BAKI BIYU COMPLETE HAUSA MUSIC

Bayan dawowar Anwar, Baffa ya wakiltama Anwar kamfaninshi guda d’aya na motoci da ke nan cikin garin Abuja, Hakan yasa yanzu Anwar baya cika zama gida. Idan har kuma yana gida, to ko yaushe yana tare da Anisah a part din Aunty zuwairah, ko kuma bayan lambun gidansu.
Baffa ya lura da irin yanayin kasancewarsu, wanda sai da yaji babu dad’i a rayuwarshi, amma tunda yaga kamar hankalinsu ya karkata da juna, k’ara ya had’a meeting domin su kawai, yaji yadda zancen yake.
Kwana biyu da hakan,Baffa ya had’a taro a part d’in Hajiya, kuma yace yana son ganin kowa har Anisah. Lokacin da aka saka taron, kowa da kowa ya halacci majalisin.
Hajiya na zaune a d’ayar kujerarta ta zaman mutun biyu, haka baffa yana zaune a d’ayar kujerar ta zaman mutun d’aya. Mama da Aunty zuwairah da Momy suna zaune a kujera mai zaman mutun ukku. Yaran kuma dukansu a k’asa suke, sai dai Imam da ke barci a hannun mama.
Alhaji Baffa ya fara magana kamar hakan,
“Alhmdulillah! Muna gode ma Allah da ya taramu anan, kuma muna rok’on Allah ya k’ara mana yawancin rai da lafiya masu Albarka ameen. Mun taru ne anan domin tabbatar da abinda ni ke son ji abakin wasu, ina rok’on Allah ya sanya ma zamanmu albarka.”
Kowa ya Amsa da ameen. Sannan baffa ya ci gaba da magana,
“Kamar yadda na umurci kowa da halartar mazauni nan, haka ni ke son kowa ya natsu yaji dalilin had’uwarmu anan. Sanin kowa ne cewa Anwar ya k’arasa karatunshi da yaje yi a k’asar waje, kuma Alhmdllh! Ya dawo cike da nasara, bayan dawowarshi kuma, na d’auki kamfani na d’aya na mallaka mishi kafin aikinshi ya fito a inda na samar mishi. To hakan yasa naga kuma ya kai wani mataki wanda zai iya ajiye mata, ba don komai ba, sai don kare martabar kanshi da kuma mu iyayenshi. Hakan yasa na tara kowa anan domin ya zama shaida akan abinda zan fad’a da kuma shi tashi maganar da zai fad’a. Ba tare da ‘bata lokaci ba, Ni ke son na ce da Anwar nan da sati d’aya ya fitar da matar da zai aura, domin shima ya shiga sahun manyan mutane, domin ayi komai cikin lokaci.”
Anwar da sauri ya kalli mahaifin nashi, sannan ya dubi gefen da mahaifiyarshi take da sauran matan mahaifinshi, sannan ya sunkuyar da kai da cewa,
“Baffa ina godiya da dukkan kyautar da na samu a gareka, sannan ina al-fahari da ku a matsayinku na iyaye na, Insha’Allah ba zan ta’ba bari ku ji kunya ba, zan bi umurninku kamar yadda kuke so. Zancen matar da nike son na aura kuma, ai abun ba mai nisa bane Baffa, domin kuwa wadda ni ke son na aura anan gidan take.”
Anisah na ji ta sunkuyar da kai, Anwarah ta d’ago ta kalleta, domin ita dama tasan da tarewarsu, tunda ko yaushe tare take ganinsu suna soyayya a lambun gidan, mama da momy sauraro suke yi suji waye haka Anwar kuma yake so? Domin basu ta’ba ji ko gani ba. Aunty zuwairah kuma murmushi tayi da jin furucin Anwar, domin ta san nasu ne shi ai.
Baffa ya d’ago kanshi da duban Anwar d’in yace,
“To wacece daga cikin gidan naku?”
Anwar babu tsayawa wani nok’e-nok’e yace,
“Baffa Anisah ce.”
Sai da gaban Abba ya fad’i, domin shi dama yasan ita ce, amma wallahi bai san dalilin da yasa yaji hakan ba. Mahaifiyar Anwar kuma, baki d’aya ta sha jinin jikinta, domin ko kad’an bata san sadda Anwar ya fara son Anisah ba. A gaskiya da ace tana shiga al-amarinshi, da ta hana wannan abun, amma saboda bata shiga lamarinshi, shiyasa ta zuba ido da yi mishi addu’ar tabbatar da Alkhairi a ciki.
Momy kuwa murmushi tayi, da nuna jin dad’inta, domin ita bata san ma meke going ba,ita dai addu’ar sanya alkhairi tayi.
Hajiya babba kuma cewa tayi, “Dama da kishiyata nike zaune a gida d’aya ban sani ba, eh lallai! Ashe kuwa zamu buga da ke, miji na shekara da shekaru yanzu zaki rabamu, amma za’aga waya fi so ni da ke.”
