BAKI BIYU COMPLETE HAUSA MUSICNOVELS

BAKI BIYU COMPLETE HAUSA MUSIC

Jin hakan yayi ma Anwar dad’i, domin ko ba’a tilastashi ba, da ya dawo zai bayyana masoyiyarshi ayi musu aure.

Da hakan Anwar ya amsa ma mahaifinshi da cewa, “insha’Allah zan kawo ta baffa.”

Tabbas! Baffa ya gano abinda yake son ganewa, kuma ba komai, hakan ma ai alkhairi ne.

Da hakan aka tsayu da jiran iyayen Faisal………….

page biyu ne wannan ko ukku? Waih! Long pages ne, bashin jiya da yau ne na biya. Muje dai zuwa,ku bini a hankali mun kusa kamo bakin zaren.

Bee²Ta Masoya
[11/3, 8:13 AM] ®Bëë Bëë Tâ Māsôyä????????: ????????????????????????????????????

___________________
♦BAKI BIYU♦
___________________

® REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS P.M.L????????????

ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ

WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM

IG PML WRITERS

©®
Khadija bee bee
Khadijabellobuhari@gmail.com@gmail.com

★★★★★★★★★
Page…8 to 9
★★★★

Faisal ya rasa ta yadda zai had’a wannan tsiyar da ya shikka, ya bazama cikin garin kaduna domin ya samu iyayen haya wad’anda zai tsara musu k’aryar da zasuyi amfani da ita, don kada yasha kunya.

Faisal yana da aboki k’waya d’aya a garin kaduna Ishak’a, Ishak’a k’wararre ne a ko wace sana’a kazo da ita ta k’arya, domin shi yana da permanent mutane masu yi mishi aiki ya biyasu.

Faisal da ya rasa yadda zai yi kuma gashi bashida mafita akan hakan, sai ya nemo abokin nashi yake bashi labarin abinda ya faru, da kuma abinda yake shirin ya yi.

Ishaqa ya ci dariya sosai, domin wannan ai ba wani aikin damuwa bane a gurinshi, domin ya sa anyi mishi wanda yafi wannan ma. Ishaqa ya tambayi Faisal cewa, da gaske yana son yarinyar? Faisal ya amsa mishi da cewa, Tabbas! Yana sonta, sai dai yasan cewa, idan har ya bayyana mata asalin ko shi wanene? Ba zata yarda dashi ba, hakan yasa ya zo mata a irin wannan matsayin ita da mahaifanta.

Ishaqa ya fahimci duk abinda Faisal ke nufi, don haka sai ya shaida mishi cewa, ya tanadi kud’i masu yawa, domin dole sai an jik’e mutanen da kud’i, kuma sai an samu manyan kaya da motoci a wannan tafiyar, sannan da kud’in da zasu saki idan sunje gidan. Faisal ya aminta da hakan, domin shi dai ko ta yaya ne ya mallaki Anwarah, bayan ta zama tashi, ko ta yaya ne? Ai ta zauna a yadda yake.

Kasancewar cuwa-cuwar da su Faisal ke yi, sai ya kasance, ko waya a rana sau d’aya suke yi da Anwarah, domin ya fad’a mata aiki suke yi, ko waya wuyar d’auka take yi mishi saboda busy. Anwarah bata damu ba, domin itama sun koma makaranta, karatu ya yi mata yawa, amma tana tura mishi text shima yana turo mata.
**
Anisah ta samu labarin zuwan wanda ke son Anwarah d’in, don haka take sanar da Auntynta abinda ke faruwa. Aunty zuwairah ta sanar da Anisah cewa, ai tana sane da duk abinda ke faruwa, amma shi mai gidan bai sanar da ita ba, ba komai su ba Anwarah ce a gabansu ba, Anwar shine a gabansu, kuma so suke yi a had’a lokaci guda ayi auren da nasu.

Anisah ta yi murna da jin hakan, domin itama burinta bai fi a ce yau ne ranar aurensu ba, ko ba komai zata fancama a cikin ‘yan uwa da abokai ta auri d’an d’an masu kud’i, kuma duniya zata shaida hakan.

Bayan sati d’aya Faisal ya sanar da Anwarah zuwan mahaifanshi a gidansu, domin ta sanar da Baffanta zuwansu, Anwarah ta sanar da momynta ta sanar da baffa yadda Faisal ya fad’a mata. Momy da murna ta sanar da baffa d’in, sannan yayi addu’ar Allah ya kawosu lafiya.

Kwana biyu da yin hakan, sai ga ‘yayan mahaifin Faisal ya zo shi da abokanshi guda biyu. Ba laifi baffa yaga kamala a tare dasu, sannan suka gabatar da kansu kamar yadda suka tsara, tare da mayar da labarin da faisal ya fad’a ma baffa, shima babu wanda yayan mahaifin faisal bai fad’a ba, hakan yasa baffa yadda da gaskiyar Faisal d’in.

