BAKI BIYU COMPLETE HAUSA MUSIC

Anisah ta kwantar mata da hankali da cewa, “Aunty menene abun damuwa anan? Idan dai rik’a gida ne, ai mun riga da mun kar’ba, kada ki manta fa mun riga da mun siye zuciyar Anwar, sannan This week yana hanya Aunty, da ya dawo aurenmu za’ayi, kinga kenan sonda mahaifinshi ke yi mishi, zai iya mallaka mishi komai, kinga yana mutuwa, duka gidan a hannunmu yake, don Allah Aunty ki daina damuwa.”
Zuwairah ta ji zuciyarta tayi sanyi da jin maganganun Anisah, tabbas! Tasan hakan zata faru a cikin k’an-k’anin lokaci, don haka sai bata damu ba, suka fara shirin taron Anwar daga dawowarshi a makaranta.
Anisah kwana ukku ana gyara part d’in Anwar, duk wani abu da ya kamata ya nema, Anisah ta tanadar mishi, sun zama uwarshi, domin ita bata saka hannunta akan duk wani al-amari nashi, domin tsananin kunyar Anwar da take yi a matsayinshi na d’an fari.
Ranar sunan babyn momy, da yaci sunan baffa, wanda aka sakama suna MUKTAR(IMAM), Anyi shagali har shagali, domin anyi taro naji da fad’i, duk wanda yazo bikin Imam, da gift d’inda yake fita, akayi taro aka k’are lafiya.
A daren ranar da akayi sunan Imam, a daren jirgin su Anwar ya sauka gida Nigeria, a filin jirgin da ke Abuja. Anwar ya changr sosai, duk wanda ya sanshi a shekaru biyu da suka wuce, ba zai iya shaidashi ba a yanzu.
Baffa ne da kanshi ya je ya d’auko Anwar, wanda a cikin mota yake bashi labarin k’anen da Momynsu ta samar musu, Anwar yaji dad’i sosai, har yaji yana son ganin yaron.
Isarsu gida, da sauri ya fad’a part d’in mahaifiyarshi, inda babu laifi yau ta saki fuska da ganin d’an nata, domin har da tambayarshi ya hanya ya karatu, kuma har ta bashi labarin Auren Anwarah da za’ayi da kuma haihuwar Imam, Anwar yaji farin ciki sosai da firarshi da mahaifiyarshi.
Bayan ya fita nan, ya shiga part d’in aunty zuwairah da zumud’in yaga sahibarshi, sai dai ya tarar da kayan ci da sha iri-iri, amma ita bata nan, tana wurin gyaran kai inji Auntyn tata. Hakan ya sa bai dad’e ba ya yi part d’in momy domin su gaisa, kuma yaga baby.
Part d’in momy ya shiga, inda suka ci karo shi da Anwarah a falo tana goye da Imam momy na wurin wanka, hannunta rik’e da waya tana fira da sahibinta. Mamaki ya kama Anwarah, domin bata san lokacin da ya dawo ba, kawai ta ganshi ne a yanzu.
“Yaya Anwar ina wuni?”
“Lafiya k’lau.” Ko kallon inda take bai sake yi ba, yayi hanyar d’akin momy, ita kuma tunda bai tambayeta ba, sai ta shareshi ta ci gaba da aikinta, ai zai dawo idan bai ganta ba.
Shiga d’akin nata da yayi, sai yaji shiru, hakan ya sa shi dawowa falon da ce ma Anwarah,
“Ke ina momy take ne?”
Anwarah na waya, tayi kamar bata san me yake cewa ba, sai da ya ambaci sunanta sannan ta sauke wayar da cewa,
“Dear ina zuwa, zan kiraka.”
Sannan Anwarah ta juyo da cewa, “me ka ce?”
“Yar rainin hankali kawai, in banda iskancin banza da rashin kunya, ana yi miki magana kina kallon mutane a karkace, halan ke wacece? To ki sani kowa da gidansu yake ado, ba gidan wasu ba, banza mara kamun kai.”
Anwar ya fad’a ma Anwarah son ranshi, sannan ya kama hanya ya fita a falon.
Anwarah kasa komai tayi, face kuka da ya maye gurbin farin cikin da ta ke ciki,
“Wai me na tare ma yaya Anwar ne? Wai ko dai da gaske ba babanmu d’aya ba? Saboda k’iyayyar tayi yawa tsakaninmu.”
Jefar da wayarta tayi a falo, ta yi hanyar d’akin momyn da kuka.
Fitowar momy kenan daga wanka taji abinda ba ta ta’ba ji ba, wato kukan Anwarah, da sauri ta tareta da cewa,
“Lafiya Anwarah? Waye babu lafiya? Me ya samu Faisal d’in?”
Da sauri momy ta matso kusa da ita, da kar’bar babyn da ke bayanta, sannan ta rik’a hannunta suka zauna gefen gado. Momy ta ajiye Imam da ke barci, sannan ta k’ara tambayar Anwarah abinda ya faru.
