BAKI BIYU COMPLETE HAUSA MUSICNOVELS

BAKI BIYU COMPLETE HAUSA MUSIC

“Subhanallah! Bawan Allah kayi hak’uri, mai wayar gatanan a Asibiti cikin mawuyacin hali, ko tayi rai ko kuma mutuwa, domin mota ta bugeta tana gudu a saman titi.”

Kafurar zuciyar Anwar ta motsa yace, “idan ma kai ne ka d’auketa, to ka sani kada ka dawo da ita a gidan nan, domin wallahi zan shikka maka rashin mutunci, mun gaji da iskancin da take yi, k’ara ta tsaya a gidan ubanta.”

Wanda ya ture Anwarah yaga babu wata ribarshi akan kare yarinyar da bai san menene Asalin abibda ya fito da ita ba, hakan yasa ya kashe wayar da ajiyeta gefe, burinshi kawai ya ga rayuwarta ta dawo.

“Malam wannan ‘yarka ce?”

  "A A malama, ni ne dai na tureta a mota ban san da ita ba."

“To gaskiya tayi mugun firgita sosai, shiyasa ta fita a hayyacinta, domin tayi mugun d’auke wuta, amma banda gogewa da tayi a goshi da hannu da kuma gwiwar k’afa, babu wata matsala da ta samu a turewar da aka yi mata, amma ka kira danginta mana.”

“Malama wayarta code gareshi, sannan ban san ta yadda zan kira ba, amma yanzu ankira na d’aga, sai naji wani yana magana, wadda ban san me yake nufi ba, shiyasa ban tsaya yi mishi bayani ba. Amma bari mu jira muji ko wani zai kira kafin safe.”

“Ok tom ba matsala, Allah yasa a dace.”
“Ameen.” Malam mai mota ya samu guri ya zauna yana gyangyad’i, domin wallahi dama ya gaji, niyyarshi da ya shiga gidanshi yayi barci, sai ga k’addara ta rutsa dashi.
★★★★★

Faisal tunda ya fad’i k’asa ya rik’e wurin da aka yankashi, sai ya fita hayyacinshi baki d’aya. Banda jini babu abinda ke fita jikinshi, gashi zindir haihuwar uwarshi, amma bai san inda yake ba.

Mai gadin gidan ya dinga biyo k’ofofin da suke bud’e, har ya kai d’akin da yake jin jinishin mutun. Ganin jini na malala a k’asa shima ya rud’e, domin ya aza wuyanshi ne aka yanka, har zai tsere kada a kamashi, sai kuma ya tsaya domin yaga akwai sauran numfashi.
Shigowa yayi a cikin d’akin, sannan ya rik’oshi, ganin inda jinin ke fita mai gadi ya rud’e yana cewa,

“Ka mutu wallahi, innalillahi! Ai nan gurin shine halittar ko wane namiji. Shi kenan ka halaka wallahi.”

Shifa mai gadin ganin irin jinin ya d’auka ko aburce aka k’ire mishi baki d’aya, bai d’auka yanka ba sai da ya duba yaga musulace akayima mata, ma’ana mugun yankane tun farkonta har k’arshenta. Da gudu ya fita yana neman agajin al-ummar da ke gidajen da ke gefen gidan.

Wani dattijo shi kad’ai ya fito domin ganin meke faruwa, mai gadi a rud’e ya nunama dattijon k’ofar gidan shiga.

Shima dattijon yaji tsoro da ganin irin halin da Faisal ke ciki, don haka ya d’aga waya ya kira yaronshi yace, yazo su tafi Asibiti. Suka samu rigar da suka gani a gefen gadonshi suka saka mishi ita kad’ai, sannan suka samu wani farin mayafi a gefen gadon suka nad’e mishi k’ugunshi, domin jinin da ke zuba a jikinshi.

Dattijon da mai gadin gidan, suka tallabeshi zuwa motarshi da suka ga makullinta a aljihun rigarshi, sannan yaron dattijon ya ja motar suka je dashi, asibitin da ta fi kusa dasu.

Likitoci suka k’i kar’bar Faisal, har sai anzo da police, domin case ne babba, mutanen da ke gurin suka had’asu da Allah ganin yadda jini ke zuba, sannan suka yadda suka kar’beshi.

“Subhanallah!” Abinda d’aya daga cikin likitocin ya fad’a, domin ganin irin illar da ke jikin Faisal. Yankane a jikin abar tashi, tun daga sama har k’asa, wanda aka yanka kamar anyi fid’a. Sai da suka yi mishi Allurar kashe zafi, sannan suka samu nasarar yi mishi d’inki ciki da waje, domin yankan ba na wasa bane.

Bayan likitocin sun k’arasa aikinsu akan Faisal, sai suka fito domin jin wanda yayi mishi illah haka. Maigadin ya shaida musu abinda ya sani, shi baiga fuskar ko waye ba, amma tabbas yaga inuwar mutun ya fita da gudu, wanda yake tunanin mace ce.

