BAKI BIYU COMPLETE HAUSA MUSIC

Dariya su ka yi, sannan suka gaisa da Anwarah sosai, tare da gabatar mata da kansu cewa, su abokan aikinshi ne a office nasu, sannan suka wuce abinsu cikin fara’a
Direct wurin suka shiga, wuri ne wanda shi kad’ai zai iya saka ka farin ciki, domin wuri ne mai saka natsuwa. A gaskiya wurin ya burge Anwarah matuk’a, wanda hakan ya sakata manta tambayar da zata yi mishi.
Ba su dad'e da zama a capet d'in da aka shimfid'a a makeken wurin ba, suka hango ma'aikacin gurin a cikin k'ofar glass d'in da aka killace gurin da shi, basket d'in nan mai tayoyi ne yake turawa, wanda knocking d'aya yayi Faisal ya ta so ya bud'e mishi.
Shigowa yayi da kayan tand’e-tand’e da lashe-lashe, wanda ga su nan barkatai, ya jera musu su a nan k’asan capet d’in, sannan ya juya ya tafi.
Dukkan abinda aka kawo a wurin, ba bak’o bane ga Anwarah, don haka ko kad’an basu burgeta ba, amma tsarin wurin ya burgeta sosai.
Faisal yaga Anwarah bata da niyyar d’aukar komai a gurin, hakan ya sakashi ce mata,
“Kina nufin kunyata ki ke ji…. Shi ya saka ba za ki ci komai ba?”
Anwarah ido kawai ta bishi da da su, sannan ta d’an had’e fuska da cewa,
“Ni wad’annan kayan ba bak’i bane a gurina, domin a gida yanzu hakan na baro su a fridge d’ina, sannan sauran kuma, baffa yana siya mana domin kada mu fita waje nema. A gaskiya Faisal idan dai har kana sona da gaske, kamar yadda ka fad’a mini, to had’uwarmu ta kasance a gidanmu, domin a gidanmu ma, munada gurin shak’atawa, kamar irin hakan. A yanzu ma ina rok’on Allah ya saka babu wanda ya ganni, wanda yasan ‘yan uwana da baffa a gurin nan, domin idan aka ji wallahi zan ji babu dad’i.”
Tunda Anwarah ta fara magana, Faisal ke kallon d’an k’aramin bakinta, yadda bakin ke zuwa da dawowa, idanunta suna lumshewa kamar mai jin barci, ya saka Faisal jin wani yanayi a jikinshi, hakan yasa ya ajiye Ice cream d’in hannunshi ya matso kusa da ita ya rik’o hannunta da cewa,
“My Anwarah kin fi kowa sanin irin son da ni ke yi miki, A gaskiya ba gidanku ne bana son zuwa ba, A A sai dai a rana ina son na dinga ganinki kamar sau biyu, wanda nasan cewa, dole a gidanku a saka mini idanun zuwa akai-akai, amma daga yau Insha’Allah ba zamu k’ara zuwa irin nan gurin ba, zan dinga zuwa gidanku, shi ke nan damuwar?”
Murmushi Anwarah ta yi, sannan ta kad’a kanta alamar aminta da zancenshi. Rik’on hannun Anwarah da Faisal yayi, sai Anwarah ta ji duk jikinta babu dad’i, domin yanayin yadda yake kallonta, da sauri ta jaye hannunta da matsawa da jikinta baya.
Duk da mayafin da ke jikinta, amma babu abinda yake kallo kamar k’irjinta, hakan yasaka Anwarah gane cewa, Tabbas! Yin hakan ba halinshi bane, amma ta lura sonta ne ke kawo wannan yanayin, domin itama ta na jin yanayin a jikinta.
Faisal ya fahimci sauyin da Anwarah tayi, don haka sai yayi saurin kawar da wancen zancen da yake niyyar aiwatarwa, sai ya juya ya d’auko Ice cream da ce mata,
“Bud’e bakin ki, ni zan baki.”
"A A Faisal ba zan sha ba, don Allah mu tashi mu tafi, domin ba na jin dad'i wallahi, kaina ciwo yake yi."
“Haba My wife, maganar da na zo muyi, ko ita fa bamuyi ba.”
“Gaskiya ni kuma, ina sonka sosai, sai dai irin abinda nike ji ba zai iya bari na naji zancen da kyau ba, amma ka tashi muje gidanmu a cen zanfi fahimtar zancen da kyau, amma anan ba zan gane komai ba, sonka zai iya tasiri a zuciyata.”
Murmushi Faisal yayi, domin ya fahimci manufar Anwarah, kuma shima ba hakan bane a rayuwarshi, dama burinshi ta so shi a zuciyarta, sannan buk’atar shi, a hakan ma ta biya, domin son yake yi yaga ta yadda sonshi ya mamaye zuciyarta, kuma ya gane gaskiyar sonshi a irin hakan.
