BAKI BIYU COMPLETE HAUSA MUSIC

Anwarah ta taso a gata, gata wanda yake gata, kasancewar kowa da part d’inshi, babu ruwan kowa da kowa, sai cen baka rasaba, Aisha na shiga part d’in uwar gidan, wato mahaifiyar Anwar, kasancewar ita ba zaka ga fushin kishinta a fuskarta ba, ko da akwaishi a zuciyarta, hakan yasa zata iya gaisawa da kowa a cikinsu.
Aisha na girmama kowa a cikinsu, sai dai zuwairah kowa kishi take yi dashi, babu babbar babu k’aramar, duk da kishin nata da neman maganinta, bai hana Allah yak’i bata haihuwa ba, domin sheka da shekaru babu haihuwa, sai iya shegen yima mata gori iri-iri, wanda daga ciki, har da cema Aisha Uwar marainiyya.
Aisha bata damuwa da sha’aninta ko kad’an, domin idan ta dawo aiki, tana a part d’inta, suci firarsu da asabe ‘yar aikinta, wadda da aure take yi mata aiki, da kula kuma da Anwarah.
Alhaji Baffa ya matsa Anwar ya dawo Abuja, amma ko kad’an baya son gidan nasu, yafi k’aunar kaduna gurin tsohuwar kakarshi da yake yima kirari da budurwarshi, sai dai yakan shigo akai-akai garin, kuma shima kwana biyu ko ukku.
A haka rayuwar gidan ta d’inga tafiya, wanda ke son zaman lafiya yayi, wanda ke son rashin zaman lafiya shima yayi abinshi shi kad’ai, tunda,kowa na part d’inshi, kuma da nisa tsakanin part da part, ko kuwa d’aya ke yi, in ba sama ya hau ba, d’aya ba zai ji ba, kuma matsayin kowa daban a zuciyar mai gidan, yasan mai hak’uri, kuma yasan mai kyautata mishi, kuma yasan mai musguna mushi.
A haka suke rayuwar gidan har shekarun su Anwarah na mik'awa...............
Bee²Ta masoya♥
[10/26, 8:47 AM] ®Bëë Bëë Tâ Māsôyä????????: ????????????????????????????????????
___________________
♦BAKI BIYU♦
___________________
® REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS P.M.L????????????
ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ
WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
IG PML WRITERS
https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
©®
Khadija bee bee
Khadijabellobuhari@gmail.com@gmail.com
★★★★★★★★★
Page…5⃣
★★★★
Anwarah ta taso cikin gata, da soyayyar iyaye da kakannin bangare biyu, wato kakarta ta wurin mahaififarta, da kuma mahaifiyar alhaji baffa wadda itama Allah ya sanya mata k’aunar Anwarah d’in, tun ranar da d’anta yaje mata da zancen an bashi Anwarah kyau, k’arshe ma shine ya rad’a mata suna, hakan yasa yayi ma Anwar ‘yar uwa da kalar sunanshi, ita kuma Anwarah. Mahaifiyarshi ta yi murna sosai, domin tana son Aisha saboda yawan kyautata mata da take yi.
Anwar a lokacin yanada shekaru goma a rayuwa, domin ya kai primary 6 , wanda idan suka je kaduna suka ganshi, sukan nuna mishi Anwarah, suce suma sun samu tasu baby, tunda shi ya gujesu, amma ko a jikinshi, domin shi a yanzu yafi sabawa da tsohuwar matarshi, ba lallai suyi komai ba don su burgeshi ba, domin shi Abujar bata burgeshi.
Kwance tashi gurin Allah ba komai bane, Anwarah nada 6years a duniya, Allah ya bama momynta ciki, lokacin da cikin ya girma ne, zuwairah kamar ta mutu, domin idan waccen ba d’iyar mijinta bace, to wannan cikin kuma na waye? Hankalinta ya tashi, tabi duk yadda zatayi taga cikin ya zube, ko ya samu matsala, amma Allah bai yi ba, domin sai da cikin yakai lokacin haihuwarshi.
Lokacin da nak’uda ta taso mata, anan gida tabar Anwarah wurin Hajiya Halima, domin ta san har abada ba zata ta’ba cutar da Anwarah ba.
Zuwansu asibiti ba da dad’ewa ba, Allah ya sauki momyn Anwarah lafiya, ta samu baby girl.
Murna gurin ‘yan uwa da abokan arzik’i ba’a cewa komai, kowa murna yake yi, amma banda zuwairah da hauka kawai ya rage tayi.
Ko da za’aje dubo mai haihuwa a asibiti, cewa tayi aiki take yi, domin oga a part d’inta yake. Anisa ta matsa akan tana son taje, amma zuwairah ta dage akan cewa, waye zai rik’a mata aiki? Don haka idan shisshigin take son tayi, to ta bari su dawo gida sai taje ta gansu.