Babu ‘bata lokaci, yayan baban faisal na k’arya, ya tambayi baffa da abasu izinin biyan sadaki a yanzu, domin su basa son wasa, saboda dama shi burinshi yaga yaron ya yi aure, domin ya mallaka mishi dukiyar mahaifinshi a hannu. Baffa kamar zai yi musu da zancen, saboda nan take babu wata shawara da ‘yan uwa za ya kar’bi sadaki? Amma kuma sai yaga ai babu komai, tunda suma ai burinsu suga Anwarah tayi aure, domin itama suyi mata nata gatan, k’arshe su mallaka mata dukiyarta a hannunta su huta, duk da kasancewarta yarinya.

Baffa ya yanka musu sadakin Anwarah dubu Hamsin, domin shi baya son riya a fagen neman aure, domin a rangwanta, shi ke saka aure albarka, ba almubazzaranci ba.

Yayan baban Faisal na k’arya ya dubi tsarin gidan, da kuma kayan da ke cikin falon kawai, yasan cewa a gidan kud’i suka yanke cibi, sai da gabanshi ya fad’i, domin ya san gidan mutunci ne, aka zo turo su, su yaudari iyayen yarinya, haka nan dai ya dake yace,

“Alhaji a gaskiya ni ban yarda da abinda zaka yi muna ba, ai darajar gida da kuma yarinyar ake dubawa, shi yasa ake kyautata sadakin yarinya, don haka mu zamu bada sadakinta a dubu d’ari biyu.”

Baffa bai aminta da hakan ba, amma ya kar’bi dubu tamanin shima sai da suka dad’e da magiya ya kar’ba.
Sunyi sallama da cewa, za su kawo lefe nan da wata d’aya, domin ba su son a d’auki lokaci. Baffa ya aminta da hakan, da yi musu rakkiya har bakin motocinsu.

Ba laifi Baffa ya yarda da abinda suka zo dashi, akwai mutunci da kamun kai, domin ganin basajar da suka zo mishi da ita, ta salihan mutane, manya masu kamala.

Baffa ya sanar da momy yadda sukayi da iyayen Faisal, kuma su da zafi-zafi suka zo, suna son ayi auren nan da wata biyu, yanzu hakan har sun biya sadakin Anwarah, dubu tamanin, da dubu d’ari biyu zasu bayar, yaga ba shine cikar aure ba.

Momy taji dad’i sosai, hakan yasa ta sanar da kowa da kowa ‘yan uwa, an kawo sadakin Anwarah, itama Anwarah taji dad’i da ta samu labari. Kafin ma ta k’arasa farin cikin har sahibin nata ya turo mata text.

Da hakan aka tsaya sauraron Faisal a kan kawo lefen da suka buk’ata a jira. Soyayya me k’arfi ke shiga zuciyar Anwarah babu kama hannun yaro, tana k’aunar mijin da zata aura sosai, hakan yasa ko yaushe ya buk’aci ganinta, bata iya yi mishi musu, akan ya zo tana jiranshi. Wajibi ne duk randa zai zo, Anwarah sai ta yi mishi girke-girke. Kasancewar ya biya sadakin Anwarah, shiyasa babu wanda ke ganin wautar Anwarah akan Faisal d’in.

Kasancewar momy nada tsohon ciki, sai zancen zuwa dubai da ita ya fasu, domin dama acen sukayi al-qawarin sayowa Anwarah kayan d’aki, amma kuma tafiyar da ita bata samu ba. Momy bata ji dad’i ba ko kad’an, amma kuma duk abinda tayi niyyar yiwa Anwarah bata fasa ba, domin doguwar ajiyarta ta faso, wadda tayi alk’awarin bud’eta a auren Anwarah, ta ba da baffa ya tafi da nashi k’udurin kuma.

Duk abinda ake buk’ata na kayan d’aki da wata kwalliya ta gida, baffa ya siyo su a dubai, jiran kawo su kawai ake yi bayan ya dawo.

Rayuwar su Anwarah nata gudana akan soyayya ta nufin aure, duk kunyar Anwarah, a yanzu ta fara rageta, domin ta riga da ta san Faisal ne mijinta idan Allah yaso. Hakan yasa bata iya hanashi rik’a hannunta, shi kuma dama haka yake so.

Ana cikin shirye-shiryen bikinsu Anwarah ne momy ta haihu, ta samu baby boy, murna ba’a cewa komai a gurin kowa, amma banda zuwairah da har yanzu a tutar babu ake, an nema kamar a mutu, amma ba’a samu ba, Ranar kamar wadda ke bori, domin duk ta ya mutse, har sai da Anisah ta fahimci wani abu daga gareta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button