“Momy me ya sa yaya Anwar ba ya sona a cikin ‘yan uwa? Ni kad’ai ya tsana, a duk lokacin da na ganshi, ko da ina cikin farin ciki ne, sai ya yi k’ok’arin ganin ya k’untata mini. Don Allah momy ki fad’a mini, me ya sa ko yaushe yake fad’a mini cewa, kowa da gidansu yake ado, ba da gidan uban wasu ba? Shin momy ko ni ba baffa bane mahaifina……”
“Anwarah….!” Momy ta kira sunanta cikin fushi da cewa, “Tunda ki ke a rayuwarki kin ta’ba jin baffanku ya fad’a miki maganar da tayi kama da bashi ne mahaifinki ba?”
Anwarah ta girgiza kai da sauri, alamar A A. Sai momy ta k’ara rik’a hannun Anwarah cikin sigar rarrashi ta ce,
“Don haka, duk wani da zakiji yana wani zance, to kawai ya fito a bakinshi ne domin kawai ya ga kina fushi, saboda Baffanku yana sonki Anwarah. Daga yanzu duk abinda Anwar zai k’ara yi miki, kada ki koma damuwa, halinshi ne hakan, ya cika masifa da zuciyar banza, ki dinga saka mishi ido kawai a duk abinda zai yi, kuma amma ke Anwarah baki yi mishi komai ba kuwa?”
“Wallahi momy komai banyi mishi ba, ya dai shigo ya tarar dani a falo, na gaisheshi, sai da ya d’age kanshi sannan ya amsa mini gaisuwar, ni kuma da na ga hakan, sai nima da ya tambayeni, na shareshi ina wayata, shine fa ya dinga yi mini masifa.”
Murmushi momy tayi, sannan ta ce ma Anwarah, “Duk abinda Anwar ke yi, ba laifinshi bane, laifin wasu ne, kuma da k’arfin addu’a ba za suyi nasara a garemu ba, ni dai burina da ke shine, ki daina damuwa da halinshi, ke da kwanaki kad’an suka rage miki ki tafiyarki ki barsu, don Allah ki daina kula zancen su kinji?”
“Insha’Allah momy zanyi hakan, yauwa! Dama ina son na fad’a miki cewa, Mama ta bani wasu magani a cikin robobi manya, ta ce na dinga sha da madara, wasu kuma da zuma zansha, suna d’aki na ajiye, zan kawo ki gani momy, ni fa wallahi bani son kayan d’aci wallahi.”
Momy ta fahimci abinda Mamar Anwar ta bata, wato kayan mata na k’ara ni’ima ga d’iya mace, don haka sai taji son mamar na shiga zuciyarta, domin ita mace ce, wadda ta san kanta, halinta mai kyau ne, ba ruwanta da wani kishin banza, ita dai kanta ta sani.
Momy ta ce ma Anwarah, “Duk abinda mama ta baki, Anwarah kiyi amfani dashi, domin nasan mama ba zata ta’ba cutar da ke ba, kuma zata baki abinda zai amfaneki, ki daure kisha kin ji, nasan zaki ji dad’insu.”
Ba musu Anwarah ta yarda da abinda momyn ta, ta fad’a mata, don haka sai taji zuciyarta ta wanke baki d’aya, babu wata sauran damuwa. Har zata fita a d’akin da murna, sai momy tace, “Yaufa k’anwarki na nan dawowa, Sun samu hutu, Antura driver yaje ya d’auko ta.”
Anwarah ta turo baki da cewa, “shine momy aka k’i fad’a mini da wuri, don nayi shirin taronta?”
Ta fita d’akin da fushi, momy na kiranta tak’i dawowa.
★★★★
Gidan a yanzu kowa ya na nan, don haka kowa rayuwarshi yake yi, babu ruwan kowa da kowa, sai dai Su Anwarah ko yaushe suna shiga part d’in mama su shawo firarsu, wanda a yanzu Imam ma baki d’aya ya dawo part d’in mamar da zama baki d’aya.
Idan momy ta zo d’aukarshi, sai ya gallara kuka, hakan yasa sai ta dinga shareshi. Wani ikon Allah kuma shine, Allah ya had’a jinin Anwar da Imam, idan zai yi shigowa d’aya, sai ya d’auki Imam sau biyu, hakan yasa yaron da yaji motsin Anwar, ko bacci yake yi zai tashi.
Kasancewar ciwon mahaifiyar baffa ya tashi, sai aka d’aukota aka dawo da ita a nan Abuja, dama da part d’inta, ko yaushe momy ce da Mama kawai ke kula da ita, zuwairah tunda ta shigo ganinta sau d’aya bata k’ara shigowa ba, wai Hajiya ba ta sonta saboda ita bata haihu ba. Su Anwarah suma suna shigowa sosai, domin a yanzu sun mayar da shiyar tata, gurin fira, sai dai Anwarah na zama ne idan har ta tabbatar da Anwar baya nan.