BAKI BIYU COMPLETE HAUSA MUSIC

Cikin Ikon Allah sai ga ciki nata girma cikin k’oshin lafiya, wanda ko yaushe Aisha na gidanta don kula da ita, shima baffa bai hana ba, domin yasan yadda suke da ‘yar uwarta, don haka shi zai kawota har ya tsaya su gaisa sannan ya wuce.
Ranar da nak’uda ta taso mata, ita kad’ai a gida, mijinta Alhaji Ibrahim khaleel, yana a gidan d’ayar matarshi, tayi kiranshi a waya, amma yak’i dagawa, domin yana tare da matarshi d’aya, wadda ta asiranceshi, ko motsi sai ta ce yayi zai yi.
Nak’uda mai muni Khadija ke yi, wanda lokacin da ta kira Aisha har ta galabaita, Da gudu suka fito a gidansu ita da baffa, domin ganin yadda hankalin Aishar ya tashi, dukansu babu wanda yayi wanka, kasancewar a part d’inta yake,kuma a lokacin ma suna bisa kan sunnah soyayyarsu kiran ya shigo.
Ita da baffa suka d’auki Khadija zuwa Asibiti, bayan Aisha ta bata taimakon da taga zata iya, amma abu ya faskara, don haka sai Asibiti.
Shigarsu kenan aka biya komai na aiki, wanda har saka hannu baffa shi yayi aka yima Khadija aiki, nan take aka ciro tsaleliyar yarinya mai mugun kyau, wadda aka mik’awa Aisha ita a hannu, amma saboda son ganin ‘yar uwarta, ta mik’ama baffa babyn tayi sauri ta fad’a d’akin, domin ba za’a hanata ba, kasancewarta ma’aikaciya wurin.
Ko da ta shiga, sai ta tarad da yayar tata na barci, don haka ta barta, domin taga alamar sauk’i sosai ta fito.
Baby na hannun baffa, wanda kallonta kawai yake yi, a hakan Aisha ta iskoshi, har sai da tayi murmushi, domin ganin yadda yake farin ciki, wanda tayi addu’ar Allah ya basu nasu tare.
Wayarshi ta kar’ba ta kirawo mamarsu, da kuma k’anen mahaifiyar tasu, wanda nauyin uwarsu yake kanshi tun bayan rasuwar mahaifinsu. Cikin gaggawa suka iso wurin suma, murna a gurin ummarsu ba’a cewa komai, ta kar’bi baby a hannun baffa d’in.
Bayan kusa 30mnt sai Aisha ta tuno halin rashin tsalkin da suke ciki ita da mijinta, sai ta nemi da su je gida su dawo, amma zata je da baby, domin a yi mata wanka, kuma su kwaso kayan da suka kamata, babu wanda yayi musun hakan, domin ma’aikaciyar Asibiti ce.
Sai data fara yowar wanka ta fito, sannan ta kar’bi babyn hannun baffa, shima ya je ya gyara jikinshi,sannan suka yima baby wanka, ta had’a madara ta bata saboda tsutsar hannun da ta ga tabayi, don haka dama suka biya suka sassayi duk abinda,ake buk’ata, ciki harda madarar baby d’in, domin ba zata sha nono ba, sai gobe.
Suka shirya suka dawo asibiti, anan suka tarad da Khadija ta farka, tana son taga abinda ta haifa, cikin gaggawa, Aisha ta sauke baby da aza mata ita a gefen hannunta na dama, kallon babyn tayi, sannan k’walla suka fito mata, ta kalli mahaifitarsu, ta kalli baby ta ce,
“Alhamdullah! Ko yanzu na gode ma Allah da ya nuna mini, ina cikin bayinshi masu ganin ‘ya’yansu a duniya, umma kinga na cika miki burinki na ganin jininki sun kawo miki jika, ga nawa nan, saura na k’anwata, itama Allah ya kawo mata, amma idan ta yaye wannan, shin menene ma aka samu…mace ko namiji?”
“Mace ce yaya khadija.” Aisha ta fad’a tana murmushi, itama murmushi tayi da cewa,
“To Allah ya raya miki d’iyarki Aisha, ki rik’e amanar yarinyar nan, tamkar wadda zaki haifa, sannan idan tayi laifi a hukuntata, amma idan bata yi ba, kada a ta’bata. Umma kawu Abu, ku shaida cewa, babyn nan ta Aisha ce, ban yarda abawa mahaifinta ita ba wallahi, kuma ban yarda ko da wasa taje gidanshi ba, Alhaji muktar, daga yau babyn nan taka ce, na baka ita halak malak, amma idan kasan zaka cutar da ita, to kada ka d’auki alk’awarin kar’barta, domin ba zan yafe cutar da ita ba.”
