BAKI BIYU COMPLETE HAUSA MUSIC

Wani d’aki ya bud’e ya shiga da ita, Jefata yayi a gadon shima ya hau kan gadon. K’ok’arin cire mata hijab yake yi, duk da Anwarah babu k’arfi a jikinta amma ba ta barshi ya cire mata hijab ba.
“Meye haka Anwarah? Ko kin manta ni mijin da zaki aura ne, sadaki shine aure, kuma na riga da na biya, lefe da duk wani abu shirme ne, don haka ki barni na samu lafiya a jikinki. Jira na samo miki abinda zaki sha.”
Ya mik’e tsaye kenan, sai yaji ba zai iya fita ko ina ba, bai d’an ta’bi jikinta ba, sai ya k’ara rarrashinta da rik’ota jikinshi baki d’aya.
“Innalillahi wa’inna Ilaihir’raji’un! Allahumma ajirni mina nar.”
Kawai sai k’arfi ya diro ma Anwarah, taji duk wata kasala ta gushe mata. babu wani tsayawa ta tureshi da cewa,
“Wallahi ka sake ni, menene hakan kaima? Wace riba zamu samu a kasancewarmu a yau? Bari kaji in ma baka sani ba. Babu abinda nafi tsoro a rayuwar Aure kamar irin wannan kwanciyar ta aure. Zan iya jureta ne kawai a dakin aure na, ba’a waje ba. Da ka ke cewa, wai ka biya sadaki, sadaki ne aure? Idan har zai iya zama shaidu a zamowar faruwar neman aure; to ba zai zamo shaidu ba a d’aura auren, don haka ka samu lemon tsami kasha, ni ba zan yarda da hakan ba. Ina so kayi hak’uri ka mayar dani gida, tun kafin na ‘bata rayuwar ‘yan uwana da dangi na.”
Mik’ewa Anwarah tayi da jawo wayarta da ke gefe. Faisal ganin ba fa yarda yarinyar nan zata yi ba, da k’arfi ya jawota yana k’ok’arin cinma burinshi. Allah ya sakoma Anwarah k’arfi, wanda duk inda yaso ya danneta a gado, sai tayi k’ok’arin kare kanta. Abun ya faskara, domin Faisal ya samu nasarar cirema Anwarah hijab d’in jikinta, ya kai hannunshi a saman k’irjinta. Kuka Anwarah ta fara, sannan ta samu sa’ar hannunshi ta cije da k’arfi, bata saki hannunba sai da ya saketa sannan ta sake shi, ta jawo hijab nata ta rufe jikinta tana shirin gudu.
Faisal ya mik’e da hannunshi mai rad’ad’i ya jawota da k’arfi yace,
“Ni zaki ciza a hannu….har ki fitar mini da jini a jiki? Wallahi kema sai na wahalar dake a daren nan, domin sai na cinma burina, kamar yadda nayi niyya a farko, don haka ki tsaya muyi abinda ya kawo mu mutafi, domin ba zaki fita ba wallahi, sai na d’an-d’ana rayuwar ni’imar da nike hangowa Allah ya yi miki, don haka ki natsu mu shayar da zuciyoyinmu k’auna.”
“Tirr! Tirr!! da wannan mugunyar rayuwa, dama Faisak ba son gaskiya kake yi mini ba? Ashe dama haka ne burinka akaina? Jiki na kake so ba ni ba? Don Allah kada ka furta mini cewa, da BAKI BIYU Kazo a wurina, ka san ina sonka, kuma nayi maka Alk’awarin baka kaina a daren aurenmu, zaka kasance a cikin farin ciki na har abada idan ka aure ni, don Allah ka da ka fad’a mini cewa, dama da yaudara kazo neman aure na. Faisal kada ka aikata abinda kake nufi a kaina, zaka cutatar dani a rayuwa, tunda nike ban ta’ba sa’bama iyaye na ba, akan ka zasu iya yin fushi dani.”
“Matsalarki ce kuma, ni dai buk’atata nike son aiwatarwa a yanzu, ki tsaya mu k’arasa ki tafi.
Ringing d’in wayarshi ke tashi, wayar ya jawo ya duba, anan yaga number mahaifiyarshi ce, sannan ya duba agogo, yaga 12:00am, to ko lafiya? Amma bari yaji.
Dauka yayi da saurarawa yace, ” lafiya kuwa inna?”
“Ina lafiya take anan? Matarka ke nak’uda, tun jiya har yanzu babu wata waraka, kuma anata neman number d’inka ba’a samu ba, don haka duk inda kake gobe ka dawo gida.”
“To inna a kaita Asibiti, akwai abinda ya tsayar dani, da na samu zan iso gob……”
“Wallahi ba zaka samu ba, kuma har abada ba zaka samu ba, jikin Anwarah ya girmi yaudararka, banza mara mutunci, hak’ik’a sai yanzu na tabbatar da na had’u da mai BAKI BIYU wallahi, ni da aurenka Har abada.”
