BAKI BIYU COMPLETE HAUSA MUSICNOVELS

BAKI BIYU COMPLETE HAUSA MUSIC

“Wawww! Anwarah kin zuba kyau, anya zan iya zuwa a hakan? Kada fa na rikita sahibina, wai ko dai na saka hijab d’ina? Amma kuma ai mayafina babba ne, ko ma dai yaya ne, na san hakan ma na yi sosai, Ina ma Humairah na nan, nasan zata iya duba mini inda nayi da kuma inda banyi ba, amma ko yanzu ba laifi, na san nayi a hakan.”

Anwarah ke ta surutunta a d’aki tana dariya, kuma tana tambayar kanta da kuma amsa tambayar da kanta. Jawo wayarta tayi, da duba number d’in babbar Aminiyyarta wato Suhaila tayi, wanda ringing d’aya wayar tayi suhaila ta d’aga a cikin murna da cewa,

“Aminiyyata! Wallahi yanzu nike shirin kiranki wallahi, sai gashi kin kira ni.”

“Eh! Ko ba haka bane, haka ne, domin ba zakiyi mini k’arya ba tawan, dama ina son naji kina gida ne?”

“Hhhh..! Eh ina gida Anwarah, hope zaki shigo ne?”

“Eh! Zan shigo yanzu ba sai anjima ba, kuma tafiyar fa ba taki bace, domin kada kiyi tsammanin zan zo na dad’e gurinki ne?”

“Na dai ji…. Allah yasa saboda yaya Abdul zaki zo, waih…! Da yau na yi farin ciki sosai.”

“Ke dai kika sani, ni dai tawa tafiyar daban ce, don haka ki jira ni.”

“Okey! I’m waiting you babynmu.”

Suka kashe waya, Anwarah ta jawo makullin motarta da ke gefen mayukkan shafawarta, sannan ta jawo k’ofar d’akinta bayan ta fito.

‘Dakin momy ta shiga da sallama, inda ta tarad da momy d’in na sallah, da Alama zaman tahiyar k’arshe ne tayi, don haka sai ta zauna a gefen gadonta. Ba’a dad’e ba, momy ta k’arasa sallah da shafawa, ta dubi Anwarah ta ce,

“Anwarah ina fatar kinyi sallah ko?”

Anwarah ta dubi momy da rufe fuska da mayafi, alamar ta gane cewa, yau bata sallah. Nan take momy ta gano, kuma mantawa tayi da yanayin ciwon da Anwarah d’in tayi jiya na mara, sai dai sabone da ta riga da ta saba na sai tambaya idan lokacin sallah yayi.

“Um…um…!”

“Anwarah na fahimta, mantawa nayi, ina zuwa hakan akaci kwalliya?”

“Dama momy zamu fita da suhaila ne gurin biki, k’awarmu ce ta haihu, yau ne taron biki, umm…. Momy ai kin santa fa, wadda mukayi bukinta last year ina exam.”

“Okey! Haka ne, to ina suhaila d’in?”

“Tana gida zan biya na d’auketa muje.”

“To Allah ya tsare hanya, sai dai a kula Anwarah, kin san zamanin nan babu kyau, a dinga yin addu’a yayin fita gida, da kuma yayin shiga mota, sannan a dinga kama mutuncin kai, duk da na shaidi Anwarah sosai, nasan ba zatayi abinda ba hakan ya ke ba.”

“Insha’Allah momy, kiyi mini addu’ar zuwa lafiya, da kuma dawowa lafiya.”

“Yanzu kuwa Anwarah, Allah ya tsare hanya, ayi tuk’i da kyau.”

Da hanzari Anwarah ta fita gidan, domin ganin time zai k’ure mata gashi zata biya gurin suhaila, domin duk abinda zatayi, suhaila sai ta jishi, domin suna son k’awancensu na amana.

Motarta ta shiga, tare da jefa hand bag d’inta a gefen kujerar d’aya, sannan ta kunna motar da juyo da ita. Hon ta saki mai k’arfi, wanda ya fito da Ayuba daga d’akin gadinshi ya bud’e mata get da sauri, sannan yace,

“Allah ya tsare hajiya.”

1k Anwarah ta mik’a mishi da cewa, “kasha ruwa malam Ayuba.”

Driving Anwarah take yi a hankali, har ta isa bakin get d’in gidansu Suhaila. Ganin idan ta shiga da motar zata dad’e, hakan yasa tayi parking nata a waje ta shiga gidan.

Cikin sauri ta shiga gidan nasu, A falo taci karo da Abdul yayan su suhaila, gaisheshi kawai tayi, ba tare da ta dubi inda yake ba, shi kuma baki d’aya hankalinshi yana kanta, domin tayi mishi kyau sosai.

‘Dakin mamansu suhailat d’in ta shiga, suka gaisa tsatstsaye, domin saurin da take yi, itama mamarsu na mugun son Anwarah, don haka ko yaushe da farin ciki take tarbonta.

