BAKI BIYU COMPLETE HAUSA MUSICNOVELS

BAKI BIYU COMPLETE HAUSA MUSIC

Anwarah ta bud’e motar ta shiga da sauri, tare da rufe motar.

Ganin Faisal tayi a cikin wani yanayi wanda bata ta’ba tsintarshi a ciki ba. Da sauri ta kira sunanshi, jin ya kasa Amsawa ta rik’o hannunshi da cewa,

“Dear me ya sameka? Don Allah kayi magana.”

“Ina cikin matsala matata, wallahi bansan ya zanyi da ita ba, kinga yanzu haka daga Asibiti nike, kuma sunce idan ba abinda nike buk’ata na samu ba, kafin safe zan iya mutuwa, don Allah ki tausaya mini ki taimake ni, yau ne kawai na samu lafiya.”

“Me ake buk’ata….. Kud’i ne?”

Cikin firgita Anwarah ta fad’a da rik’oshi baki d’aya a jikinta, domin wallahi ta rud’e sosai, don haka bata san ma tayi ba.

“Wane kud’i Anwarah? Idan kud’i ne ina da su wallahi, sannan kud’i ma za su iya siya mini abin nan take, sai dai ni ba d’an iska bane, ba zan so jikina ya shiga a jikin wata ba, in ba matata ba. Anwarah budurcinki nike so ki sadaukar mini dashi a yau, tunda ni ne wanda zan aureki, yanzu haka komai na lefe na had’a, gobe za’a kawo, kinga idan aka kawo, 2 weeks sai ayi auren mu k’arasa rayuwarmu acen, babu wanda yasan munyi hakan, daga ni sai ke.”

“Budurci na…..!? Innalillahi! Faisal ka kuwa san me kake cewa?”

“Ina sane Anwarah, Ina tsoron ki rasa ni ne, nima na rasaki, likita yace zan iya mutuwa idan har ban had’u da mace ba, a cikin daren nan, don Allah Anwarah ki sadaukar mini da budurcinki na yau, ni kuma zan zamo mai halacci gareki har abada.”

Da sauri Anwarah ta sake shi idonta na zubar da hawaye tace,

“Ba zan iya ba Faisal, ba zan iya zubar da kimar kaina ba, tun kafin na shiga a d’aki na ba, ban ta’ba aikata hakan ba, shin tayaya zan iya jure wannan ranar da na samu labarinta ga k’awaye cewa, ana wahala a duk lokacin da hakan ya faru, to idan na samu kaina a hakan, nayi jinyar jikina a wane guri? A gaban iyaye na? Ko a cen inda abun ya faru zan tsaya? Sannan wane k’unci iyaye na zasu shiga idan suka farka suka ga bani tare da su? Faisal ba zan iya ba.”

“Ashe dama ba sona ki ke yi ba Anwarah? Ashe dama son da ki ke yi mini, bai kai ki bani abinda shine zai ceci rayuwata ba? Tabbas! Da na san haka ne, da ban tsaya na wahalar da kaina ba anan, na tafi gurin wasu karuwai na samu maganin hakan, domin kuwa zan zuba musu kud’i, na biya buk’ata ta, sannan idan na kwaso ciwo, ba zaki sani ba zan sakar miki shi idan munyi aure, shin don na zo gurinki a matsayinki na matata na samu magani shine hakan zai zamo mini da matsala? Ki fita Anwarah daga motar nan, sai dai ina son ki sani cewa, daga yanzu ki fara kukan rasa ni a rayuwarki, domin mutuwa ita ce maganina, kamar yadda aka fad’a mini.”

Kuka Anwarah take yi, haka shima Faisal d’in. Don haka da Anwarah ta ji irin kalaman Faisal ke fad’i, sai tsoro ya kamata. Hak’ik’a ta na son Faisal, kuma ta na iya sadaukar mishi da komai nata, sai dai tana tsoron iyayenta idan suka ji, amma tunda haka ne ta aminta da zancenshi tunda shine zai aureta, tasan babu wata matsala, amma kuma dole ta je ta sanar da momy inda zasu je, domin gudun kada a ga laifinta.

Allah sarki! K’urciya wata abu ce mai cike da wawta. A ganin Anwarah momy zata yarda tunda ta san shi zai aureta.

“To na aminta zan bika mu tafi, amma zan shiga in sanar da momy, na san tana son abinda nike so, idan taji yadda mukayi da kai, zata yarda na bika, ka ga ko da na dawo, zata iya jinyata, ba sai kowa ya sani ba.”

‘‘ku ji k'urciya don Allah’’ faisal ya fad'a a cikin zuciyarshi, kuma ai ba zai bari ta tafi ba, domin ai su ba jahilai bane, itama don tana yarinya ne, ya biyo mata ta bayan gida.

Har Anwarah zata fita motar, sai Faisal ya jawota jikinshi da sauri, wani irin gurnani yake yi kamar wani kare. Anwarah tsoro ya kamata, ta fara k’ok’arin k’wace kanta gareshi tana cewa,

“Ka bari muje cen gidan naka, anan a hanya ne, kuma dare ya fara yi, bari na fad’ama momy sai na dawo.”