Mik’ewa Anwarah tayi, jikinta babu k’wari ko kad’an, da sauri ta nufi hanyar fita gurin. Da sauri Faisal ya rik’o mayafinta, wanda ya sa’bule zai fad’o, Anwarah tayi saurin rik’e rabin mayafin nata a k’irjinta, wanda hakan ya saka Faisal mik’ewa da saurin mayafin a hannunshi ya matso kusa da inda take yace,
“Anwarah me zai saka ki tafi ki barni? Kin kuwa san yadda sonki ya fara yi mini illah a yanzun nan? Wallahi idan har kika ce zaki barni, to zaki iya samun labarin na rasa rayuwata, domin zan iya shan guba na mutu akan sonki. Anwarah wallahi ina sonki, kuma sonki ba zai iya bari na na cutar da ke ba, ki yarda dani, zanyi miki duk abinda kike so, amma ki sani ina sonki so na gaskiya.”
‘Innalillahi! Me ke shirin faruwa dani ne? Me nike ji a zuciyata? Karayar zuciya? Ko kuwa soyayya mai tsanani? Hak’ik’a Faisal ina sonka, so na gaskiya, bana jin akwai wata soyayya wadda tafi wannan, amma zuwa gidanmu shi zai iya tsayar mana da gudun fad’awa irin abinda nike ji a zuciyata, wanda ni ke jin komai zaka yi mini ba zanga illarsa ba.’
Anwarah ta na wannan zancen ne a zuciyarta, wanda tana zancen zucin ne, tana kallon fuskar Faisal da ke kallonta da kallon so mara misaltuwa, wanda bayanta yake jingine a k’ofar glass d’in gurin. A hankali Anwarah ta fara jaye saurar mayafinta don ta gyara rufe jikinta, domin bayyanar da k’irjinta yayi a d’unkin da ke jikinta kad’ai ta san zai k’ara sauya Faisal, kuma ita wallahi bata son hakan ko kad’an.
Tajanye mayafin, amma kuma hannunta ya rik’e, sannan ya nuna mata zuciyarshi da yatsanshi d’aya, wanda nan take k’walla suka zubo mishi a idanunshi, firgicewa Anwarah tayi, sannan bata san sadda ta rik’o hannunshi d’aya ba ta ce,
“Haba my Dear! Kana son mu kasa tafiya daga nan ne? Faisal akwai matsala, akwai matsala wallahi, ba wai zan tafi bane don bana sonka ba, A A wallahi sai don mu kare mutuncinmu, saboda mu kasance tare, ya saka nike son mu had’u gida, domin na gabatar da kai da wuri, don asaka aurenmu a k’an-k’anen lokaci, a lokacin zaka fi samun duk abinda kake so a gareni.”
Gaban Faisal ya fad’i, wanda hakan ya sakashi sakin hannun Anwarah, itama data ga ya saketa, sai ta sakar mishi Hannun. Hakan ya bashi damar goge k’wallar fuskarshi, domin yaji maganar gaskiya da k’afafunshi tana yawo.”
“Idan dai har da gaske Anwarah za ki aureni, to na aminta da hakan, zamu dinga had’uwa a gidan naku, sai dai ina fatar babu wata matsala ko? Domin kada na fara zuwa a samu matsala, duk da shirye nike da d’aukar ko wane irin k’alubale ne akan sonki. Insha’Allah, my Anwarah ni ne abokin rayuwarki.”
Murmushi tayi, sannan ta ce mishi,
“My Faisal nima na baka dukkan yarda da amincin kaina, sannan zan nuna maka k’auna, irin wadda ba’a ta’ba gani ba a tarihin rayuwar masoya, sannan kuma……….”
Kiran wayar Faisal shi ya hana Anwarah fad’in kalmar da zata fito a bakinta, sai tayi shiru da duban shi, domin kada ta hanashi d’aukar wayar, sai dai duba wayar tashi da yayi, sai kuma ya dubi Anwarah da yaga tana kallonshi, k’ara duba mai kiran wayar yayi, sannan kuma sai yayi alama kamar ta rashin gaskiya, sai ya kashe wayar da yin tsaki yace,
“Mtsww..! Haka kawai ka dame ni da zancen bani-bani, ko yaushe mutun babu godiyar Allah, ana bashi amma baya godewa, ni har zai ‘bata mini rai wallahi, sai dai Anwarah na tana kusa dani, babu mai ta’ba zuciyata.”
“Hmmm! Sosai kuwa, amma don Allah me yasa ba zaka taimaka mishi ba, may b da kai ya dogara a duniya, kuma yasan kana bashi shiyasa zai dameka, don Allah ka kirashi kace zaka bashi ko me ya ke so, idan kuma baka da, ni zan baka ka bashi, kira shi please.”
“Noooo! Barshi kawai, zan kirashi a baya, ba na son ina tare da ke, ana damu na, muje kawai.”
Wannan abun kad’ai zai iya saka Anwarah gano, menene Faisal baya so ta sani? Sai dai kash!! Anwarah yarinya ce, kuma wadda wannan shine farkon fara jin ta na son d’a namiji a rayuwarta. Hakan yasa komai ba ta ganewa, sai kalmar so da soyayya sai kuma k’auna, iya wad’annan kawai ta sani, amma bata fahimtar sharhin d’aya daga cikinsu, don haka take tafiya da kalmar “mu masoyan juna ne, kuma mu masu k’aunar juna ne, zamuyi aure, domin son da nike yi miki.”