BAKI BIYU COMPLETE HAUSA MUSICNOVELS

BAKI BIYU COMPLETE HAUSA MUSIC

“Shin wai Aisha Yaron nan da zai auri Anwarah kuwa yazo tunda abun nan ya faru ko kuma ya yo waya?”

Baffa ya fad’a bayan ya fito daga d’akin Anwarah d’in suna magana da momy a falon sama. Momy ta amsa mishi da cewa,

“Wallahi wayarta na hannuna tun a ranar da aka ganta, amma har yanzu bai kira ba, kuma na saka Humaira ta kirashi, wayar na ringing ba’a d’aga ba.”

“Okey! To babu komai, zan nemi iyayenshi naji ko lafiya yake?”

“Gaskiya da hakan yafi, domin ita har yanzu ta kasa cewa komai, kuma ni wallahi Abban Anwar, kamar ganin nike yi, yarinyar nan Aljannu ne suka d’auketa suka dawo da ita, domin wallahi na rasa kanta, daga rufe kunnuwa, sai rufe idanuwa, shi kad’ai take yi.”

“Insha’Allah babu komai Aisha, zan kira malam Anjima ya duba mana ita.”

“To Allah ya kiyaye hanya, sai ka dawo.”
Baffa ya fito da tunani iri-iri a zuciyarshi. Anan yaci karo da Anwar da ya dawo a tafiya. Har zai shiga mota da driver ya tayar, sai kuma ya tsaya, don hango motar Anwar da ke shigowa, sai ya tsaya. Anwar nayi parking d’in motarshi, da sauri ya fito ya zo gurin mahaifin nashi da duk’awa ya gaisheshi.

“Anwar kuma sai na samu labarin kayi tafiya a wurin hajiya, Ina fatar ka dawo lafiya?”

"Eh baffa, wallahi tafiyar ce ta zo mini a gaggawa, domin ko Mama ban sanar ba, saboda naga duk kuna asibiti ne, shiyasa na fad'a ma hajiya cewar zanyi tafiya ta kwana biyu, ko Anisah ma sai da naje na samu chance nike fad'a mata."

“Okey! Babu komai, Amma kuma ka san anga k’anwarka ko?”

Anwar yaji baffa kamar ya dakar mishi zuciya, wai k’anwarshi. Shi wallahi ya tsani ana had’a jininshi da jinin ‘yar iska, wadda yaga iskancinta a zahiri ba a’boye ba, ya ga na farko, kuma yaga na biyu da idonshi, har a had’ashi da ita? Shi wallahi ya tsani ganinta ma, shiyasa ya tafi kaduna abinshi ya huta. Kuma yayi al-k’awarin ba zai fad’ama kowa abinda ya gani ba, sai sun ga halinta da kansu, sannan zai yi magana…….

“Anwar tunanin me kake yi ne muna magana?” Baffa ya katse tunanin Anwar, hakan ya dawo da hankalin Anwar yayi murmushi.

“Wallahi baffa ina tunanin kayan da mukayi da wani ne, shin ko ya turo mini ne, ko ko cewa yayi sai gobe, shiyasa na d’anyi shiru. Ashe an samu ganinta? To Allah ya tsare gaba, zan shiga ciki baffa.”

Mamaki ya kama baffa, murmushi kawai yayi ya shiga mota driver ya tayar suka tafi.

Anwar kuma ya kama hanyar part d’inshi. Jin an rik’o hannunshi ne ya sakashi saurin juyowa, Ido hud’u sukayi da Anisar shi. Wani sanyi ya dira a zuciyarshi wanda ya kasa ko wane iri ne.

“Mijina! Ka tafi ka barni da kewarka, wallahi na damu sosai, kuma ni duk wayar da zamuyi, idan ba ganinka nayi ba, bana jin na natsu.”

Anwar yaji dad’i, wanda ya saki murmushin da sai da fararen hak’oranshi suka bayyana, sannan ya gyara tsayinshi dai-dai da jingina bayanshi a jikin bangon k’ofar shiga part nashi ya kalli Anisah yayi dubarar k’wace hannunshi daga gareta, domin ya ji wani sauyi a jikinshi lokacin da yake kallon idanunta yace mata,

“Ni na isa na share rabin raina? Yanzu hakan saboda ke na dawo gidan nan wallahi, domin ba zan iya shafe 1 week banganki ba.”

“Allah mijina.”

“Sosai mata ta.”

Farin ciki ya saka Anisah k’ara matsowa jikin Anwar, ai nan take Anwar ya dakatar da ita da hannunshi, domin shima yana cikin matsala sosai, shi kad’ai ya san me yake ji idan Anisah na matsowa jikinshi, domin jin yake yi tsikar jikinshi na tashi.

Anisah bata sanya mayafi babba wanda zai iya rufe mata jikinta baki d’aya, sannan kuma Anisah na saka k’ananan kaya ko yaushe a jikinta, wanda dole ne in kana cikakken namiji mai lafiya ka dinga shiga wani yanayi idan kana tare da ita, amma ita ko a jikinta, rayuwar turai take yi, bayan ko abujar bata ta’ba tsallakawaba.

“My Anisah! Kin ga yanzun nan at shigowata, kuma ina son na shiga part d’in mama, idan na fito zan kiraki mu had’u a bayan lambu, sai muyi magana ko?”