Likitan ya k’ara tambayarshi da cewa,

“Yanada mata?”

“A gaskiya zan iya ce maka ban san yanada mata anan ba. Domin a gaskiya gidan da nike gadi, to gida ne na gwamnati, kuma a yanzu shine mutun na ukku da ya kama haya yake zaune a ciki, kuma a gaskiya ina yawan ganinshi da ‘yan mata, kunga ba lallai na’iya shaida cewa daga cikinsu akwai matarshi ba, domin itama wannan a yau ya shigo da ita.”

“Subhanallah!” Abinda baba dattijo ya fad’a kenan. Sannan likitan shima yace,

“A gaskiya yana cikin matsala, domin anyi mishi yankan da ya kawo mishi illah ga jikinshi, domin lakkar da ke saka wata sha’awa daga jikin d’a namiji ta wurin, ta samu tsiyayewa, don haka jijiyar wurin ta samu rauni, kamata yayyi a samo wadda tayi mishi hakan.”

Mai gadi ya yi murmushi yace,
“A gaskiya bana jin za’a iya yima yarinyar komai, domin na zo wucewa ta bayan d’akin naji irin gamashi da Allah da take yi, akan kada ya zubar mata da mutuncinta bata saba yin hakan ba. Amma wallahi yak’i aminta. A k’arshe ma, ina tunanin yarinyar da zai aura ce, ya yaudaro domin cinma burinshi. Ranka yadad’e, wannan yarinyar ba ita ce ta farko ba, kuma ba ita ce ta biyu ba a cikin wad’anda ya yaudara, wannan ce kawai Allah ya bama sa’a ta yi mishi hakan domin ta tsira.”

Dukkansu da suka ji hakan, sai suka yi mishi addu’ar samun lafiya sukayi gaba, amma banda mai gadin gidan, domin idan ya tafi bai san ta yadda zai kwashe ba, anan ya kwana.

 ★★★★★

Asubar farko momy ta fito domin ta tashe da yaranta suyi sallah. Ranar ita ce da mai gida, don haka a part d’inshi ta taka sama domin ta tashesu.

‘Dakin Humairah a rufe yake tana barci, k’wank’wasawar momyn ya sakata tashi ta fad’a toilet yin arwallah.
Momy d’akin Anwarah ta fara k’wank’wasawa, inda tura k’ofar d’aya da zatayi, sai taga k’ofar ta bud’e.

Abun ya bata mamaki, tunda ta san cewa, Anwarah bata bud’e k’ofa, sai safiya idan zata sauko karin safe, amma k’ofarta yau a bud’e. Kamar ta wuce, kuma sai taga ya kamata ta shiga d’akin.

Ganin gadon Anwarah gyare lafiya k’lau, ya tabbatarwa da momy cewa, Anwarah bata kwanta gadon ba, kuma ga kayanta da ta cire ta saka na barci.

Duba toilet nata tayi, shiru babu motsin komai, banda ruwan da ke zuba a bahon wankanta.

Momy ta fito da sauri ta k’wank’wasa d’akin humairah, da sauri humaira ta bud’e da cewa,

“Momy na tashi fa, arwalla nike yi.”

“Humairah, Anwarah a d’akinki ta kwana ne?”

“A A momy tana d’akinta, domin munkai 10:pm muna fira da ita, sannan na dawo d’aki na kwanta.”

“Anwarah bata a d’akin to.”

Gaban humairah ya fad’i, cikin tsoro tace,
“Momy to a ina taje ne?”

“Humairah shine nima nike tambaya, amma bari nayi sallah sai naji ko part d’in mama taje, ko kuma part d’in hajiya. Je kiyi sallah kawai.”

Humairah tayi sallah, amma hankalinta na gurin ‘yar uwarta, bayan ta k’arasa, ta riga momy fita domin zuwa part d’in guda biyu.

Suma duka sun sha mamakin ganin humairah da sanyin asubar nan, basu ankare ba, ta fara tambayar yayar tata.

Kowa cikinsu ya kar’ba mata da cewa, Anwarah bata shigo ba.

Humairah kuka ya su’buce mata. Bata wahalar da kanta ba ga shiga part d’inda ta san bata zuwa ba, part din Aunty zuwairah, don haka ta kamo hanyar part dinsu da kuka.

Karo taci da Anwar ya dawo masallaci, gaisheshi tayi sannan ta wuce. Yana ganinta tana kuka yace,

“Wahalalla! Ke kina kukan rashin ganinta, ita kuma tana cen tana holewarta da wani k’ato hankalinta kwance. Tunda ‘yar iska ce, ai zata yi abinda yafi hakan ma, wai meyasa ma nike mayar da hankalina ga wata banza ne? Tun jiya mamakinta ya hanani sakat, sai ganinsu nike yi a idanu na, k’ara ma na daina kula lamarinsu, ko ta dawo kada ma nazo inda zan ganta, domin zan iya furta abinda baffa zai tsaneni.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button