BAKI BIYU COMPLETE HAUSA MUSIC

“Ganinki ne ya sakani kiranki my queen, a mota kawai na hango ki, amma baki d’aya duk na rud’e, ki fito gani nima fitowa a tauwa motar, ko tsaya ma na zo na tafi da abar sona.”
Murmushi kawai Anwarah tayi, sannan ta kashe wayar domin jiranshi, kamar yadda ya buk’ata. Mayar da wayar tayi a hand bag, sai dai bata k’ara matsawa daga inda take ba, domin ita fa ta tsani irin wurin nan da kowa da kowa zai iya ganin mutun, lallai Faisal yayi fice a zuciyarta, tunda har ta iya kar’ba irin wannan gayyatar da wuri.
Ko 30second cikakku ba’a samu ba, sai ga Faisal tsaye gaban Anwarah, wani mashin so da kibiyar so suka dira a zuciyar Anwarah, wani kaurjini Faisal yayi mata a rayuwa, don haka sai Anwarah taji kunya, cikin sauri ta rufe fuskarta da mayafi, saboda kyawon da taga yayi mata a rayuwarta.
Murmushi Faisal ya yi irin mai tafiyar da hankalin mace komai taurin kanta, wajibi ne ta sauke nauyin kan nata taji wani yanayin a zuciyarta.
Ganin Anwarah ta rufe fuskarta, sai ya ya sunkuyo da fuskarshi izuwa cikin motar, ya aza hannunshi a marfin motar da ke bud’e, sannan ya saka d’ayan hannunshi ya jaye mayafin gefen, domin ganin fuskar ta-ta sosai.
Ba musu Anwarah ta saki mayafin, nan take suka had’a idanunsu guri d’aya, wani tarkon na so ya k’ara ruftawa a zuciyar Anwarah, domin ganin irin shigar da faisal ya zo da ita, wadda Anwarah na mugun son taga namiji a irin shigar, domin yana burgeta, wato shigar k’ananan kaya.
★★★
Faisal: matashi ne mai ji da kanshi, faisal nada kud’i, wanda za’a iya kiransu da ba gada yayi a mahaifa ba, Aikin da yake yi, sune suka bashi wadatar da har iyayenshi da shi suka dogara, domin sai abinda ya aiko musu suke Amfana dashi.
Faisal nada kyau, sannan wajibi ne yace yana son mace bata rufta a tarkon k’aunarshi ba. Faisal mutun ne da zai iya halakar da kud’i ko nawa ne, domin ya samu zuciyar mace, hakan zai iya amfani da miyau bakinshi domin ganin ya siyo zuciyar mace, don haka ya k’ware a iya kwalliyar d’a namiji a jikinshi. Totally dai Faisal k’wararrene kuma d’an soyayya na gaske.
★★★
Kayan jikinshi sun kar’beshi, hakan yasa Anwarah sakin baki tana kallonshi, har ya rik’o d’ayan hannunta bata sani ba, sai jin hannun nata tayi a hannunshi, da sauri ta kalleshi, amma shi ko a jikinshi, saboda duk’awa yayi gabanta kamar me neman gafara ya ce,
“Ya kamata mu shiga ciki, domin mu samu ko ruwa ne musha. Hakan zai sanyaya zuciyarmu da nasan a halin yanzu suna dangantaka da juna, oyah…, mik’e tawan.”
Faisal ya fad'a da mik'ewa tsaye, ya d'aga hannunta sama, Amma Anwarah ta saka, na farko jikinta a mace yake, saboda kallonshi kawai ya sakarmata kasala a sonshi. Na biyu kuma, ita da ma suyi maganar da zasuyi anan ta yafi, domin wallahi bata cika son zuwa irin gurin nan ba, sannan ba ma ita kad'ai ba harda saurayi, don haka ta ke ganin kamar ba zata iya shiga ciki ba, kuma ba zata iya ba. Da sauri ta kalleshi ta saita muryarta ta ce,
“Wallahi ban saba zuwa irin wurin nan ba, hakan kawai ya sakani jin ba zan iya shiga ba, don Allah mu tsaya nan a mota muyi maganar, kaga ma asiri rufe babu wanda zai ganmu bare yayi gulma.”
“My Anwarah…!” Ya fad’a raunane tare da turo mata idonshi baki d’aya, wanda cikin sauri Anwarah ta kalleshi da cewa,
“Na’am….. Kayi hak’uri muje to, amma ba zanyi 30mnt a ciki ba, kuma kayi mini al-k’awari, daga yau gida zamu dinga had’uwa ba’a nan ba, domin a gaskiya baffa ya samu labari, zai yi matuk’ar sa’ba mini a rayuwata, domin ya tsani irin hakan, don haka ban ta’ba zuwa ba, sai dai driver ya zo ya siya mana.”
Murmushi kawai Faisal yayi, sannan ya d’aga kanshi ya kalleta yace,
“Daga yau a gidanku zan dinga zuwa my Anwarah, nayi miki al-k’awarin hakan, yau ne dai kawai ni ke so mu sha ice scream tare da sahibata.”