Anisah ta Amsa kawai ne, amma ita fa ba haka ta so ba, ta so su d’an dad’e da juna, domin akwai wani had’in turare da ta shafo a jikinta, kuma Anso ya had’u da jikinta, sai dai shi kuma yana jin tsoron hakan domin komai zai iya faruwa dashi, domin tsananin sha’awar da Allah yayi mishi. Kuma ya san ita zai aura, to idan yana dinga matse mata a jiki, idan sunyi aure ba wani dogon feeling zai ji ba a gareta domin sun saba hakan a waje, shiyasa yake gujema Had’uwar jikinsu guri d’aya.

      ★★★★★

Wata biyu da faruwar Abinda Faisal ya yiwa Anwarah, amma har yanzu Anwarah bata magana, Abu ya zamar mata kamar wata kurma, kuma tanaji amma maganar ce ke wuyar fita bakinta.

Su momy sun kai Anwarah Asibiti, amma Ance musu lafiyarta k’lau, sai dai Akwai abinda ya firgita rayuwarta sosai.

Baffa ya ce a k’yaleta, duk ranar da ta so yin zance ai zai fito, sai dai damuwarsu ita ce, har yanzu faisal bai kira ba, kuma bai aiko da kayan Auren da ya ce ba, gashi lokaci ya shige, saboda rana d’aya baffa ya so ya had’a auren Anwar d’in da Anisa, ita kuma Anwarah da Faisal, amma kuma har yanzu shiru.

Idan aka kira wayar Faisal bata shiga, idan aka kira wayar iyayen k’aryar Faisal ba ta zuwa kwata-kwata.
Baffa ya tura aje a kaduna a tambaya mishi labarin Faisal a company da yace na mahaifinshi ne, da kuma mutanen da yace mahaifanshi ne, sai dai baki d’aya wurin basu san ma waye hakan ba.

Baffa ya shiga rud’ani na gaske, sai dai bai sanar da kowa ba, amma kuma yana ci gaba da bincike.

Anwar duk hanyar da zata sadashi da Anwarah baya so, domin zai iya fad’a mata abinda bai yi niyyar fad’a ba idan ya ganta, don haka k’ara ya tsaya inda Allah ya ajiyeshi yafi mishi sauk’i.

A haka akayi ta tafiya, Amma Anwarah bata iya cewa komai, sai dai kowa tana kallobshi ne da ido, idan taji zancen kalma mai kama da ta faisal, sai dai ta dinga hawaye.
Baffa ya riga da ya gano cewa, matsalar Anwarah ta na nasaba da zancen Faisal, kuma idan ma saceta aka tashi yi, to may b shi yanada Hannu a ciki, sai dai kawai yayi shiru, domin zargi ne kawai yake kawowa a zuciyarshi.

Shirye-shiryen Auren Anwar ake yi da Anisah, wanda komai da komai Anshirya, har gidan da zasu zauna baffa ya bashi, duk wata rayuwar burgewa, ta taru a gidan Anwar, yanzu rana kawai ake jira ta d’aura aure.

Ango da Amarya shirye-shirye kawai ake yi, babu laifi kowa ya naji da bukin nan, domin dangin maman Anwar dukansu sun zo garin Abuja, hakan dangin baffa na gefen hajiya, suma duk sun xo.

Amarya Anisah da Auntynta babu zama tun ana sauran sati ukku biki, suke yawon gidan manyan bokaye, domin ganin anyima Anisah duk wata mallaka a jikinta, wadda ko motsi Anwar zai yi, sai da izinin Anisah d’in.

Rubutu a jikinta, Rubutu a jikin miyagun bokayen malamansu, wanda suke yi a jikin al-aurarsu su wanke su bata tasha, ko kuma suyi rubutun, suce sai an shiga daga ciki za’a samu waraka. Anisah komai bata ji, domin ba yanzu aka fara hakan ba, da hakan ta k’are makaranta ba tare da ta wahala ba.

Anwar duk wani aboki nashi, na waje da gida Nigeria ya gayyato, ‘barin kud’i ba’a cewa komai, domin akwaisu ajiye an tara domin wannan rana.

Gida ya cika sai hidima ake yi, Gari ya d’auka Anwar baffa zai yi aure, kowa da kowa jiran ranar yake yi.

 Suhailah ta damu da Halin da Anwarah take ciki sosai, amma Anwarah tak'i ta fad'a mata meke faruwa, sai dai idan tayi mata maga, ta kar'bi wayarta ta rubuta mata "Faisal." Amma bata k'arasawa sai dai ta fashe mata da kuka. Suhaila ta shiga damuwa, kuma itama tasan cewa, lallai akwai mugun abinda faisal ya aikatama Anwarah, domin in ba haka ba, me zai sa har yanzu bai aiko ba, kuma bai zo ba? Suhailah na yawan nanata wannan zancen a zuciyarta na cewa,
"Anwarah baki ta'ba yadda ba, da cewa, fuskar Faisal tayi kama da ta masu *BAKI BIYU* ba, amma a yanzu ai k'ila ki yarda, idan dai har shi yayi miki wata illar a zuciya."

Ana gobe za’a je gurin partyn auren su Anisah, kowa da kowa yana shirin kayan da za’a saka, ita kuma Anwarah tana d’aki kwance abinta, banda kuka babu abinda take yi.

Sallamar Suhailah taji, wanda ya sakata saurin share hawayenta.
“Anwarah kowa yana falo, amma ke kuma gaki nan kwance kamar mara gata, to ki taso ki zo muje, a yau zaki tabbatar da cewa, ni mai k’aunarki ce Anwarah.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button