Hajiya Halima kuma ko a jikinta, domin ita bata ga abun kishi anan ba, domin ta san haihuwa Allah ke badawa, idan har zaka dinga yak’i da Allah, komai naka zai dinga yin baya, don haka idan dai kishi ne, tana yi irin na musulunci, amma kuma ba mugun kishi irin wanda babu abinda yake jawo maka sai wahala, don haka ba ta’ba jin haushin wata daga cikinsu ta haihu ba, domin tasan rashin yawan haihuwar daga Allah ne, sannan ita da ke da d’a namiji, tasan zai yi aure, kuma zai haihu da izinin Allah, don haka bata ta’ba damuwa ba, da rashin haihuwar da ta dad’e bata yi ba. Da Allah ya jarabceka da haihuwa da yawa wadda babu amfani a cikinta, har k’ara Allah ya baka d’a d’aya tilo mai Albarka, domin zaka fi wadata da hakan.
Irin wad’annan tunanen masu kyawo, ke saka Hajiya Halima zama babba managarciya a rayuwarta, sannan k’ara mace take yi ta shiga part dinta taga abun k’i a ciki, don haka zaman aurenta da mijinta yake zama so ne na k’aunar farko, bai ta’ba yadda ya wulak’anta ta ba a gaban matanshi ba, kuma ko wacce zai aura, zai sanar da ita girma da darajar da matarshi ke da ita gareshi, don haka ko yaushe yake samun matsala da zuwairah.
Bayan andawo gida da kwana biyar, aka fara shirye-shiryen bikin suna, inda komai aka tsarashi ta yadda ya kamata. Mahaifiyar Alhaji baffa ta zo tun kwana ukku da haihuwa, hakan yasa Anwar ya biyota, duk da exam din da zasu fara, domin a lokacin yana j.s.s 2, amma dashi aka zo.
Duk wani kuri da za’ayi mishi da wane k’anenshi ne, shi sam! Baya gane yarensu, shi dai ganinsu yake yi, yayi dariya.
Anyi bukin suna an k’are, inda baby taci sunan mahaifiyarta Aisha, wadda aka sakama (Humairah), buki yayi buki, domin dangi sun hallara sosai.
Tunda Anwar yazo garin, baya cin abincin kowa sai na zuwairah, domin ko yaushe ita tana part d’inta bata zuwa ko ina, don haka yake ganin abincinta yafi na kowa tsafta. Kasancewar mahaifiyarshi bata nuna damuwar ita ta haifeshi, hakan yasa shima idan yazo bayan sun gaisa, sai yayi part d’in aunty zuwairah.
Ko ina Anwar yana shiga, amma yadda yake shiga part d’in Aunty zuwairah yafi yawa, domin nuna take yi, a duniya babu d’anda take so kamarshi, idan zai yi wani abu ma, ita yake fad’amawa, idan zai sayi wani abu a abuja idan yazo, ita yake fad’amawa ta bashi kud’i ya siya.
Ta hakan tayi nasarar chusa ma Anwar wata muguwar ak’ida, ta ko in kula da uwarshi da mahaifinshi, da kuma momyn Anwarah.
A irin wad’annan miyagun labaran da take bashi, harda labarin cewa, momyn Anwarah ta mallake mahaifinshi da mahaifiyarshi, da kuma hajiyar baffa, wanda ta nuna mishi cewa, baya ganin komai zasuyi sai da ita? Anwar yaro ne a lokacin, duk abinda wanda ke nuna mishi k’auna ta fad’a, zai aminta da zancenta, don haka sai ta dasa k’iyayyar Hajiya Aisha da Anwarah da Humairah a zuciyarshi, babu wadda ya yadda da ‘yar uwarshi ce a gidan sai Anisa.
Zuwairah ba haka kawai ta samu zuciyar Anwar ba, a cikin abincin da yake ci ne a wurinta, ta samu ta mallake shi, wanda hakan ya bawa kowa mamaki, ta rasa dama ne, sai ta komai hauni, ta rasa zuciyar tsohonshi ne, shiyasa ta biyo ta gefen Anwar d’in, inda tayi nasara anan.
Anwarah ko kad’an ba ta burin ta gamu da Anwar ko Anisa idan ta biyo hanyar part d’insu. Anwar daga hutu sai hutu yake zuwa garin, amma Anisa ko yaushe tana ganinta, duk da makarantarsu ba d’aya ba.
Anwarah school d’inda take yi, yaran manyan garin acen suke yi, kuma an sakata makarantar ne a dukiyar mahaifinta da mahaifiyarta wanda suka tara suka bar mata, ko ba haka nan ba, baffa da momy ba za su bari rayuwar Anwarah ta salwanta ba, domin Alk’awari suka d’auka na rik’eta amana da dukiyarta, wanda ita har yanzu bata ta’ba sanin ba sune iyayenta ba.