BAKI BIYU COMPLETE HAUSA MUSICNOVELS

BAKI BIYU COMPLETE HAUSA MUSIC

Su kad’ai Anwarah ke ganewa, amma k’urciya da yarinta su ne gaba a lamarinta.
*

Sun kama hanyar fita gurin, inda Faisal ya samu laida ya zube kayan da aka kawo musu, wad’anda ba’a ta’ba.
A irin takun farko, a irinshi suka bar gurin, wanda kowa ke musu kallon ma’aurata ne su.

A bayansu kuma, akwai wanda tunda suka shigo yake biye dasu, har suka fito kuma idonshi akansu yake har sa’adda Faisal ya raka Anwarah ta shiga mota, wanda shima sai da ya d’ad’e a bakin motar, ya sakama Anwarah kayan a gaban mota, sannan sukayi bankwana ya wuce, da ce mata, za su yi waya.

Bayan ta wuce ne, shima ya kama hanyar motarshi, da ciro wayarshi, domin kiran number da ta kirashi, abu d’aya na’iya ji a lokacin da zai bud’e motar ya ce,

“I’m sorry please! Wallahi ko……….”

Ban ji sauran zancen ba, saboda rufe marfin motar da yayi, da kuma tayar da bak’in glass d’inshi da yayi, sannan ya tuk’a motar ya tafi

Wanda yake binsu a baya, tunda yaga sun wuce, shima sai ya kama gabanshi yayi gaba, domin cin abinci ya kawo shi gurin, ganinsu ya saka ya kasa tafiya, domin yaga sabuwar rayuwa a gidan Alhaji muktar Baffa.

Anwarah ta kasa komawa gidansu Suhaila, sai dai kawai tayi mata waya ne a motar da ce mata, gata hanyar gida, su daina zuwa bikin nan, gobe sai suje suga baby.

Suhaila tayi mamakin jin hakan, sannan tayi mamakin cewa Anwarah zata koma gida, da alama ko 1hour bata yi da barin gidansu ba, Anya kuwa ta ma ga Faisal d’in kuwa? Babu lokacin tambaya anan, amma gobe zata je gidan da kanta taji ko menene.

“Allah ya sa ta daina son Faisal d’in nan, ba don komai ba, sai don ina son yaya Abdul ya auri Anwarah ta.”

Da wannan zancen suka rabu a waya.

  *ASALIN LABARIN*

Ku biyo ni a hankali, domin jin wannan sark’ak’k’en al-amari da ke cikin labarin BAKI BIYU, kada a manta, akwai fad’akarwa, wa’azantarwa, da kuma babban jigon taken nawa, wato soyayya mai gardi. Muje zuwa kawai.

Bee²Ta masoya♥
[10/24, 9:10 AM] ®Bëë Bëë Tâ Māsôyä????????: ????????????????????????????????????

___________________
♦BAKI BIYU♦
___________________

® REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS P.M.L????????????

ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ

WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM

IG PML WRITERS

https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035

©®
Khadija bee bee
Khadijabellobuhari@gmail.com@gmail.com

★★★★★★★★★
Page…4⃣
★★★★

  *ASALIN LABARIN*

BIRNIN ABUJA: Gari ne da masu abin hannu suka fi kwad’aituwa da su zauna a ciki. Galibin mutanen da ke cikin garin ba nan ne asalin mahaifarsu ba, sai dai daga baya su kwaso iyalinsu su dawo dasu a cikin birnin, wanda a ciki za’a dinga haihuwar wasu ‘ya’yan daga ciki.

‘Daya daga cikin ‘yan taho na tahon garin, aka samu Alhaji muktar Ahmad (baffa), Alhaji muktar (baffa) d’an asalin garin jahar sokoto ne, iyayenshi da kuma danginshi duka suna a garin na sokoto, sai dai sanadiyyar d’aukaka da wadata da Allah ya bashi, ya sakashi jawo ‘yan uwanshi maza yana dawowa dasu a garin kaduna yana sama musu aiki, wanda hakan yasa suma suka samu gurin zama da matansu da iyalansu a garin kaduna.

Jin dad’i ya sakashi d’auko mahaifiyarshi daga sokoto, ya dawo da ita a garin kaduna, domin ya kyautata rayuwar mahaifiyarshi.

Alhaji muktar (baffa) asalinsu fulani ne, wanda uwa da uba duka a rugga aka tashi, haka shima a ruggar ya tashi. Bayan haihuwarshi da kwana goma Allah yayi ma mahaifinshi rasuwa, Haka d’aukar nauyinsu ya koma a k’ark’ashin yayan mahaifinshi, saiddai babu kyautatawar yau bare ta gobe, haka suka taso cikin k’unci, wanda sanadiyyar Hakan muktar ya rasa ‘yan uwansa guda biyu maza, wanda ya rage shi kad’ai ne ga mahaifiyarshi sai ‘yan uwa.