Anwarah d’akin Suhailat ta fad’a da sallama, suhailat ta tare ta da murna, da kod’a kwalliyarta, wadda har suhailat ke cewa,

“Allah yasa yaya na bai ganki ba, domin nasan wajibi ki rikitashi sosai wallahi, ni na rasa me yaya Abdul ya rasa da Anwarah baki son shi wallahi.”

“Suhailah….! Me yasa kike wannan maganar ne wai? Yaya Abdul na d’auke shi a matsayin yaya, tamkar yadda ki ke a matsayin k’anwarsa, don Allah ki daina wannan maganar. Kin ga ni yanzu haka a bisa hanya nike wallahi, na biyo ne na shaida miki cewa, yau zamu had’u da mutumen fa.”

“Waye kenan….? Kada ki ce mini Faisal Anwarah? Lallai Faisal yayi zarrah a zuciyarki, anya kuwa a hakan ya shiga zuciyarki kuwa?”

“Haba! Suhaila me yasa yau zaki so zuciyata tayi rauni a kan kalamanki? Na san kina son duk abinda ni ke so, wallahi Suhaila ni kaina nayi mamakin son Faisal da ya bi jiki na, ke kanki shaida ce akan rashin yadda dashi da nayi a baya, amma a yanzu wallahi ko dogon motsi nayi sai na tuna Faisal a zuciyata, suhaila mu bar zancen nan hakan, ni don Allah ki shirya ki taka mini, muje mu ganshi, in ya so sai mu dawo tare, daga nan mu biya mu gano babyn k’awarmu jidda, yau ne taron bikin ta.”

"A gaskiya Anwarah, babu inda zanje, domin bai kamata ace mune zamu isko shi ba, shi ne ya kamata ya zo gurinmu, kin san cewa ina sonki, kuma ina son dukkan za'bin ki, amma ina kishin yaya na da baki damu dashi ba, a gaskiya ba zan je ba, amma idan kin dawo kiyi mini waya, sai mu je gidan su jidda d'in."

Anwarah ta saki baki tana kallon aminiyarta, wanda ta ga chanjin fuskarta nan take, Anwarah tayi murmushi, domin ta san cewa suhailat na taya yayanta kishi ne, wanda ita ko kad’an baya tsarinta, don hakan ta juya da ce ma suhaila,

“Ba komai, kuma kada kiyi tunanin cewa, hakan zai saka naji aminiyyata ta ‘bata mini rai ko kad’an, don haka zan tafi, kuma zamuyi waya.”
Anwarah ta fad’a da rik’o hannun suhaila ta na murmushi, sanna ta k’ara da cewa, “kada kiji komai k’awata, ke kin san ba zan ta’ba yarda nayi wasa da rayuwata ba.”

“Yauwa! To Allah ya tsare, sai dai don Allah ki kare muna mutuncinmu Anwarah, duk da nafi kowa sanin halinki, Amma ina yi miki wa’azi ne, don fad’akarwa nada dad’i.”

Da murmushi Anwarah ta fita d’akin, haka suhaila ta bi bayanta domin rakata. Sallama sukayi da maman suhaila, sannan ta kama hanyar fita gidan a cikin taku mai burgewa, daga nesa Abdul ya hangota, amma babu damar su gaisa, don haka ya shareta, ya ci gaba da kallon wayarshi.

Sai da Anwarah ta shiga mota, sannan suhailat ta dawo cikin gida. Anwarah ta jawo hand bag d’inta sannan ta duba wayar ta.
“Ya salam..! 6miss call?” Cikin sauri ta tayar da motar, da duba address d’in da Faisal ya turo mata, ta tashi motar ta tafi……

Hakan take!

Bee² Ta masoya♥
[10/22, 8:28 AM] ®Bëë Bëë Tâ Māsôyä????????: ????????????????????????????????????

___________________
♦BAKI BIYU♦
___________________

® REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS P.M.L????????????

ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ

WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM

IG PML WRITERS

https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035

©®
Khadija bee bee
Khadijabellobuhari@gmail.com@gmail.com

★★★★★★★★★
Page…3⃣
★★★★

Driving Anwarah ke yi hankalinta kwance har ta iso restaurant d’in da Faisal ya turo mata address d’in. Ta fahimci hakan a ganin makeken symbol na gurin.

Murmushi Anwarah tayi, domin duk iya tsananin yawon da take yi a gari, bata ta’ba zuwa restaurant ba da sunan sayen wani abun domin ci, domin ko lokacin da suke makaranta tafi yarda da ta dafa abinci da kanta da ta fita zuwa sayen shi.

Parking tayi a inda aka tanadar domin ajiye motocin customers d’in wurin, don haka Anwarah itama ta jera ta-ta motar, tare da jawo hand bag d’inta, hannu ta saka ta jawo glass d’inta ta saka, sannan ta d’auko wayarta a hannu.

Ringing wayar ta-ta take yi, don haka sai ta bud’e motar, ta turo k’afafunta a waje, sauran jikinta a cikin motar ta amsa wayar da cewa,

“Na iso fa…. Ina parking place yanzu hakan sahibi na.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button