BAKI BIYU COMPLETE HAUSA MUSICNOVELS

BAKI BIYU COMPLETE HAUSA MUSIC

“Haba…! Sahibata menene abun razana? Kada fa ki jefa mini kanki a damuwa, ba komai bane, face yanayin da na kwana jiya ne, ya sakani a rud’ani, baki d’aya barci ya k’aurace mini, babu abinda nike tunani sai Anwarah na, idona baya ganin fuskar kowa sai Anwarah na, k’arshe ma idan na juya a gefen filona da ke gefe na, sai naga kamar Anwarah ce a gefe, sai na shafa naji ba Hasken ruhina bace. Totally dai wallahi a yamutse na kwana jiya.”

“Hmmmm…!” Anwarah ta ja doguwar ajiyar zuciyar da sai da ta kai kunnen Faisal, sannan ta jawo filon bayanta ta aza kanta tana kallon rufin d’akin, sannan ta ce,

“Wallahi nayi tunanin wani abinne ya same ka, baka ji yadda hankalina ya soma tashi ba, kad’an ya rage na fara kuka, amma tunda tunanin Anwarah ne, ai babu komai. Kasha kuruminka, Anwarah taka ce insha’Allah, ai kuma ka samu Anwarah, daga yanzu ka dinga saka man zuciyarka natsuwa, (no one but you) insha’Allah.”

Wata k’ara Faisal ya saki a cikin wayar, wadda ke nuni da tarkonshi ya kama tsuntsuwa, don haka sai ya k’ara saita muryarshi k’asa-k’asa ya ce,

“Idan dai har haka ne, a yau ina son na ganki Anwarah na, Hakan kawai zai saka zuciyata natsuwa, ina son ki za’ba mana wurin da zamu had’u, sannan ki bamu lokacin had’uwar.”

Murmushi Anwarah tayi, sannan ta juyo da wayar gefen d’ayan kunneta ta ce mishi,

“A nan gida zamu had’u, domin ni a tsarina ban ta’ba had’uwa da ko wane namiji ba a waje, hassalima ban ta’ba fira ba bare har nasan inda ake had’uwa, don haka mu had’u a gidanmu kawai.”

“No no no……! My Anwarah kin san yaune farkon had’uwarmu a yadda da soyayyata da ki ka yi, kuma kin san irin son da nike yi miki, waji bi ne mu fara fahimtar juna, sannan a gidanku su fara sani na, don haka ina son yau kawai, mu had’u a saven O saven restaurant domin anan zan fi nuna miki ai nahin soyayyata a gareki.”

Murmushi Anwarah tayi, sannan ta gyara towel d’in jikinta da cewa,

“Kasan Anwarah akanka ta fara wani shauk’in love, ko nace kai ne kayi zarrah a cikin maza dubu, don haka ba komai na sani a soyayya ba, yadda kace haka za’ayi, insha’Allah zuwa 2:pm zamu had’u, sai dai ka turo mini address na wurin, domin ni ba ko ina ne na sani ba, daga school sai gida, sai gidansu suhaila, bayan nan ban san ko ina ba.”

“Ba matsala, zan turo miki, kuma zamuyi waya kafin time d’in, sai dai ina fatar kinyi break fast….domin ina ji a jikina my Anwarah bata ci komai ba?”

Dariya Anwarah tayi, domin ba zata iya ce mishi a yanzu ta tashi ba, don haka sai ta ce mishi, “A yanzu hakan, ina shirin fita falon ne naga abinda aka shirya mana, sai naci.”

“Yauwa! Ki ci nawa da naki, idan kika k’i ci da yawa, anjima zan tambayi cikina naji gaskiyar zance.”

“Insha’Allah, zanbi umurnin shugaban zuciyata.”

Sukayi sallama tare da murmushi.

Iya matuk’a Anwarah ta fad’a soyayyar Faisal sosai, domin ta kai wani mataki wanda komai ya ce mata, zata yarda dashi. Anwarah naji dad’in fira da Faisal, domin yasan lungu da sak’o na soyayya, ya iya kama zuciyar mace, ga Anwarah da mugun son love kamar ta mutu, hakan kawai ya saka Anwarah cewa, lallai a yanzu take ganin ta samu abokin rayuwa na har abada.

Mik’ewa tayi ta fad’a toilet ta yo wankanta ta fito, babu abinda ke tashi a jikinta sai turaren wanka. Hakan ya sakata shirya jikinta domin period time da take ciki.

Turare ta fesa a ko ina na jikinta, sannan ta jawo doguwar riga da k’aramin mayafinta, ta saka da d’aura mayafin a kanta.

Powder kawai ne a fuskarta, sai lipstick da ta shafa a la66anta, kasancewar a yanzu babu inda zata je sai anjima.

Ringing d’in wayarta ke tashi, wanda a halin yanzu tasan kiran ba zaya wuce na momy ba, don haka ta d’auki wayar a cikin ladabi da cewa,

“Momy ganinan saukowa, dama na d’an tsaya wanka ne, saboda na tashi jikin nawa babu dad’i.”

Murmushi ta sake yi, wanda sai da ta d’an rufe fuskarta, da alama akwai zancen da momy ta fad’a mata, wanda nima ban san ko me momyn ta fad’a mata ba, kawai dai naji ta ce,

“To momy gani nan zuwa.”