Ina ai Faisal ya kame hannuwan Anwarah duka biyun ya rik’e, sannan ya yi nasarar cirema Anwarah hijab d’inta baki d’aya. K’ok’arin k’watar kanta take yi, amma abun ya faskara ta kasa wallahi, bakinshi yakai a cikin bakinta ya datse yana wasa da harshenta, babu yadda Anwarah ba tayi ba, amma ta kasa. Kasancewar rigar barci ce jikinta, ba bu komai sai brezeer da ke jikinta, hakan yasa Faisal kai hannunshi don cire brezeer d’in ya kasa, don haka sai yakai hannunshi duka ya chakumota. Ajiyar zuciyar da Anwarah tayi, ya saka Faisal cewa, ya sakata a wani yanayi, don haka sai ya tashi motar ya tafi.

Kashh…..! Ashe tunda Anwarah ta fito gida, Anwar ya hango hasken fitilar waya da kuma jin motsin get, ya lek’o yaga ko wacece ta fita? Hijab kawai ya gani, amma baiga fuska ba, kawai sai ya fito daga part d’inshi yaga ko wacece ta fito a daren nan? Tambayar mai gadi yayi, wacece ta fita? Mai gadi yace bai san ko wacece ba, don baya kusa.
Anwar ya bud’e get ya fito, hango hasken wayayi, wanda hasken ya hasko mishi fuskar Anwarah a gaban mota, tana rik’e da wanda take ik’irarin mijinta ne na aure. Anwar bai matsa ba, kuma bai koma gida ba, sai ya tsaya daga nesa yana kallon ikon Allah. Ganin an kashe fitilar wayar ne, sai ya tsaya ya gani, kamar minti biyu kuma, sai ya hango hasken fitilar wayar a kunne, sai ya ga irin rik’on da Faisal yayi ma Anwarah, wanda yake shirin kai bakinshi a bakinta, sai Anwar ya haska Fitilar wayarshi da cewa,
“Suwaye anan?”

Sai aka ja motar aka tafi da sauri. Anwar gida ya koma, amma kuma ya kasa barci, ya rasa me yasa hakan? Sai a yanzu yake tuno video da Hashim abokinshi ya tura mishi a lokacin yana India, inda yake fad’a mishi cewa, “ji rayuwar da k’anwarka Anwarah ke ciki, a seven O seven restaurant.” Tabbas! Pic d’in gayen cen ne da aka ce Anwarah zata aura, in bai mance ba, ai ya ganshi sau d’aya bayan dawowarshi, kuma tabbas! Ko yanzu shi ya d’auketa.

Har Anwar zai fita ya sanar da mahaifinshi, don yasan ko wacece Anwarah, wallahi bata da wani buri, sai na ta ‘bata masu sunan gida da mahaifinsu tunda ita ba mahaifinta bane, menene ruwanta? Sai kuma yaga, bari ya barta yaga iya gudunta da kuma basajarta akan gidan, duk wanda ya rufama wani Asiri, Allah zai rufa nashi, sai dai tunani kawai yake yi iri-iri.

“Tirr…! Da wannan bak’ar rayuwar irin ta Anwarah da mugun mijin da zata aura, bayan sun gama komai a waje, ake tunanin Aure zai yi k’arko a hakan? Allah ya tsareni da aikata mugun aiki irin wancen, saboda rashin hak’uri, saura kad’an auren, amma ba sa jurewa, an saba iskanci.”

Tunani ya hana Anwar sakat, kuma ya kasa zaunawa, daga tsaye sai tsaye, yana jiran ya hango hasken motar dawowarta, ya yi mata wulak’anci son ranshi, amma shiru har 12:am babu motsin mota, bare shigowar Anwarah……………..

page biyu ne shima wannan, shiyasa nike tsallake rana d’aya banyi posting ba. A ci gaba da gashi.

Bee²Ta Masoya
[11/8, 10:40 AM] ®Bëë Bëë Tâ Māsôyä????????: ????????????????????????????????????

___________________
♦BAKI BIYU♦
___________________

® REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS P.M.L????????????

ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ

WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM

IG PML WRITERS

https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035

©®
Khadija bee bee
Khadijabellobuhari@gmail.com@gmail.com

★★★★★★★★★
Page…1⃣0⃣
★★★★

Anwarah bata ankara da inda Faisal ya iso da ita ba, sai da ta bud’e idonta taganta a wani makeken gida. Bud’e gaban motar yayi da d’aukota baki d’aya ya shiga da ita cikin gidan. Wani abun al-ajabi shine, Anwarah bata san cewa Faisal wani abu bane ya shak’a mata a hancinta ba. Hakan ya saka jikin Anwarah mutuwa baki d’aya, don hakan batayi musu ba a lokacin da ya shiga da ita cikin gidan.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button