BAKI BIYU COMPLETE HAUSA MUSICNOVELS

BAKI BIYU COMPLETE HAUSA MUSIC

Kallo kawai Anwarah tabi Suhailah da shi, domin bata san me take nufi ba. Kamar kada ta tashi, kuma sai suhaila ta rik’ota da jawo mata d’ankwalin rigar jikinta ta d’aura mata, ta rik’ota suka fito falo.

Da ido Anwarah tabi kowa, inda tagane cewa, meeting kuma aka sake had’awa kenan. Babu ko shakka k’ila baffa ya gano waye faisal kenan? Anwarah bata k’arasa tantance kowa ba, sai taga wasu mutunane su ukku a gefe, wad’anda biyu daga ciki zata iya tuno su a wani wuri, sai dai ta manta ko a ina ta sansu.

Baffa yace ma Suhaila, su samu guri su zauna.
Tunda matsalar nan ta faru, kowa yayi ma Anwarah sannu, Amma banda Anwar, domin ko Anisa tayi mata sannu na munafucci, amma shi sai yau ma Anwarah ta ganeshi a falon nan na baffa, gashi yanzu kusan wata ukku kenan da faruwar abun.

Bayan An natsu, baffa ya fara magana da cewa,

“Dama na kira ku ne baki d’aya, domin kowa yaji abinda ya faru da kunnenshi, domin kada daga baya na dinga jin wata magana na tasowa wadda ban yadda da ita ba. A matakin farko da muka tsaya shine; an jira mijin da Anwarah zata aura, ya turo kayan lefenshi amma kuma muka ji shiru, wanda hakan yasa a ka tsayar da zancen auren nata, za’ayi na ‘yan uwanta. To a binciken da nayi, sai na gano wasu abubuwa dangane da shi Faisal d’in, sai dai na k’i fad’i ne domin banida shaida akan hakan. Kwatsam! Yau sai ga K’awar suhaila ta zo da bak’i akan cewa, suna son su fad’a mini wanene Faisal d’in, wanda mu ba mu sanshi ba. Duba da bana yin abu, sai tare da iyalina, shiyasa na tara kowa da kowa, yaji me suka zo dashi? Kuna iya fad’a muna ko ku suwaye? Kuma ya kuke da Faisal d’in?”

‘Daya daga ciki ta nuna wata mace da ke gefen dama tace,

“Alhaji wannan ita ce wadda Faisal ya tashi aure a garin kaduna, kuma k’awatar mu ce sosai, domin tare mukayi karatu, kuma muka fara aiki tare a ofishin ‘yan passion da ke garin kaduna. A lokacin suka had’i da ita, soyayya mai k’arfi ta shiga tsakaninsu, wanda har ankai ga zancen aure. Ya turo iyayenshi da kuma sadak’in auren. Bayan haka suka zauna a matsayin jiran ranar auren. Anan Faisal yaci galaba akanta har ya samu ya yaudareta, kullum suna tare tamkar mata da miji, har rabon ciki ya shiga tsakaninsu. Tunda Faisal ya gano sumayya nada ciki, sai ya tsallakewarshi ya barta. Anyi nema har an gaji, kuma wad’anda ya turo a matsayin iyayenshi, suma ba’a samesu ba. Lokacin da iyayenta suka gano halin da ta ke ciki, sai suka koreta a gidan nasu, domin mahaifinta shine limamin unguwarsu, to yana jin tsoron abin kunya, shiyasa ya ce ta bar mishi gidanshi. Lokacin ne ta koma gidan mamar mahaifiyarta ta zauna, sai gashi Allah ya kawo k’addarar zubewar cikin, ta ci gaba da aikinta, amma kuma bata ga Faisal ba. Wata rana munje Seven O seven restaurant, sai muka ga Faisal shi da waccen da ke zaune a gefe, sai ya ke ce mana ai yayi aure. Bayan mun koma gida, sai muka sanar da sumayya cewa, Faisal yayi aure, anan ta ce sai ta d’auki fansa, mu gano mata gidan matar da ya aura. Hakan yasa muka dage da gano inda yake, amma bamu samu ba. Wata rana mun ta’ba ganin Suhailah ita da wadda muka yi zaton ita ce matar Faisal d’in, don haka mukayi k’ok’arin ganawa da ita har gidansu, bayan munyi bincike mun gano inda gidan nasu yake, anan muka tambayeta gidan auren k’awarta, take sanar damu ai batayi aure ba, kuma ma yanzu hakan bata da lafiya, shine ta ce mu zo nan.”

Anwarah da momy da Humairah kowa kuka yake yi, amma kowa mamaki ya kamashi, banda Anwar da ke yima Anwarah kallon itama ai ya gama da lalata rayuwar tata, don haka ko a jikinshi, domin ita ma 'yar iskar ce, domin har video aka yo mishi na lokacin da suna restaurant d'in, irin yadda yake wani rungumeta a jikinshi kamar wata matar tashi, kenan da yardarta hakan ta faru, don haka shi ko a jikinshi.

