BANBANCIN KABILANOVELS

BANBANCIN KABILA COMPLETE

BANBANCIN KABILA COMPLETE HAUSA NOVEL

Su na cikin hira, Safina ta zo ta kira Nafisa da Olamide, wai ana kiran su aciki, sannan ta kare ma Abdallah kallo, sai ta ce “ba kai ne crush dina ba”? Ta tambaye shi.
“Ni kuma”? Shima ya tambaye ta.
“Ae kai”. Ta amsa tana murguda baki.
“A’a bani bane”. Abdallah ya fada.
Sai Olamide tace “Safina muje”.
“A’a aunty, bari na mai explaining ko zai gane”. Safina ta fada.
Kawai sai Olamide taja hannun ta, suka bar wajan. Ita kuma Fisa, ta dinga dariya, sanda Olamide ta harare ta, ta daina.

Da suka isa dakin, har zuhur yayi, kowa yayi sallah, Nabila ta sake wanka, aka chanza mata kaya, tasa atamfa Exclusive, wanda aka dinka shi da style mai kyau, ga kayan sun zauna ajikin ta, sunyi kyau, aka sake mata makeup, alokacin kuma anfara shiri, zaa akai amarya dakin ta a garin Gombe. Sanda aka gama mata, aka kai ta wajan manyan Familyn su, suka mata nasiha one by one. Nabila ta ci kuka, bari ma lokacin da Ummin su ke mata. Haka suka rungume juna suna kuka, ita ma Safina tayi joining din su. Shi ma Faeeq, yayi hugging din ta, kaman ba zai sake ta ba. Sanda Faeeq ya ma Farouq warning, kaman ma basu da alaka, daman shi Faeeq, ba ruwan shi, duk abun da yazo bakin sa yake fada.
Da zaa sa amarya a mota ma, sanda aka sha drama. Daman amarya da ango, da abokan sa guda biyu, da kawayen amarya biyu, ta jirgi zasu, sauran kuma su bi ta hanya.
Nabila kam ko da suka shiga jirgi, suka zauna, taga jirgin ya tashi, ta fara new version din kuka. Tana ganin fa jirgi ya tashi, tasan bye to kano, sai dai inta dawo, bayan two weeks kuma.
Olamide da Nafisa kuwa, suna can suna ta shirmen su. Suna ta ma juna dariya, wai first time din da zasu hau jirgi, iye, auran Nabila kam yayi favouring din su sosai.
Sai tabe tabe suke, suna dariya kadan kadan dan kar aji su.

Kafun kace me, har sun isa Gombe, suka fara sauka agidan iyayen ango. Daman wayanda zasu bi jirgi ba, sun riga sun fara tafiya, saboda su isa Kafin su Amarya.

Da aka gama komai, by 4:00pm, aka kai ta gidan ta. MashaAllah gidan yayi kyau Sosai, gaskiya Farouq yayi kokari sosai.
“Kai Nabila a gidan flower zaki zauna”. Nafisa ta fada yanda su uku kawai zasu ji, sai suka fashe da dariya, kallo kuma ya dawo kan su, sai suka yi shuru da suka ga yanayin kallon.
Cikin gidan ma shi ma mashaAllah kawai, dan gaskiya Ummi tayi ma Nabila kaya sosai ba kadan ba, ko ina yayi kyau, kayan suka yi rhyming da kalan gidan, so cikin gidan ma ya bada light sosai. Gidan three bedroom flat ne, da dan guestroom din sa a parlor. So da dare yayi, tunda familyn da suka rako ta, almost dukan su a Gombe suke, wayanda aure kuma ya kai su wani gari, suka je family house din su, nan suka kwana, yan gari kuma suka koma gidaje su. Su Olamide kuma, suka kwashi kafafuwan su sai guest room.

Da suka shiga room din, sun samu shima a gyare, komai yayi dai dai, yayi kyau. Kan gado su biyu suka fada, sai Olamide tace “wallahi your bed and pillow are among those things that give you comfort, without asking for anything in return”.
“Gaskiya kika fada habibty. Ko wani irin gajiya ka kwaso, toh bed and pillow will make you forget, by comforting you to sleep”. Nafisa ta fada.
“Am telling you. Kinga duk da cewa bed and pillow are comforting, shima wanka is comforting. So bari inyi wanka, in chanza into night wear, inba haka ba, I may wakeup sick, saboda and soo exhausted”. Olamide ta fada, tana mika, sannan ta tashi ta shiga toilet, tayi wanka, ta fito ta shafa mai, sannan ta sa nightyn ta. Ita ma Nafisa ta shiga wanka, ta zo ta shirya cikin nighty, basu ma wani tsaya hira ba, kowannan su tasa kai akan pillow, su kayi azkar, sai suka lula cikin duniyan barci.

Thanks for reading, and also been patient with me for not updating when I was meant to.

Comment
Like &
Share.

 ~Zeexee ce~ ????️????️????️

[8/30, 1:21 PM] Abokiyar Fight????????: ????????????????????????
????
BANBANCIN KABILA
(Short story)
????????????????????????
????