Mahaifiyar Faisal ta d’an jiyo maganar mace a gefen Faisal, amma bata k’arasa ji ba, ya katse wayar da jefar da ita gefe, yaga yayi abinda ya kawoshi shi yafi mishi.
Rikici ya kawai suke yi, shi burinshi yakai inda yake so, ita kuma ta hanashi ko cire hijab nata. Amma Faisal sai da yayi k’ok’arin jaye k’afafunta domin ya biya buk’atarshi.
Runtse ido Anwarah tayi da ambaton sunan Allah, domin k’arfi ba d’aya ba. Anwarah ta sadak’ar da cewa, shi ke nan ta rasa martabarta har abada. Hannunta ta aza a table d’in domin ta samu k’arfin tashi, saboda ta hard’e k’afafunta sosai. Jin wani abu a takarda ya tabbatar mata da rezo ce a ciki, hannanta ta saka ta cireta a cikin takardarta, rik’eta a hannunta. Bud’e k’afafunta tayi kamar ta aminta da shi d’in.
Ganin yadda tayi ne ya saka Faisal cewa, “ko ke fa? Ba gashi kin gano gaskiyar ba, zamu shayar da junanmu kafin ranar auren namu, don Allah ki cire hijab d’in to, zamu fi samun gamsuwa.
Anwarah komai bata ce mishi ba, hawayen bak’in ciki kawai ne cike a zuciyarta, domin ita kawai tasan me take ji a zuciyarta, wanda tunda aka haifeta bata ta’ba jin alamunshi ba ko kad’an.
Faisal an yaye jiki ana shirin lalata rayuwar Anwarah, kawai sai Anwarah ta gyara da saka Hannunta ta rik’o aburda yake shirin illata rayuwarta da ita. Har wani farin ciki ya cika zuciyar Faisal, domin yasan zata yi mishi irin abinda yafi buk’ata ne, wasa da wurin, don haka sai ya saki ajiyar zuciya da cewa,
” ko ke fa? Yauwa! Anwarah na, zamuji dad’i sosai.”
Anwarah tun da Allah yayi ta, bata ta’ba ganin jikin d’a namiji a bayyane ba sai yau. Hakan bata ta’ba rik’a jikin d’a namiji ba sai a yau, shima tana son ta tsira da mutuncinta ne.
Rik’on da tayi mata ne, sai ta saita rezor d’in da ke gannunta, tunda daga cen sama ta yankota, sai k’asa ta dire mishi ita da rezor d’in.
Kuwa Faisal ya saki a lokacin da yaji saukar aradu a jikinshi.
Subhanallah! Jini yace in bakai bani wuri, nan take Faisal ya fita hayyacinshi, ya fad’i k’asa da rik’e aburda ita ce rayuwarshi.
Jini Anwarah tagani na fita kamar an yanka rago. Baki d’aya jini ya ‘bata inda yake kwance, da sauri taja wayarta ta fita aguje. Mai gadin gidan na a kwance ya hango fitar mutun kamar a mafarki, da yake wawa ne, sai yayi cikin gidan ba waje ba.
Anwarah gudu kawai take shek’awa a cikin daren. Kasancewar unguwar ta mutane ce, shiyasa take d’an jin motsin mutane. Gudu take yi amma bata san inda take zuwa ba.
Gudu kawai take yi ba a cikin hayyacinta ba, domin a tsakiyar titi take gudun bata sani ba.
Wata mota na kawowa ta yima Anwarah mugun bugu ta fad’i gefe. Mai motar ya fito da gudu, domin shi bai d’auka mutun ce ya buge ba.
Hasken wayar da ya gani a gefen da take, ya ganar dashi cewa d’an adam ce.
“Subhanallah! Me kuma ya fito da wannan yarinya a cikin dare haka? Gashi da ganinta kaga mutunniyar kirki, to wai ina ta fito?”
Ganin babu wata fa’idar tsayawa yana tambayar iska, ya sakashi d’aukarta da wayar ya saka a mota yayi asibiti da ita, sannan ya sanar da iyalanshi cewa, yana hanyar dawowa ya bankad’e wata, yanzu hakan suna asibiti don ganin an ceto rayuwarta.
Da gudu nurses suka rugo da gado, suka kar’bi Anwarah sukayi ciki da ita.
Wanda ya bankad’eta hankalinshi ya tashi, domin idan ta mutu ya bani wallahi, don haka ya damu nurses d’in da su taimaka mishi ta mik’e.
Ringing d’in wayarta ke tashi, nan take mutumen ya d’auka.
“Banza mara mutunci, idan kun k’arasa iskancin ke da wanda kuka fita, to kada ki dawo gidan nan, kiyi gidan danginki, domin ba zai yuyu ki dinga ‘bata ma mahaifinmu suna ba, domin za’a dinga kallon ke d’iyarshi ce, kike yawon bin mazan ba.”