BAKI BIYU COMPLETE HAUSA MUSICNOVELS

BAKI BIYU COMPLETE HAUSA MUSIC

Ya wuce abinshi, da casbaha a hannunshi, yayi part nashi.

Momy na jin kukan humairah, ta san cewa, Anwarah bata part nasu, itama sai taji nata kukan yazo, da tambayar kanta inda Anwarah ta tafi a cikin daren jiya.

Ganin ba ta da yadda zata yi, sai ta je ta sanar da Baffa abinda ke faruwa. Baffa jikinshi na rawa ya fito waje da tambayar mai gadi abinda ke faruwa? Mai gadi ya sanar dashi cewa, shi baiga fitar kowa a cikin gidan ba, kuma baiga fitar kowa ba, sai Anwar da ya fita ya dawo.

Baffa ya dawo ciki, da kiran Anwar d’in ko ya san wani abu? Anwar ya ce, shi baisan komai ba, amma ai su kira wayarta suji.

Baki d’aya sun rud’e, shiyasa suka manta da neman layin nata. Momy ta kira jiki na rawa, wayar na ringing ba’a d’aga ba, momy kuma sake kira take yi.

Anwar na gefe yana kallonsu yana mere baki, domin yayi al-k’awarin ba zai furta komai ba, sai dai ita ta fad’i abinda ta aikata da bakinta.

Baffa ya kira layin da kanshi, anan ne mutumen da ya kawo Anwarah Asibiti, ya mik’ama wata nurse wayar ta Anwarah, domin yaga an saka “BELOVE DAD.”

Nurse d’in ta kar’ba da yin sallama.
Momy na ji ta matso kusa da share k’wallar idonta ta saurara.

“Don Allah ina mai wayar take ne?”

“Gata nan asibitin ISHARA HOSPITAL, wadda ke nan Garki Abuja. Dama tun jiya muke son mu kira ku, amma wayar nada code ne, kuma mai wayar bata san inda kanta yake ba, amma zaku iya zuwa yanzu, domin ta samu accident ne, kuma wanda ya kad’eta yana gurin.”

Baffa bai tsaya cewa komai ba, ya juya part nashi zuwa d’auko makullin mota, haka momy ta mik’ama Humairah Imam ta ce, ta kaishi wurin mama, itama ta bi bayan baffa.

Basu wani dad’e ba, suka shiga Asibitin, baki d’aya ma’aikatan Asibitin momy ta sansu, don haka bata sha wiyar gano inda Anwarah take ba.

Baffa ya tsaya gaisawa da wani wanda ya sanshi sosai, sai dai baffa d’in yana gaba dashi ta wurin komai.

Baffa ke tambayarshi, ko lafiya ya zo asibiti? Ya ke shaida mishi cewa, ai wata yarinya ya kad’e a hanyarshi ta dawowa gida.

Baffa shima ya ke fad’a mishi cewa, ai shi kuma yarinyarshi ce aka sanar dashi cewa tana asibitin, shi yasa ya shigo yanzun. Suka gaisa sosai, sannan suka kama hanyar inda patient d’in tasu take.
Anan suka gano cewa, mutun d’aya ce dai, abun ya sama.

Alhaji buba ya sanar da baffa duk yadda abun ya faru, anan iyayen suka sha mamaki, domin a d’aki suka barta.

Momy ganin Anwarah kwance, sai kukan mutuwar yayarta ya dawo mata, da tuno al-k’awarin kariya da suka d’auka zasu bata, gashi yau har hakan ta faru da ita. To Amma me ya fitar da Anwarah daga gida cikin dare?

Wannan tambayar ita tafi d’aurema kowa kai, domin Anwarah bata ta’ba aikata wani mugun aiki ba, bare ko suyi tunanen cewa, ita ta fita don kanta, har hakan ta faru da ita.

Baffa ya ce da Alhaji buba, yaje gida tunda gasu sunzo, kuma ai an sanar dasu cewa, bata da matsalar komai a dalilin bugewar motar, sai dai firgita da kuma abinda ta gani ya tsorata ta, shine ya sakata fita hayyacinta.

Alhaji buba yayi godiya, sannan ya ciro kud’i domin yi mata magani, Baffa ya nuna mishi cewa, basa buk’atar komai, Allah dai ya tsare gaba.

Hankalinsu ya kwanta da jin inda Anwarah take, sai dai yau kwana biyu bata farka ba.

Duk wani masoyin Anwarah yana gurin, kowa jiran farkawarta yake yi domin suji dalilin fitarta, da kuma abinda ya firgitata, amma shiru har yanzu, kuma likitocin sunce babu wata matsala zata farka.

Suhailah k’awar Anwarah ko yaushe tana Asibiti, burinta taga farkawar aminiyyarta.

Kowa ya zo ganin Anwarah, harda munafukan gidansu, amma banda Anwar, wanda ya tsiri tafiyar k’arya domin kada ya zo asibitinma.

