BAKI BIYU COMPLETE HAUSA MUSIC

“Gobe za’a d’aura maka aure da matar da kai kake so, ni kuma zan d’aura maka aure da wadda baka so, wato Anwarah a matsayin matarka ta biy……..”
Ai baffa bai k’arasa zancen ba, momy da Anwar suka mik’e tsaye, amma mama ko kad’an bata matsa ba, har sai dai tayi murmushi da jin zancen.
“Abban Anwar, ka kuwa san me kake shirin aikatawa kuwa? Anwar da Anwarah aure? Kuma bayan ka san yaro ne ba zai iya d’aukar mata biyu ba. A gaskiya ka duba zancen nan ba zai yuyu ba. Yaya kina jin abinda ake shirin yi fa, don Allah ki saka baki.”
“Banda ke Aisha, kin ta’ba jin baki na a duk al-amarin yaron nan? To babu ruwana a ciki, sai dai nayi masu addu’ar zaman lafiya.”
Anwar baisan lokacin da ya fara magana da cewa ba,
“Baffa! Mama!! Anya kuwa kune kuka haife ni? Ko dai ni ne ba d’an gidan nan ba? Don Allah ku fad’amani in fahimci ko ni waye, domin idan kune kuka haifeni ba zaku so mini abinda ni ba shi nike so ba, don Allah baffa, mama ku fad’a mini gaskiya.”
Baffa kallon Anwar yake yi, wanda bai san menene dalilin da ya saka suka yanke wannan hukumcin ba, don haka baffa ya kalli Anwar yace,
“Shi ya tabbatar mini da cewa, har abada ba zaka ta’ba iya cika al-k’awarin da kace zaka iya cika mini buri na ba, don haka ka sani umurni ne nike baka, ba wai neman al-farma ba, gobe za’a d’aura aurenka da Anisah da Anwarah. kuma ka tashi ka tafi, na k’arasa maganar da nike son yi da kai.”
Anwar fita yayi da sauri, wanda momy tayi k’ok’arin rik’eshi don su bama baffa hak’uri akan ya jaye maganar, amma zuciyar Anwar ta rufe ko gani bayayi, sai hawaye da yaji sun cika mishi ido. Da sauri ya nufi part d’in momy ba tare da yatsaya ganin mutanen da ke cikin part d’in ba, da gudu ya haye saman benen da tura k’ofar d’akin Anwarah da k’afa, wanda sai da Humaira ta mik’e tsaye domin tsoron da taji, haka Anwarah ta tsorata sosai, wanda sai da ta saka filo ta danne kanta, bata d’ago ba sai da taji sautin Anwar yana cewa,
“Banza mara mutunci, wallahi ki sani ba zaki ta’ba cin nasara akaina ba. Kin gama iskancinki da wani, har kike tunanin ni zan aure ki. To ki sani wallahi ba zan ta’ba auren ‘yar iska ba. Mafita d’aya ita ce a gareki a yanzu, ki je ki fad’ama baffa cewa, ba ki sona, kuma idan kin fad’amasa, ki kwashi kayanki ki koma gidan ubanki, domin hakan shi zai fi maki sauk’i. Kin mallake ubanmu, sai abinda kike so shi yake yi miki, wallahi sai dai na mutu, amma ba zan iya aurenki ba wallahi.”
Sai da Anwarah taji ya ambaci sunanta sannan ta fahimci da ita yake, shin me yake nufi da kalmar aure? Dama ana aure tsakanin yaya da k’anwa ne? Don haka ta mik’e tsaye da nuna kanta da hannu, domin bata iya magana.
“Eh ke da ke nike, kurmancin naki na k’arya, wallahi ki natsu ki bud’e baki ki sanar dasu cewa, ba kya sona, idan koh har kika yadda aka d’aura aurenmu a gobe, wallahi zaki fi kowa muzanta a rayuwarki, kuma wallahi bani son……..”
Kafin Anwar ya k’arasa furucinshi na k’arshe, har Anwarah ta zube k’asa a somammiya, wadda ko motsi bata k’ara yi ba.
“Da kin mutu ma, wallahi da yafi miki, domin ba zan iya auren macen da wani ya rage ba, ni kuma na zo na k’arasa zama da ita, kamar wani mara gata a duniya.”
Yana fita Humairah ta kwad’a kuwa, tana kiran sunan “yaya Anwarah ki tashi don Allah. Wayyo na shiga ukku!.”
K’arar kukan Humairah ya dawo da mutanen da ke falon, don haka d’akin ya cika da mutane, ana zubama Anwarah Ruwa, kamar ana d’auke mata numfashi, domin wanda bai san mutuwa ba, zai iya kiran Anwarah da matatta……………
4 comments;
0⃣8⃣1⃣0⃣9⃣1⃣8⃣8⃣8⃣8⃣3⃣
Bee²Ta Masoya♥