Ba musu Anwarah ta fito a motar, da gyara mayafinta da rik’a hand bag d’inta da kyau, sannan ta rufe marfin motar, ta danna madannin remote d’in motar ta rufe motar, sannan ta juyo ta dubi Faisal wanda ya had’e hannu da a k’irji yana kallonta babu ko k’yaftawa, had’a idonshi da yayi da ita sai sukayi murmushi, sannan ya dubeta da kyau ya ce,
“Hak’ik’a nayi dace a rayuwata, Anwarah ganinki kawai na sakani shiga wani yanayi, wanda ban san ta yadda zan misalta hakan a gareni ba. Anwarah Allah yayi mini kyautar da babu wanda ya isa yayi mini ita, saura kad’an nayi hasara wadda take hasara mai ta’bewa, inda na rasa soyayyarki da k’aunarki, kamar yadda a farko kika kasa yadda da aminta dani, wallahi nayi 3days ina fama da zazza’bi, amma a yau gani ga ki a matsayin masoyan juna, wajibi ne nayi murna sosai.”
Wad’annan kalaman na saka Anwarah zaucewa daga hayyacinta, wanda hakan kawai ya sakata jin, bata da mijin aure wanda ya wuce Faisal, kuma ita wallahi tafi k’aunar suyi aurensu da wuri, domin tasan hakan shine burin baffa da momy a yanzu, don haka a yanzu ta shirya shaida musu za’binta a rayuwa, domin tasan zata iya samun natsuwa da Faisal, domin kasancewarta mai mugun son love a rayuwarta, don haka sai taji, ta samu abokin wasa a babban falonsu na aure.
Nan take tayi taku izuwa inda yake, sannan tayi murmushi da lumshe idonta tace,
“Lokaci na k’urewa bamu sha abinda kace kana so musha ba, kuma ka tsaya kana wani tunanin da bansan waye kake tunawaba, bayan gani tare da kai. Please….! Don Allah ka daina tunani na gani nan a gabanka muje.”
Saida yayi murmushi, sannan suka kama hanyar shiga *Seven O seven restaurant* d'in. Wuri ne na sai wane da wane ke iya zuwa domin cin abinci, sannan wurin ci da sha kenan na masoya, wanda aka tanadi nasu wurin na musamman domin an k'awata wurin da kyawawan flowers, waji bi ne kaji wurin ya shiga ranka lokaci d'aya idan ka iso.
Tunda su Anwarah suka shigo idon kowa a idonsu, domin sun burge kowa, hakan yasa kowa yayi musu d’aukar mata da miji ne a irin yadda aka gansu. Faisal ya samama Anwarah wata kujera da ke gefe ta zauna, sannan ya isa gurin biyan kud’in inda zasu ci abincin da kuma wurin da zasu zauna domin k’awata k’aunarsu. Aka bashi receipt sannan ya matsa inda Anwarah d’in take ya mik’a mata hannu alamar ta taso suje.
Sai da Anwarah ta duba kowa da ke gurin idonshi a kansu yake, don haka sai ta mik’o mishi hannu domin kada ta kunyatashi, sai dai lokacin da ta mik’e takalmenta d’aya yaso mak’alewa da d’ayan takalmen, nan take k’afar ta hard’e d’aya zata fad’i, da sauri Faisal ya rik’ota da had’e jikinshi cikin nata, wanda hakan ya burge kowa da ke gurin, amma hakan bai yima Anwarah dad’i ba ko kad’an, domin bata sababa, k’arshe ma, hakan bai ta’ba had’ata da kowa ba, kallon sa kawai tayi, sannan ta yi saurin matsawa daga jikinshi, shi kuma ya ce mata.
“Sorry dear! Da kin fad’i da naji babu d’ad’i, sai dai gangar jikinmu ba zata ta’ba barin d’ayan jikin ya sha k’asa ba, sannu! Gyara mu tafi.”
Murmushi Anwarah tayi, shi kuma dad’i yaji sosai, sannan suka wuce inda zasu je. Suna karya kwanar wurin, sai ga wasu mata su biyu sun fito a kwanar, murmushi sukayi da ganin Faisal yayi aure, da sauri suka matso domin tayashi murna. Shi kuma dad’i yaji domin yasan labarin zai isa a inda yake son ya je.
Kallon da d’aya daga cikinsu tayi mishi ne, ya saka Anwarah dubanshi, sai dai maganar da ta ji d’ayar nayi ma Faisal da murmushi ya sakata sakin fuska,
“Oga Faisal congratulation, gaskiya kun dace da juna, sai dai kuma auren sirri haka, ba tare da kowa yaji ba? Lallai anyi mana ba zata a wannan shagali da mukayi missing.”
Faisal murmushi ya saki, da saurin bud’e bakinshi ya ce,
“A A Nafeesa ba’a riga akayi shagalin bikin ba, amma tabbas ba ki yi k’arya ba, ni da ita mata da miji ne, kuma ma har komai ya zo k’arshe, date kawai muke jira.”
Faisal ya fad’i zancen da rik’o hannun Anwarah, sannan ya kalleta. Itama shi ta kalla da mamaki cike a zuciyarta, domin tanada alamomin tambaya da yawa a wannan tsayuwar, sai dai gudun kada ta bayar dashi, sai itama tayi murmushi da duban ‘yan matan guda biyu.