Abun tambaya ga kowa na gidansu shine, Shin ina Faisal yake? Domin shine mijin da zata aura, ai ya kamata ace ya san da halin da take ciki. Kuma sai sukayi tunanin cewa, zai iya yuyuwa bai san halin da take ciki ba. Amma bari a nemoshi inji momy kenan.

“Humairah ki duba wayar Anwarah, sai ki kira Faisal ki sanar dashi halin da Anwarah ke ciki.”

“Tom momy.” Inji Humaira kenan.

Humairah ta kira layin nashi, amma a kashe yake. Yinin ranar number d’inshi kawai take kira, bata samu ba, kuma Anwarah bata farka ba har yanzh.

Momy tace ta k’yaleshi, ai idan bai jita ba, zai kira layin nata……….

kuyi hak’uri, 2days kunji shiru ko? Na d’anyi gyaran wani abin ne, amma kuma komai normal yanzu.

Bee²Ta Masoya
[11/11, 12:27 PM] ®Bëë Bëë Tâ Māsôyä????????: ????????????????????????????????????

___________________
♦BAKI BIYU♦
___________________

® REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS P.M.L????????????

ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ

WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM

IG PML WRITERS

https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035

©®
Khadija bee bee
Khadijabellobuhari@gmail.com@gmail.com

★★★★★★★★★
Page…1⃣1⃣
★★★★

Momy ta hango hannun Anwarah na motsi. Cikin sauri ta mik’e tsaye da matsawa a gadon da Anwarah take kwance ta kira sunanta har sau ukku.

Anwarah jin muryar momy ya sakata k’ok’arin bud’e idonta, amma kuma sai taji sunyi mata nauyi sosai, saboda kunburin da fuskar tayi. Bud’e idon tayi ahankali, sai dai banda dushi-dushi babu abinda take gani, amma tana ganin mutane ba sosai ba.

Momy na ganin Anwarah ta bud’e idonta, sai tayi dariya ta rik’o d’ayan hannunta da cewa,
“Alhmdllh! Allah na gode maka, Anwarah bud’e idonki ki ganni momynki ce.”

Mutanen da ke tsaye a cikin d’akin, suma suka matso gefen gadon suka tsaya. Anwarah fa na ganinsu, sai dai ba zata iya shaida suwaye ba, ko momy ma muryarta ta gane. Amma su a rufe suke ganin idon nata.

K’walla suka hango suna fitowa a idanunta, wanda nan take momy ta yi saurin goge mata, amma kuma wasu bayan wasu haka suke fitowa.

Ganin kukan ba mai tsayawa bane, sai maman Anwar ta matso da rik’a Anwarah d’in ta tashi. Ta aza mata filo a bayanta ta zauna.

“Anwarah sannu kinji. Zaki sha ruwa?”

Anwarah murya kawai take ji, amma bata ganin fuska, sai dai tana gane muryar kowa. Ruwa momy ta kawo da wata roba, aka sakama Anwarah MacLean a brush aka mik’a mata ta fara wanke bakinta, sannan mama ta had’amata tea ta bata. Babu laifi Anwarah tasha tea d’in sosai, domin kwana biyu a kwance ba wasa ba.

Ita kanta taji k’arfin jikinta, sai dai babu abinda Anwarah ke yi sai kuka, da anyi mata magana, babu wata amsa da zata iya maidawa sai kuka, kuma kuka mai tsanani.

Momy ta firgita da wannan al-amari na Anwarah, tunda ta farka babu kalma d’aya da ta fito bakinta face kuka, sannan duk wata dubara da za’a yi don tayi magana, anyi amma shiru sai kuka.

Da baffa yazo shima yayi iya k’ok’arinshi, amma Anwarah banda kuka babu abinda take yi.

Ganin Anwarah ba ta da matsalar komai a jikinta, sai likitocin suka sallameta, tare da bata magungunan k’arin k’arfi, da kuma warwarewar sauran jimuwar da ta samu a goshinta.

Bayan Anwarah ta dawo gida ne, sai momy ta had’a mata ruwan zafi tayi wanka, sannan aka bata abinci taci, amma Anwarah ta ka sa cin komai, sai kuka take yi, da tuno abinda ya faru da ita, wanda ta d’auki al-k’awarin ba zata fad’ama kowa ba.

Momy ta damu sosai, wanda sai da takai tana yima Anwarah fad’a akan kukan da take yi. Baffa yace ta k’yaleta, yanzu hakan ita kawai tasan me ke damunta. Momy ta share lamarin Anwarah, iyakarta tayi mata hidimar da ya dace da ita.

Damuwa ta shiga jikin Anwarah sosai, wanda yakai ko magana bata iyawa, tun ranar da abin ya faru. Momy tayi tunanin iskanci ne ya saka Anwarah yin shiru, amma kuma ba haka abun yake ba, domin abun ya kasance, idan tana zaune ita kad’ai, sai ta rufe idanunta tana kuka, kamar taga wani abu, sannan sai ta rufe kunnenta, kamar Ana fad’a mata wani abun. Al-amari ya kasancema Anwarah kamar mai aljannu. Tayi bak’i duk ta rame, abun ya damu baffa shi kanshi, domin yasan akwai dalilin yin hakan.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button