BAKI BIYU COMPLETE HAUSA MUSICNOVELS

BAKI BIYU COMPLETE HAUSA MUSIC

Da yawa Anisa na kira mata Marainiyya, amma ita kawai ta d’auka duka doguwar k’iyayace, wadda taga Aunty zuwairah na yi mata tun tana k’aramarta, har yanzu da ta kai secondry school. Inda Anwarah bata mayar da hankali da zancen nata shine, saboda k’iyayyar harda Humairah ciki, wanda a lokacin tana primary school ita humaira, shi kuma Anwar, a lokacin ne yake shirin fara shiga University anan Abujar, ita kuma Anisa anan Abuja take yin secondary nata, a wata makarantar da school piece nata, ko kud’in rabin term d’in school piece d’in Anwarah bata taka ba.

Anyi rigima da zuwairah akan wannan distance d’in da aka samu, inda take cewa, “idan Anwar da Humairah yaranka ne, to ita waccen marainiyya d’iyarka ce? Ko ko kai ne kayima uwarta ciki a bayan fage? Domin naga yadda kake son Anwarah, ko ‘ya’yan cikinka baka k’auna haka nan, don haka tunda har ban haihu da kai ba nima, wajibi ka saka Anisa irin school d’inda ka saka Anwarah, domin itama ai ba d’iyarka bace.”

Rana ta farko da aka ta’ba jifar Alhaji baffa da mugunyar kalma mara dad’i, wadda hakan sai da idonshi sukayi jawur, zuciyar fulanin asali ta motsa, wanda bai san lokacin da ya d’auki hannu ya mari zuwairah a fuska ba, marin da bai ta’ba yi ma wani shi ba, sannan ya bud’e baki a cikin fushi yace,

“Tabbas! Ina son Anwarah sosai a zuciyata, kuma ban ta’ba yi mata abu ba, banyima ‘ya’yana shi ba, k’arshe harda agolar d’iyar ‘yar uwar taki da kika kawo cikin gidan. Ina son kisan wani abu da kika manta anan, Anwarah bata jiran komai daga gareni, domin iyayenta sun barmata abinda zaya tayata rayuwa har k’arshen rayuwarta, sannan banda haka momyn tata kawai ta isa ta saka Anwarah duk inda take so, domin itama da nata arzik’in, wanda bata jiran ayi mata, sai dai tayi. Ki sani Anwarah ta wuce duk yadda kika sani, kin ‘bata mini rai wanda har ya sakani fad’a miki abinda banida niyyar infad’a, kuma da Anwarah da Anwar da humairah duka d’aya na d’auke su, don haka ki fahimci wani abun daga abinda na fad’a miki.”

Ko da ake yin rigimar a part d’in zuwairah, Anisa na tsaye a gefen k’ofar tana jin komai, wanda sai da tayi hawaye, jin motsin fitowar baffa d’in ya saka Anisa ‘boyewa, bayan wucewarshi Anisa ta fito ta fad’a d’akin inda taji Aunty Zuwairah na cewa,

“Lallai kuwa zaka ga Baki Biyu a rayuwarka, ni kayi ma Baki Biyu? Wallahi sai na nuna maka ni renon nufawa ce, yadda ta iya neman asirin da ya shafe nawa, haka zan dinga had’a mata masifa iri-iri a gidan nan, idan Baki biyu kayi mini, ni zanyi maka Baki hud’u banza a banza, muje zuwa dai.”

Anisa na tsaye tana kallon Auntyn ta-ta, wanda sai da ta zubar mata da hawaye, nan take ta rugo ta dafata da rik’ota tace,

“Aunty don Allah kiyi hak’uri, ki daina kuka.”

“Anisa ke nike so ki zama fansa ta, Anisa wajibi ki auri Anwar ta ko wace hanya ce, komai daran dad’ewar da zaiyi a inda yaje, burina ki zamo kece komai tashi, tare da taimakon abinda zanyi.”

“Auntyy…..!” Anisa ta kira sunan da k’arfi, ba tare da ta k’arasa maganar da ke bakinta ba, sannan ta kalli Auntyn nata tace,

“Amma Aunty ke kanki kinsan ina da wanda nike so, shine wanda ke sona tun ina k’aramata, a lokacin da Nuraddeen ya fara sona, ban cika mace ba, bare yanzu da na zama mace, kinsan burinshi d’aya a yanzu, na kammala karatuna next year muyi aure, kuma Aunty kinsan cewa, shine wanda nike so, ta yaya zan auri Yaya Anwar kuma?”

“Hmmm! Anisa wajibi ki sadaukar mini da wannan zuciyar taki, domin ta hanyar Anwar zamu kawo k’arshen zaluncin da shegiyar matar cen ta k’unsa, wanda kowa baya ganin girmanshi sai nata, kin san cewa Anwar ne kawai d’ansa, kuma idan ya rasu, Anwar ne magajin gidan, komai na mahaifinshi zai zamo hannunshi, to ta hakan zamu samu mu cika burin mu, Nuraddeen d’an uwa ne, zan san yadda zanyi dashi ya hak’ura da sonki.”