Allah ya wadata muktar (baffa), da arzik’i mai tarin yawa, wanda idan za’a kira mutun ukku a garin Abuja a gefen masu kud’inta, to za’a iya kiranshi da na hud’u, idan ka cire shugaban k’asa. Shi d’an kasuwa ne, wanda saye da sayarwa ne aikinshi, yana siyar da motoci da mashuna, wanda duk wata sabuwar mota da zaka ganta ta yayi, to ta company din shi suke shigowa, ta hakan yayi suna sosai, kuma d’aukaka na shigo shi, babu rowa, babu k’yashi ga d’an uwa, bare kuma talakan da ke tare dashi.

Alhaji Muktar Ahmad (Baffa), yanada mata ukku, Ta Farko ita ce, Hajiya Halima, wadda sukayi aure da ita saurayi da budurwa, Hajiya Halima itama ‘yar Asalin garin sokoto ce a cikin wani gari da ake kira Tambuwal. sun had’u Alhaji muktar ne a lokacin bukin wani abokinshi a sokoto, wanda suka fara soyayya, har aure ya tabbata, aka kawota a garin kaduna kafin ya samu ci gaba, su koma Abuja.

Hajiya Halima ita ce uwar gidanshi, kuma ita ce uwar babban d’anshi mai suna Ahmad (Anwar Baffa), Ahmad ya ci sunan kakanshi ne, don haka suke kiranshi da Anwar. Hajiya Halima nada kunya sosai, shi yasa ba lallai ka gane ita ce ta haifi Anwar ba, domin bata kula da duk wata rayuwa tashi, hakan yasa bata damu da rayuwarshi ba, shima shi yasa baya damuwa da ita sosai, shi yasa yake zamanshi a kaduna gurin kakarshi.

Hajiya Zuwairah ita ce matarshi ta biyu, ya aureta ne, domin yana burin yaga gidanshi da zuri’a sosai, domin tun bayan haihuwar Anwar, ba’a sake haihuwa a gidanshi ba. Ita ‘yar Asalin minna ce, niger state, ya aureta ne a lokacin da suka had’u a wurin wani taro, dama yana son ‘ya’ya, dayaga kamar zai iya samu a gefen ita zuwairar, sai dai hakan kuma bai samu ba a gurinta. Ganin zata ta tashi tutar babu, anan ta fara biyar bokayen garinsu domin ganin ta mallaki gidan, ta hakan ne ya sakata d’auko d’iyar yayarta Anisa ta rik’eta a gidan, wanda saboda girman magani, ko me Anisa zata yi, babu mai iya cewa k’ala, domin an mallake kowa.

Hajiya Aisha ita ce k’arama, kuma ita ce yarinya a cikin matanshi, domin ita tayi karatu sosai, hakan yasa ta d’an tsaya batayi aure da wuri ba, Alhaji muktar na son Aisha, domin kyautatawa da kuma wayewarta, ga shi tana son mahaifiyarshi sosai, da hakan ta samu zarrah daga sauran matanshi, duk da yana k’aunar uwar gidanshi sosai, amma yana son Aisha fagen kyautata mishi.

Hajiya Aisha ta dad’e itama bata haihu ba, kasancewarta ma’aikaciyar Asibiti a wancen lokacin sai ake ganin kamar tana wani abunne, domin kada ta haihu da wuri, sai dai ita komai bata yi ba. Ita ‘yar asalin garin katsina ce, Aiki ya kawo mahaifinsu kaduna, anan suka had’u da Alhaji muktar (Baffa), Hajiya Aisha su biyu ne kachal a gurin mahaifinsu da kuma mahaifiyarsu, don haka suke k’aunar juna da ita da yayarta Khadija,d’aya baya abu sai d’aya ya sani, duk da Khadija na gaba da ita sosai, amma a haka suke rayuwarsu.

Khadija ta yi aure shekaru da dama, amma da ta samu ciki sai ya zube, ko kuma ta haihu, jariri baya da rayuwa, ta yi haihuwa tafi a k’irga a rayuwarta, wanda sai ta cire rayuwa da samun baby sai kuma Allah ya bata wani. Tunda ta samu wani cikin, mahaifiyarsu ta duk’ufa rok’on Allah ya sa ya tsaya, ko zata ga jikokinta a duniya, wanda aka bata shawarar ta nema mata taimako ko iska ne ke saka wannan matsalar, ba musu mahaifiyarsu ta yadda da zancen mutane ta tafi wurin wani malamin addini, anan ya tabbatar mata da cewa akwai sa hannun mutanen ‘boye, sai dai saka su akayi, k’arshe ya tabbatar mata da cewa, Aikin kishiyar Khadijar ne, domin bata son ta haihu, ya bayar da taimako, da kuma rubutu da addu’oi yace a dinga yi mata.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button