Baffa ya kalli masu kukan baki d’aya, yace da su, “ya kamata ku daina kukan nan, domin bayada wani Amfani, kuyi imani da k’addarar da Allah ya d’auro, kuma mu gode ma Allah da abun ya tsaya anan.”

Tausayin Anwarah ya kama kowa da ke gurin, amma banda mutun ukku, domin ba su damu da ita ba.

Baffa yaci gaba da cewa, “Ni a binciken da na saka akayi mini na Faisal shine; ance yanada Aure, kuma shi d’an Asalin garin Jigawa ne, domin a ma’aikatar da yake aiki, acen naje har nagano inda asalinshi yake. Kuma wanda na tura ya shaida mini cewa, ance Faisal d’in an mayar dashi gidanshi cen jigawa, domin wani rauni da ya samu a jikinshi, ‘yanzu hakan ance baya iya aure, ko yayi kuma babu mai iya zama dashi.”

“Subhanallah!” Abinda hajiya babba ta fad’a kenan, kuma sauran wurin suma suka maimaita yadda ta ce. Anwarah kuma murmushin zuci tayi, domin ta san ita ce sillar nakkasa shi, domin yankan da tayi mishi ba k’aramin yanka bane.

Anwar da Anisah an takurasu, domin sunada shirye-shiryen da suke son gabatarwa, domin lokaci na k’urewa, don haka suka ‘bata fuska, babu kamar Anwar da zuciyar nan tashi ta cika.

Baffa ya rufe taron da cewa, “To Alhmdllah! Tunda haka Allah ya k’addaro, babu yadda zamuyi, wani zancen anyi kaza-anyi kaza, daga nan ya k’are, ku kuma mun gode sosai, shi kuma Allah ya sa hakan shine silar shiryuwarshi, don haka zancen ya k’are anan.”

Anwar ya kalli baffa d’in yace a zuciyarshi,
‘Tab! To wa ma ya damu da ita, da zai bi ta kan zancenta? Ni wallahi an takurani anan domin wallahi na gaji.’

Rufe taron akayi, kowa ya kama gabanshi, bak’in suka tafi, amma Anwarah tak’i daina kuka, suhailah tun tana rarrashinta har ta gaji ta tafi ta barta.

Baffa yayi al-k’awarin share hawayen Anwarah, kamar yadda ya so a farko, kuma insha’Allah k’udurinshi na nan a zuciyarshi babu inda zai je.

Baffa ya saka momy tayi wa Anwarah magana ko a rubuce ne cewa, akwai abinda Faisal ya ta’ba yi mata na dangane da keta haddinta? Domin akwai abinda yake shirin yi.

Babu musu momy tayima Anwarah wannan binciken sosai, kuma Anwarah ta tabbatar mata da babu komai, domin tun daga farko har k’arshen abinda ya faru, sai da Anwarah ta rubutama momy ta bata a takarda, wanda shi momy ta kaima baffa.

Dukansu sun yarda da abinda Anwarah tace, sai dai sun rasa dalilin Anwarah na rashin yin magana, ga shi tana ji, amma bata iya mayarwa, wanda tun suna d’aukar zancen wasa har ya zamo gaske.

Anata hidimar buki, a yau akayi party na soyayya, wanda bukin ba laifi ya had’u, sai dai kowa yaje, banda mama da Anwarah da hajiya, kowa yana part d’inshi zaune.

Bayan an dawo ne baffa ya saka a kirawo mishi Anwar, a lokacin Anwar na cen manne da Anisah ana soyewa a part d’inshi, domin sai yanzu ya yadda da had’a jikinshi da nata, domin gobe ne d’aurin auren, ko nace tsimin boka na aiki a jikinshi, domin wani sonta yake ji yana shiga jikinta sosai, har yake ganin nawar gobe tayi.

Sak’on kiran baffa ya iso kunnen Anwar, wanda bai tsaya ‘bata lokaci ba ya isa d’akin mahaifinshi da sallama, momy da mama suna zaune.

Anwar ya samu guri daga k’asa ya zauna, baffa na tsaye ya juya bayanshi yana kallon wani pic na family nashi lokacin yaran na k’anana, Anwarah na rungume jikinshi, Anwar na gefen momy zaune, Anisah na zaune gefen Aunty.

“Baffa gani.” A lokacin baffa ya juyo yana kallon Anwar yace,

“Ni ne na haifeka?”

“Eh baffa! Na san banida wani uba bayan kai.”

“Ka yadda zaka yi mini biyayya akan duk abinda na umurce ka?”

“Sosai baffa! In dai har bai sa’bama dokokin ubangiji ba, zanyi maka biyayya na kar’beshi.”

“Anwar ko menene ka ya yarda zaka yi mini biyayya a matsayin buk’ata d’aya da na ta’ba nema a gareka?”

“Sosai baffa! Nayi al-k’awarin cika maka burinka.”

Ba Anwar da ake sakoma tambayar ba, hatta iyayen da ke zaune, sai da suka firgita da jin abinda basu saba ji ba daga gareshi, don haka hanjin Anwar suka d’uri ruwa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button