Jefar da wayar tayi a gadonta, sannan ta fita d’akin tana murmushi.

Cikin natsuwa Anwarah ta dinga saukowa a benen gidan, inda kafin ta k'arasa saukowa ta hango Momy da Baffa a zaune a dining d'in. Cikin sauri ta k'araso, tare da duk'awa har k'asa ta gaishe da Baffa d'in.

Murmushi ya sakar ma Anwarah, a cikin so da k’auna, irin ta d’a da mahaifi, sannan ta gaishe da momy d’in, itama dai kamar Baffa d’in, sannan Anwarah ta mik’e ta jawo d’ayar kujerar dining d’in ta zauna, da jawo cup da plate domin zuba nata karin.

Momy ta dubi Anwarah da kyau, wanda sai da ta samu kanta itama a yin murmushi da cewa,
“A zahiri Anwarah ta ce bata jin dad’in jikinta, amma a bad’ini Anwarah na cikin farin ciki, to ko me ke saka Anwarah d’inmu farin ciki a sanyin safiyar nan?”

Baffa ya dubi momy ya yi dariya, sannan ya kalli Anwarah da kyau, ya gas-gata zancen momy d’in, wanda hakan ya sakashi kur’ba tea d’in da ke gabanshi kuma ya ajiye cup d’in da cewa,

“Anwarah ko me ke sa ka ki farin ciki haka, wanda har ya kasa ‘boyuwa a fuskarki….? domin nasan Anwarah sosai, kuma na san bata da k’arya a rayuwarta, sai dai akwai fad’a, idan an ta’beta, ya kamata a sanar damu domin muma mu taya Anwarah farin ciki.”

Ba musu Anwarah ta dubi momy da ke gefenta, sannan ta rufe fuska da gefen mayafinta, ta duk’ar da fuskar sannan ta d’ago tana dariya tace,

“Baffa! Allah babu komai, ko da akwai wani abun, to ba’a bakina za’a jishi ba, sai dai a bakin Humairah idan ta dawo school, ni dai a yanzu ba zance komai ba, sai dai nace, ku sakani a addu’ar ku.”

Hakan da ta fad’a, sai ta ja cup d’in tea d’inta ta mik’e da sauri, cikin jin kunya da dariya ta yi sama abinta.

Baffa da momy sun fahimci abinda Anwarah ta fad’a, don haka sai farin ciki ya kama su baki d’aya, babu kamar momy da take burin ganin ranar da Anwarah zata fara fidda gwani a rayuwarta, domin ta cika Alk’awarin da ta dad’e da d’auka a duk lokacin da Allah ya nuna mata irin wannan lokaci.

Baffa kuma addu’a da murna ya ke yi, domin shima da nashi burin a rayuwarshi, wanda yake fatar Allah yasa tunanin ya zamo d’aya da nashi, da yafi kowa farin ciki a rayuwarshi.

Da wannan tunanin suka k’arasa break nasu, Baffa ya mik’e domin zaga yawa sauran part d’in matanshi, domin ganin sun tashi lafiya, duk da nisan da ke tsakanin part da part, amma haka yake zuwa part d’in ko wace mace a gidan.

Momy ta k’walama Asabe kira, domin ta zo ta kwashe kayan da suka k’arasa karin dasu, ta kai su kitchen, sannan itama ta haye sama domin shiga d’akinta, kafin Baffa ya dawo ta rakashi bakin mota don zuwa office, domin wannan Al-adarta ce a ko wace ranar girkinta.

        *1:30pm*

Anwarah ta ci kwalliya wadda take kwalliya, tare da saka kaya wad’anda suke kaya na’azo a gani, domin kuwa less ta saka irin na 30k d’in nan, wanda cikin flowers nashi, aka k’awata shi da duwatsu masu d’aukar ido.

‘Dunkin jikin less d’in, ba wani d’unki bane, domin kwalliyar less d’in kawai ta isa ta hana wani k’arin k’yal-k’yali ya hau a jikinshi,domin za’a bata adon less d’in.

Dirin jikin Anwarah yayi dai-dai da kayan da ta saka, duk da kasancewar Anwarah ba fara bace, kuma ba’a iya kiranta a bak’a ba, sai dai idan ta jera da farare, zata ban-banta da su, haka idan ta jera da bak’ak’e zata ban-banta da su.

Tsarin Anwarah tsari ne na k’ira mai kyau, don haka kayan da ta saka, sai suka kar’bi jikinta. ‘Daura d’an kwalin tayi da kyau, wanda baki d’aya ta rufe gashin kanta, amma kuma d’aurin ya tsaya da kyau. Body spray kawai ta fesa a jikinta, sannan ta jawo mayafinta da takalmanta da jikkarta iri d’aya, ta yafa gyalen a k’afad’arta, sannan ta d’auko hand bag d’inta ta sak’ala a hannunta ta saka takalmanta da duba mirror d’in d’akin da ya ke showing d’in mutun daga sama har k’asa, ta dubi kanta ta k’ara duban kanta, wanda ita kanta ta burge kanta bare kuma wanda zai ganta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button