TAMBARI WRITER’S ASSOCIATION

????((Home of Expert and Talented writers, da tambarinmu muke tafe domin kawo gyara da cigaban Al’umah))

*T.W.A*

https://www.facebook.com/Tambari-writers-Association-106058867819812/

WRITTEN BY ZAYNAB (zeexee)

MARUBUCIYAR

-RAYUWAR HUSNA

-MAHAKURCI MAWADACI (2020)

```Dedicated to precious lady and Ummu Jannan❤❤❤❤❤❤. Comment din ku na nishadar dani????????????????????????????????????????❤❤❤❤❤❤❤, thanks so much.```

1️⃣9️⃣&2️⃣0️⃣

Shima Abdallah, suna gama duk abun da zasu yi, ya wuce gida, tunda dare yayi. Yaso yaje gidan Adda Fadi, dan suyi magana, amma lokaci ya wuce, ga shi ma agajiye yake.
Daya isa gida, suka gaisa da su Umna da Abba, Umma tace ga abinci nan a dinner, ya ce shi ya koshi. Wata zuciyar ta ba shi wai ya fada masu shi ya samu wace yake so, wani kuma yace a’a kar ya fada, wannan maganan na neman natsuwa ne, dole sai kowannan su na cikin farin ciki, kafun ya iya tunkaran su da wannan maganan, kuma ya fara fada ma Adda Fadi, tunda she is more closer to him, and she understands him better.
“Tunanin me kake ne auta na”? Abba ya tamyaye shi
“Bakomai abba na, na gaji ne kawai, ka san wannan harkan akwai gajiya”. Ya fada yana mika.
“Kai kam akwai randa ba zaka dawo kayi complain ba kuwa, gaskiya banga rannan ba, maybe nan gaba”. Umma ta fada tana jijjiga kai.
“Subhanallah! Abdallah ya fada yana dafa kai. “Wai ni ni kam Umma me yasa baki so na ne?
Kullum sai kin yi complain, kar ki damu, na kusan barin maku gida, ko kya huta da da complain”. Ya fada.
“Ai kuwa dana ji dadi sosai.
Amma in tambaye ka, har ka samu mata ne”? Umma ta tambaya, idon ta a kan sa.
“Kai Umma what do you mean, amma dai something like that, but it’s not settled yet, when it is, In Sha Allahu zaku ji”. Yana fadan haka, ya dau jakar sa, ya bar parlorn da sauri, gudun kar Umma ta kira shi da marasa kunya.
Yana barin wajan, Umma ta ce “ni kam me yaron nan ke nufi ne”? Ta fada tana kallon Abba.
“Oho, nima ban sani masa ba. Amma baya ce zamu ji ba in komai yayi settling, so have sabr my dear wife”.
“Okay I will, amma idan suspicion dina ya tabbata, I will be soo happy, saboda at least wannan tsohon ba zai kara maka maganan banza ba”. Ta fada tana huci.
“Bari kawai, ni zan ma fiki jin dadi. Kin san jiya ma dana je gaishe shi, sanda ya tada maganan, kinga irin kallon rainin daya ke mun ne, worst part din shi ne, dana je, na samu Wasila da mijin ta da yayan ta, wai sun je mai gaisuwan jumma’a. Wasilan da rabon ta da gida, almost one month, amma dana ce me tazo yi, Baffa yace wai sun zo gaisuwan jumma’a kaman yanda suka saba zuwa. Toh shiyasa kika ga jiyan nan sun biyo ni, saboda kunya”. Abba na fadan hakan, ya sake numfashi.
“Nima gaskiya na rasa wace iri ce Wasila. Tunda tayi aure, ta guje mu, kiran ma da Sudais, da Bilkisu da Fadila ke mun kullum safe, ita kam sai taga dama take kira na. Ta bi ta dauki mutumin nan tamkar mahaifin ta, mu kuma ta dauke mu tamkar iyayen goyon ta. Kuma bata son taga laifin sa sam, shiyasa bana ma wani shiga shirjin ta, saboda duk abun da akayi a gaban ta, sai tsohon nan yaji. Shi yasa ma mijin ta yafi ganin mahinmancin tsohon nan, akan mu”. Umma ta fada rai a bace.
“Ya muka iya, tagan mu talakawa, amma ta sani, acikin wannan gidan ta girma, ci da shan ta, da sutura, duk mu muke mata, bata taba ganin tsohon nan ya bamu kobo ba. Kuma ke kika dau cikin ta tsahon wata tara, kuma kika raine ta. Amma tun da rayuwar da tayi choosing kenan, Allah ya bada sa’a. Ai ni ban ma san suna baya na ba, dan dana ga yanda aka ita share ni, nima na tashi, na fita. Ban kai su kudi bane, amma ina da mutunci, bazan bari su raina ni ba. Ina fita na shiga mota, Idi yana ganin expression dina, ya san ba lafiya, shima ya ja mota, muka bar gidan. Ashe dana fita, sun biyo ni abaya, shiyasa kika ga mun shigo tare ai”. Abba ya fada.
“Hmmm, wallahi da bani na haife ta ba, dana cire hannu a cikin alamarin ta, amma yana iya, sai dai in ci gaba da mata addu’a. Ada ko Wasila ta fi su hankali duka, amma yanzu kam sai hamdallah”. Umma ta fada.
“Kaman yanda kika fada, mu ci gaba da mata addu’a kawai”.
“Ya muka iya, ai dole”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button