Cikin tsoro baffa ya kalli duk mutanen gurin, Kowa kuka yake yi, amma ita dariya da hawaye ke fita fuskarta, kuma magana take yi, tamkar tana wasiya ne. cikin tsoro Aisha ta ce,
“Haba Yaya Khadija! Me yasa kike irin wannan zance? Ai ciwo ba mutuwa bane, kuma yanzu me ya rage muna face murna kin fita lafiya? Ko baki fad’a ba, babyn nan ai tawa ce, kuma duk d’anda zan haifa, ba zai kaita a gurina ba, domin ita muka fara gani, please! Ki daina.”
Ummarsu ta gano Khadija bankwana ne take yi masu, don haka sai hankalinta ya tashi, shi kuma baffa ya riga da ya gano me khadija ke fad’i. Banda murmushi babu abinda take yi, cen kuma sai tace,
“Aisha ku d’auke babynku, hannuna ya fara ciwo.” Ba musu Aisha ta d’auko baby ta mik’oma ummarsu, ita kuma ta mik’ama baffa, suka juya suna sauraron maganarta da ta ke cewa,
“Aisha ki kula da umma don Allah, kada ki barta tanemi wani abin ta rasa, inda hali, ki sayamata gida a garinku ta koma kusa daku, kin san komai gameda account dina, sannan ku sakama baby suna naji, domin kune uwa da ubanta.”
Aisha kuka take yi sosai, haka kowa ma sai da yayi hawaye, nan take baffa yayi ma babyn hud’uba da saka mata Khadijah, duk da babu wanda yaji.
Furucin khadija na k’arshe shine, “Ki bama Ibrahim sak’on cewa, na yafe mishi, saboda nasan ba laifinshi bane, saka shi akayi, kuma ki ce……….”
Ai bata k’arasa fad’ar zancen ba, tari ya sark’eta, da gudu Aisha ta yi mata abinda ake yi ma masu aiki idan tari ya taso musu, gani yak’i tsayawa, kawu Abu ya kira likitoci domin su duba.
Da sauri suka shigo suna fad’a akan magana aka sakata, gashi ta zamar mata illah, sunyi k’ok’arin tsayawar tari da allura, wanda suke ganin barci ne ta samu, amma kuma lokaci ne yayi, don haka suka ce su fita daga waje, wanda wata nurse ta jawo Aisha suka fito waje.
Likitan da yayi ma Khadija Aiki shi ya shiga ya dafa hannun khadija yaga ruwan da suka saka mata basu tafiya, anan ya gano ta rigamu gidan gaskiya.
Babu jinkiri ya sanar dasu, baki d’aya sun rikice, wanda Aisha da umma sai da aka rik’asu.
Nan take Aisha ta mik’a hannu ta kar’bi baby da kallon baffa tace,
“Menene sunan da ka saka mata.?”
Yace, “Khadija na saka mata, sai dai za’a kirata da (Anwarah).”
Kowa yaji dad’in sunan sosoi, nan take akayi gida don yima khadija sutura da kaita makwancinta, sannan Aisha ta duk’ufa neman maganin da zata sha domin ta shayar da khadija, wasu suce saboda bata ta’ba haihuwa ba, ba zayayi ba, wasu suce tunda har ta ta’ba miscarriage, zata iya shayar da baby.
Da haka suka nemi magani Aisha na shayar da khadija Anwarah, tare da taimakon madarar jarirai.
Bayan kwana arba’in da rasuwa, sai ga Alhaji Ibrahim da kunya tayi mishi kad’an ya zo gaisuwa, da cewa baya k’asar, shiyasa bai samu shigowa ba.
Babu wanda ya kulashi, iyaka an nuna mishi d’iyarshi daga nesa, sannan aka fad’a mishi sak’on matarshi. Yaci kuka kamar ranshi ya fita, k’arshe ya bar gidan. Tunda daga lokacin ciwo ya kamashi, wanda shi ne ya zama ajalinshi.
Bayan wata ukku da rasuwarshi, sai ga abokanshi sun zo har gidan baffa, domin kawo wasiyyar da ya bari a ba ma d’iyarshi.
Takardun kud’i ne, da kuma kud’in mahaifiyarta da ta bari a hannunshi, baki d’aya ya tattaro da takardar neman gafara, da yace a bawa d’iyarshi. Aisha ko kallon kud’in bata yi ba bare takardar hannunshi, don idan da a hannunta takardar tazo, da sai ta yagata, domin bata son ma ‘yarta ta taso da sanin ba su ne mahaifanta ba.
Anwarah nata girma, son duniya Alhaji baffa ya d’aura akan Anwarah, domin k’aunar da yake yima Anwar d’inshi da ya haifa, ba zai fi k’aunar Anwarah a zuciyarshi ba.