BANBANCIN KABILANOVELS

BANBANCIN KABILA COMPLETE

BANBANCIN KABILA COMPLETE HAUSA NOVEL

 ```BAYAN SATI DAYA``` 

Su Olamide kawayan amarya, sai shiri suke, sun dau anko har sun kai dinki, sun raba invitation, sunata shiri, don next week Saturday kam In Sha Allahu Nabila zata zama amarya.
Kuma duk zuwan da suke gidan su Nabila, Olamide bata haduwa da Faeeq, hankalin ta ya kwanta sosai, ta sake sosai a gidan, duk Familyn su Nabila da suka zo, su Olamide sun shiga masu rai, especially Olamide. Wasu macewa suke wai karya take ba bayarbiya bace, wai bata da halin su, kuma bata kama da su. Amma ai kun san ta da baki, ta ce masu wato kowani yare nada kaman sa kenan, kuma ko wani yare na da halin sa, ai ita bata taba sani ba, abun data sani shi ne, Allah ya halince mu duka.
Hajiya Hajara ko sai nuna ta ma kowa take, wai yar ta ce, although ba ita ta haife ta ba, amma yar’ta ce, ita ce yayar Safina.

     ```WEEK DIN BIKI``` 

Kawayan amarya ansha lalle, itama amarya, ta sha gyare gyare, Hajiya Hajara da yan’uwan ta, sun gyara ta spiritually, physically, ta mentally, sai kyali ta ke, black skin din ta yayi kyau sosai, Nabila ta dawo kaman ba ita ba, tabi tayi kyau sosai.

Yau Friday, za’ayi kamu, yan matan amarya, sun sha makeup kala kala, da wanda nata yayi fitting din ta, da wanda nata baiyi fitting din ta ba. Nafisa ma ba’a barta a back ba, makeup artist da aka dauka, ta rangada mata makeup itama, tayi kyau sosai, inba kasan ta ba, baza ka gane ta ba. Olamide kuwa anyi anyi da ita a mata makeup, taki, wai su foundations, din da za’a sa mata, zai sa zafi ya kama ta, kuma ita baza ta iya juriyan safi ba. So powder, da wani nude colour lipstick ta sa. Itama tayi kyau daidai gwargwado. Sai shiri ake za’a kamu by 4:00pm.

〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️

A matsayin sa na aminin ango, tare suke zurga zurgan biki, suje nan suje can. Gidan da za’a sa amarya ma, sanda suka ga gidan was looking it best.
Abdallah ya kai makulli, lokacin da aka zo jere.
In suna tare da Farouk, ya ita tsokanan sa, sai kuma ya shiga land of dreams din sa, ace shi ne ma zai yi auran, daya ji dadi, sosai.

Ranan Friday da safe, suka tafi kano, da shi da ango, da sauran abokanan su. Suka sauka awani hotel, kafun lokaci yayi, su tafi venue din da za’ayi kamun.
Bayan asr, suma suka fara shiri, dakin ya dauka da kamshin turaren maza kala kala. Sunyi kyau sosai, abunka da fararen maza, amma still cikin su, ba’a rasa bakaken ba, suma sun sha kyau sosai.
Basu bar hotel din ba, sai 4 dot, suka kama hanya, suka je venue din event, nan suka samu, wasu kawayan sun zo, amarya da main girls din ta basu zo bako, amma within 5mins, suma suka iso. Suna isa, Nafisa ta fara fita daga cikin motan, tana wani kyali. Abdallah, ya kallie Farouk, ya ce “Guy baka fada mun amarya nada extraordinary beautiful friends haka ba. Just take a look at this one, although dai tayi makeup, kuma kasan I don’t go for madeup girls”. Yana cikin magan Olamide ta zura kafafun ta ahankali, ta fito. Ai anan bakin shi yayi full stop, yama kasa cewa komai, sanda Farouk yayi taping din shi sau uku, kafun ya ce ” subhanallah, which of the favors of your lord would you deny”.

“`Thanks for reading, please kuyi maneji.

      ~Zeexee ce~ ????️????️????️
[8/30, 1:21 PM] Abokiyar Fight????????: ????????????????????????
             ????
 *BANBANCIN KABILA* 
      _(Short story)_ 
????????????????????????
             ????

*TAMBARI WRITER'S ASSOCIATION*

*_????((Home of Expert and Talented writers,  da tambarinmu muke tafe domin kawo gyara da cigaban Al'umah))_*

    *T.W.A*

 *WRITTEN BY ZAYNAB* _(zeexee)_

MARUBUCIYAR

  *-RAYUWAR HUSNA* 

  *-MAHAKURCI MAWADACI (2020)*

Dedicating this page, to my Moza(Xulley sparks)???????????? and my abokiyar fada????????????????????????????????. I love you guys overdose????????????????.“`

1️⃣3️⃣&1️⃣4️⃣

“Which of the favors of your lord would you deny”. Abdallah ya fada.
