zuwa falon nashi domin suyi magana. Ba musu Anwarah ta koma suka zo tare da Faisal d’in, ta nuna mishi k’ofar falon na baffa, sannan ita kuma ta shiga d’akin momy cikin farin ciki.
Bayan sun gaisa, Baffa yake tambayar Faisal shi d’an ina ne, kuma suwaye iyayenshi?
Faisal gabanshi ya fad’i, domin ba zai iya fad’in iyayenshi ba, saboda ba za’a d’aukeshi da daraja ba, kamar yadda yaga nasabar Anwarah cikin daula.
K’ir-k’iro k’arya yayi da cewa, mahaifinshi ya rasu, mahaifiyarshi kuma tana a jigawa, shi kuma wurin yayan babanshi yake zaune a kaduna, yayan baban nashi, shi ke kula da company mahaifinshi na yin atamfofi, wanda kowa ya san A.JIGAWA COMPANY da ke kaduna. Sai dai shi yana aiki ne a pension office ne da ke kaduna, kuma shi da aure yake son Anwarah.
Baffa kallonshi kawai yake yi, domin shi nashi buri daban a cikin zuciyarshi, sai dai babu yadda ya iya zai hak’ura da wannan d’in hakan.
Bayan baffa ya gama sauraron Faisal da ya fesa mishi k’arya, sai ya yi mishi ta’aziyar mahaifinshi, sannan yace, idan yaje gida ya turo yayan baban nashi, zasu yi magana.
Anan cikin Faisal ya k’ara d’urar ruwa, domin ina zai samu wanda zai yi mishi wannan aikin? Jiki a sanyaye ya mik’e, da bama kanshi Amsa da cewa, ‘ai kud’i na nan, za su gama komai’
Faisal ya dawo, da kiran Anwarah don suyi sallama, kud’i ya sakar mata, da kuma kud’in mutanen gidansu ya bata ta rarraba musu harda na ‘yan aikin gidan.
Momy murna kawai take yi, zata ga auren Anwarah cikin k’urciyarta. Hakan ya sanya ta kira mahaifiyarsu ta sanar da ita, itama murna tayi sosai, jikarta zata yi aure.
Da murna Anwarah ta kwana a ranar, kowa ya yaba da za’binta. Shi kuma da shirin yadda zai ‘bullo ma wannan k’arya da shirya ma kanshi.
★★★★
Baffa ya kira Anwar domin ya sanar dashi k’anwarshi tayi mijin aure, Anwar ya tambaya wace k’anwar tashi? Domin shi babu wadda yake kira k’anwarshi a gidan, face Anisa, domin a gaban kowa zai kirata da k’anwarshi, saboda ita yana wasa da ita, amma su Anwarah gausuwa kawai ke had’asu dashi, saboda basu son musgunawa.
Anwar gabanshi fad’uwa kawai yake yi, domin tsoro yake yi kada ace Anisa ce aka yi ma miji ba a san suna soyayya ba, cikin hanzari ya tambaya da cewa,
“Baffa wace k’anwar tawa daga ciki?”
Baffa ya bashi amsa cikin ruwan sanyi, domin yana son ya fahimci wani abu daga ciki, sai yace mishi,
“Anwarah mana, yau yaron yazo gida har mun gaisa dashi, zai turo iyayenshi akai k’arshe.”
Wata irin ajiyar zuciya Anwar yayi, sannan ya yi murmushi da cewa,
“Amma nayi farin ciki sosai Baffa, ai ya kamata ayi mata aure haka nan, domin ina samun labarin abubuwan da take yi, to ai k’ara ayi mata auren a huta da rashin ji.”
Rayuwar Baffa ta ‘baci, ya rasa me yarinyar cen tayi ma Anwar da ya ke jifarta da miyagun zantuttuka hakan? Don haka shima ya nufi hanyar k’untata mishi da cewa,
“Haka ne! To kaima ai next month zaku k’arasa komai ko? Kuma zaka dawo gida, to idan ka dawo ina son kaima ka fitar da matar da zaka aura, ayi lokaci guda a huta.”