Kowa dariya yayi, babu kamar Aunty zuwairah da hakan yayi ma dad’i sosai. Anwarah da humairah kuma, k’asa-k’asa suke magana kada aji me suke cewa, “yaya Anwarah Masu bak’in hali iri d’aya, sun had’u guri d’aya, wai chakwakkiya kenan.”
Anwarah ta rufe baki tana dariya tace, “Ai k’anwata hakan yayi mini dad’i, domin ko ba komai zamu sha kallo, domin ita babu hak’uri shi babu hak’uri, sannan zamu ga yanzu yana son kwalliya ko baya so, tunda mu da muke yi, ya ce muna mahaukata.”
Dariyar k’eta yaran nan suka la’be sunayi, wanda sai da Anisah ta so gano me suke yi, Anwar ma ya fahimci me suke yi, don haka kawai ya kallesu yana harararsu da gefen ido.
Baffa ya nuna jin dad’inshi a fili, da tambayar Anisah cewa, itama ta aminta da zancen Anwar d’in? Ta amsa da ta aminta. Anan baffa yakai k’arshen maganar da cewa, zai ga zuwairah zasuyi magana da ita, domin ayi komai cikin lokaci.
Da haka taron ya watse, da wanda ya so hakan, da wad’anda basu so hakan ba ma, da ‘yan dariyar wurin, duk aka yi dariya aka watse.
Murna gurin Anisah da Auntyn ta ba’a cewa komai, don haka ta fara sanar da ‘yan uwanta da kuma yayar ta-ta domin ta shaida ma mahaifin Anisah d’in neman aurenta da su baffa zasu zo, may b da sadakin auren zai biya.
‘Yan uwan sunyi murna da taka arzik’i da Anisah zata yi, a auren Anwar d’in.
Bayan Baffa ya tabbatar da komai akan son da Anwar ke yi ma Anisah, sai baffa ya shirya shi da abokinshi Alhaji muftahu zuwa nema ma Anwar Aure kamar yadda musulunci ya gabatar. Iyayenta suka ji babu dad’i, domin yarinyar ai a gidanshi ta tashi, ko shi mai aurar da ita ne, bare kuma ya taso da kanshi.
Ya nuna musu ai hakan musulunci ya tanadar. Aka yanka sadakin Anisah Naira dubu d’ari da Hamsin, baffa zai yi magana, amma Alhaji muftahu ya hanashi, domin shi zai yi musu nuni da yadda Annabi yace, shi kuma Alhaji muftahu, girmanshi ya duba da arzik’inshi, sai aka wuce wurin, suka dawo gida. Zuwairah murna kawai ake yi za’a samu mulkin gida a hannunsu, har dai idan Anisah ta haihu.
Aka wuce wannan babin da jiran mijin Anwarah, saboda a yanke ranar auren baki d’aya ayi kowa ya huta.
★★★★
Soyayya mai tsanani ke shiga jikin Anwarah ta Faisal, wanda yanzu ko wane lokaci suna tare, sai dai a fira ma an samu sauyi sosai, domin firar ta kasance kusa da kusa ake yi.
Ana saura kwana biyu akawo lefen Anwarah, kamar yadda Faisal ya fad’a, da daddare Faisal ya kira Anwarah da cewa yana nan tafe. Anwarah ta yi mamakin jin cewa Faisal yana nan tafe, domin 10:pm yayi, hasali ma kowa na gidansu ya shige, su ma har sun saka kayan barci, wayarshi kawai take jira ta kwanta, sai kuma taji kiranshi da cewa zai zo.
Da sauri Anwarah ta tambayeshi ko lafiya? Ya ce mata ita dai zai zo yanzu, zata yarda ya ganta? Ba musu Anwarah ta Amsa mishi da, ya zo tana jiranshi.
Ko 30minutes ba’ayi ba, sai ga hon d’in motarshi a bakin get nasu, waya yayo ma Anwarah da cewa, don Allah ta fito gashi a waje. Anwarah tace mishi, “baffa yana gida, kuma wallahi a sama yake zai iya ganina, ko momy ta gane ni, amma kai ka shigo gani nan ina jiranka.”
Ko kad’an ba haka Faisal ke so ba, amma kuma sai ya k’ara tirjewa da cewa, “Anwarah wallahi mutuwa zanyi, sannan idan ban ganki ba, wallahi zan iya shiga wani hali Anwarah.”
Tsoron jin hakan ya kama Anwarah, don haka sai ta yi sauri ta gyara hijab d’inta ta fita da sauri tana waige-waige. Da sauri ta bud’e k’ofar get d’in ta fita, mai gadi kuma ya shiga toilet yin fitsari, bare ya tambayeta ina zuwa hakan? Saboda basu saba fita a irin wannan lokacin ba, ko Anwar da At namiji baya yin dare a gidan, saboda baya da abokai a abuja, sai kaduna.