“Non ya akhi”. Farouq ya fada.
“I can wait to see my Bila wallahi”. Farouq ya kara magana.
“Ni kam I have seen my qalbi, amma ya rage yanda zata zama nawa, don kasan heart dita ce, dole na samu yanda zan daidaita ta”. Abdallah ya fada yana rubbing din palms din sa.
“Gaskiya ne, daga ganin yarinya har ka fara maganganu”? Farouq ya tambaya.
“Dole na fara, saboda Allah’s creation is sooo beautiful, full of beautiful features. Just take a look at her, batayi wani makeup ba kaman sauran, amma tafi su. Kaga daa bahaushiya nake nama, amma Allah ya kawo mun bafulata a sawwake”. Abdallah ya fada.
“Toh Mallam ka dauke ido, only first look is halal. Gaskiya kam, kana da over assurance. Amma idan bai yuwu ba, sai mu fada ma Bila, sai ta taimaka ma rayuwar ka. Kuma to be sincerely speaking, ban taba ganin kana ma mace haka ba, but just looking at her made you this way, what if ta yarda, maybe you will loose a knot”. Farouq ya fada.
“Ai naga haka kaima kayi loosing din knot, kaga dole in bi sahu”. Abdallah ya fada da wasa.

Olamide ko, data fito daga cikin motan, ta gyara tsuwar ta, Nabila ta fito. Kai sunyi kyau sosai. Daman ankon Olamide da Nafisa, daban ne dana sauran kawayen, kuma style din su daya.
Da Nabila ta fito, Olamide ta ce dan gombe bai iso bane”?
“Ke baki gani ne, ga dan gombe can da wani handsome kusa da shi”. Nafisa ta Fada.

Su Abdallah na ganin fitowan Nabila, suka kara sa inda suke. Duk yanmatan da suka wuce, kallon su kawai suke, amma ina ango da abokin ango, anyi nisa.

Nafisa na ganin suna zuwa direction din su, tace “subhanallah, Bilatu, wannan shi ne wanda kika fada mana ko”?
“Ae shi ne, harkin fada a tarkon sa ne”? Nabila ta tambaya.
“A’a, ya mun haske da yawa. Nikam na bayan nan, daya ke bayan angon ki directly, ya shiga mun rai, ala dashi za’ayi wuf”. Nafisa ta fada tana dariya.
“Ohhh Asim! Ai shima Doc ne. Yawancin abokan yaya na, Doc ne”. Nabila ta fada.
“Habibty, yana ga kin yi shuru ne, ba zaki tofa naki ba”? Nafisa ta tambayi Olamide.
“Toh me zance, duk basu mun ba. Bana imagination akan abun da nasan da kyar ya zama gaskiya. Ai suna jin koni wata yare ce, zasu fara nuna mun tribalism, kuma kunsan bana taking shit. So in other to avoid that, gwanda na auri bayarbe ko dan Suleja, hankali na kwance”. Olamide ta fada.
Nafisa na son ta yi magana kenan, su Abdallah suka iso.

Da suka jeru, Olamide da Abdallah suka kasance side by side, Nafisa taso ace ita da Asim suna side by side, unfortunately, yana bayan wanda ke side din ta, kaman tace masa suyi exchange da Asim.

Da kowa ya samu wuri ya zauna, kawayan amarya suka zauna kusa da ita, akan stage. Ai ko Abdallah ya ita satan kallon mide, tun bata sani ba, har suka zo suna ido 4 har sau uku. Na hudu kuma, Mide ta harare shi, ta murguda mai baki, amma ko ajikin shi, instead ya ragu, sai kallon ya karu. She was feeling soo uncomfortable, sai tace ma Nafisa “Habibty, inaga zan tashi anan in koma inda jama’a suke, am feeling uncomfortable”. Olamide ta fada tana daure fuska.
“Kai habibty, haka bai dace ba, kinga mune manyan kawaye, ya kamata mu tsaya da ita, wallahi zata ji wani iri inta gan ki a can”. Nafisa ta fada.
“Ni kadai nasan abun dake damuna, amma I will be patient. But if I keep feeling this way, gaskiya zan bar wajan nan” Olamide ta fada fuska a daure.
“Ae, ki bari, zan maki coverup a lokacin, but for now ki zauna please”.
“Shikenan” Olamide ta amsa.

Bayan some mins, aka fito rawa, Olamide tayi gum kaman bata wajan. Amma Nafisa kuwa ana can Ana cashewa.

Abdallah ma yaki shiga wajan rawa, ya zauna kan kujeran sa kaman wani boss, yana ta dubawa ko zai ganta cikin masu rawa, amma yaga bata wajan, sai yaga Fisa ana cashewa. “Hmm, yarinyar nan akwai busy body. Although nasan na yaba mata, amma bata da natsuwa. Amma ga qalbi na, bata shigo cikin wannan hayaniyan ba, qalbi na natsasiya ce.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button