Hawaye suka fito a fuskar Anisa, wanda sai da suka d’igo a k’asa don bak’in fici tace,

“Aunty don Allah ki daina wannan shawarar, domin wallahi bani son Anwar, ban ta’ba kuma mafarkin aurenshi ba, hassali ma Anwar karatu zaije a dis year, sannan sai yayi shekaru biyu ya dawo, ni kuma mun shirya tsara aurenmu a next year da nayi graduate, a gidanshi zan k’arasa karatuna, kenan Aunty zan zamo mai Baki Biyu kenan a wurin Nuraddeen, sannan ‘yan uwa na, na gefen mahaifinmu, zasu zargi mahaifiyata da hana auren kamar yadda suke ganin ita ce ba ta so. Aunty mu changer wani tsarin don Allah, wallahi ni ko wane iri ne zan iya, amma ba na son rabuwa da yaya nuraddeen.”

“Na fad’a miki babu wata matsala, ni zanji da dukkan zuciyoyinsu, babu wanda zai kawo rikici a ciki, za’a juye zuciyar Nuraddeen d’in a kanki, sannan za’a juye ta masu magana, sannan za’a dasa soyayyar ki a zuciyar Anwar, burina ke dai kisan yadda zakiyi, zamu fara gabatar da aikin kafin Anwar d’in ya tafi.”

Anisa kamar zatayi magana, kuma sai tayi shiru, da hakan ta mik’e da tunane iri-iri a zuciyarta tayi d’akinta.

       ★★★

Bayan watanni goma.
A haka sukayita tafiya da rayuwar, Anwar ya na india k’arasa karatunshi, amma yanaji a zuciyarshi, kamar akwai soyayyar Anisa acikinta, tun lokacin da ta kawo mishi abinci a daren ranar da jirginsu zai tashi da safe, shigowarta part d’inshi na gidan ne, ya fara jin Anisa ta shiga ranshi, sannan ta mallaki abinda duk yake so a jikin mace, sai dai yasan cewa, tanada wanda take so, amma wajibi shima yabi sahu, domin yaga aburda yake so, kuma yasan Aunty zata yarda da shi akan kowa, mahaifinshi kuma, ai bayada matsala dashi, domin yasan zai bashi duk abinda yake so.

Tun da ya isa, yake ji a zuciyarshi babu kamar Anisa a rayuwarshi, domin irinta yake so, farar mace, ba mai jiki ba, kuma wadda bata da d’aukar kai, kowa ya kasance nata, sannan wadda bata son kwalliyar banza, a shafa powder, a shafa wani shegen abu, wai jan baki, baki kamar an dama dusa, kwalliya iri-iri na bashi haushi, saboda k’iyayyar lalle a rayuwarshi, idan mace tayi shi, ko mamarshi ce, baya iya cin abinda ta dafa da hannunshi.

ANWAR: a halin yanzu, shekarunshi 27 a duniya, sannan ya kasance shi fari tas! Kasancewar iyayen da suka haifeshi naki d’aya farare ne, saboda zamowarsu fulani na asali, totally dai Anwar mai kyaune ta ko wane ‘bangare ya gadi kyau, shi dogo ne ba irin sosai d’innan ba, haka kuma bai zamo gajere ba.

Anwar bayada d’aukar kai, amma kuma kowa bai dameshi ba, wannan d’aya daga cikin halayyar mahaifiyarshi kenan, saboda tsananin miskilancin shi, idan gaki gashi kuka had’u, idan baki yi mishi magana ba, ba zai kalleka ba kaima. Duk da irin wannan halin nashi, yana girmama matan Mahaifinshi, sai dai babu kamar Zuwairah da ta riga da ta siyeshi a sihiri. Anwar nada hak’uri a rayuwarshi, domin k’arya ne kace kaji yana fad’a da wani, amma idan aka k’ureshi zuciyar babu kyau.

Anwar na matuk’ar son iyayenshi, sai dai rashin zaman da mahaifiyarshi bata yi dashi tayi shawara dashi ke bashi haushi, don haka da sun gaisa zai bar part d’inta, yana son mahaifinshi, duk da juye mishi zuciya da akayi, duk abinda yace mushi yakanyi shi ne, ko da kuwa da Baki Biyu, ya faranta ma mahaifinshi rai, daga zuciyarshi kuma yaji zafin yi, domin ba haka yaso ba, amma idan yayi mishi addu’a zai ji dad’i. Sannan yana son kakarshi sosai, ita kam idan tace yayi, zai yi da Baki ‘Daya domin ita baya son yak’i yin abinda take so, saboda irin son da take yi mishi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button