BANBANCIN KABILANOVELS

BANBANCIN KABILA COMPLETE

BANBANCIN KABILA COMPLETE HAUSA NOVEL

Da Abdallah ya bar parlorn, dakin sa ya tafi, nan ya watsa ruwa, ya fito ya sa PJ din sa, sannan ya kwanta kan gado, ya jawo wayar dake saman bedside drawer, yayi dailing din numbern Olamide, amma ya ita ringing, ba’a daga ba, ya kara kira, still ba’a daga ba. Sanda ya kira almost 7times still the same, sai ya mata sms, ya saurari reply almost 20mins, still ba reply, sai yayi concluding maybe tayi barci ne, gobe zata gani, Allah Yasa ta kira shi. Ya ajiye wayar, ya shige blanket, ya kwanta kan hannun daman shi, yayi azkar, ya shafa, aiko nanda nan barci ya dauke shi.

〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️

Cikin dare, alarm din Olamide ya fara kara, a tsorace, ta tashi, dan tama manta ta sa alarm, soboda irin gajiyan da suka yi. Tana tashi, taga alarm ne, tayi snoozing din shi, after 5mins, ya kara ringing, ta gaji sosai, amma it’s time for tahajjud, haka ta tashi, jiki ba kwari, ta dauki toothbrush din ta da toothpaste. Daman indai Olamide zata je hutu, ko a ina ne, sai taje da brush, toothpaste, da soson wanka, da kuma sabulu, shi yasa ma bata ma wani damu ta tambayi Nabila komai ba.
Tana daukan toothbrush din ta da toothpaste, ta shiga toilet din dake cikin guestroom, tayi business din ta, sannan tayi brush, kafun ta yi alwala, ta fito daga toilet. Data fita, taje ta side din da Nafisa ke kwance shame shame kanan wata gawa, ta fara tada ta, da kyar ta samu Nafisa ta tashi, kafun ta rike hannun ta, tayi leading din ta zuwa toilet, ta tura ta, sannan ta rufe kofar. Luckily akwai sallaya adakin, ta shinfida masu, ita ta fara sallah.
Acikin toilet kuwa, Nafisa nata faman zuba ruwa a fuskar ta, ko idanuwan ta zasu budu garau, amma ina, sai kara rufewa suke. Da kyar dai ta samu tayi alwala, ta fita a toilet, ta saka hijabi, itama ta fara sallah. Suna idarwa, ko wacen su ta dauki wayar ta ta bude Islam pro app, suka karanta alqur’ani, sannan su kayi addu’a safe da maraici. Suna gamawa, da kyar ma suka iya nannade sallayan da suka yi sallah akai. Sharp sharp suka hau kan gado, suka koma barci.

〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️

Cikin dare Abdallah ya tashi, yayi sallah, lokacin fajr yayi, ya samu Abba a parlor, suka hada hanya, suka tafi masjid tare.
Da suka dawo, yayi tillawa, yayi addu’an safe da maraici, sai ya kwanta, dan haryanzu gajiyan bai gama barin jikin shi ba.
Yana cikin barci by 9:00am Umma ta zo ta kwankwasa kofar sa, yana ji ana kwankwasa, amma yayi zaton ko yana mafarki ne, sanda yaji tas abaya, ya tashi arazane.
“Kai Umma, wai me yasa kika tsane ni ne haka?
Haba Umma na, wani laifi na maki ne”. Ya fada yana shafa bayan sa da ta dake shi.
“Toh ai kai din ne baka ji, kasan abun, amma kullum sai na tuna maka”. Ta fada tana jan kunne sa.
“Oush Umma, laifin me nayi kuma yau”? Ya fada yana kokarin cire hannun ta.
“Laifin rashin zuwa cin breakfast da wuri”. Tana fadan haka, ta sake mai kunne, ta kara cewa “ka tashi kazo ka ci abinci, ka san fa jiya baka ci dinner ba, and that is not good for your health at all”. Umma na gama magana, ta bar dakin.
Tana fita, shi ma ya tashi, ya shiga toilet, ya kuskure baki, ya wanke fuskan sa da ruwa, sannan ya goge da towel, kafun ya fita, ya wuce dinning, ya samu shi suke jira, ya samu wuri ya zauna, nan suka ci abinci tare.
Yana clearing din kwanonin da suka ci abinci da su, wayar sa ya fara ringing, sai ya ajiye kwanonin hannun sa da sauri, dan a tunanin shi, maybe Olamide ke kiran shi. Ya na ganin sunan Asim, yaja tsakin takaici, sai ya yi picking.
“Assalamu Akaikum”. Ya fada.
“Waalaikumus salaam. Nace kar dai ka manta yau zamu je gidan Farouq”. Asim ya fada.
“A’a ban manta ba, ai baku fada time ba”.
“Toh su Ahmad sun ce wai by 10, sai muyi kaman 30mins or less”. Asim ya fada.
“Toh hakan ma yayi, sai ku biyo mun, kun san nike kusa da hanyar gidan”.
“Shikenan, sai mun zo. DanAllah ka shirya da wuri, banda nawa”. Asim na fadan haka, ya kashe wayar.
Abdallah ko yayi murmushi, ya jijjiga kai, sannan ya ci gaba da aiki, yana tunanin dalilin da ya sa Olamin sa bata kira ba, Allah yasa dai lafiya. Kuma yau In Sha Allah, in suka bar gidan ango, gidan Adda Fadi zai fara zuwa, suyi magana, kafun ya koma ya dauke ta, su koma gidan Adda Fadi. Amma still Allah yasa Qalbin Abdallah na lafiya.

Duk abun da yake, hankalin sa bai kwanta ba, yanzu suna hanya ne, da shi da sauran abokanan sa zasu gidan Ango. Tunanin qalbin Abdallah yake, Allah yasa dai lafiya.

Su Olamide basu tashi ba, sai 9:30am, shi din ma saboda Nafisa tazo tada su, dan misalin 8:30 cip cip, aka kawo masu abinci daga gidan su Abdallah, sannan wasu cousin din ta through Ummi, sun zo, sun dan mata arranging din wasu abubuwan, da sharan inda aka bata jiya. Data ita jiran kawayen ta, taji shuru, shine taje duba su, ta ga barci suke, sanda ta jijjiga kan ta, tace "ragwaye kawai", tana fadan haka, ta zuba masu tafin hannun ta biyu a bayan su, a zabure suka tashi, ita kuma ta fashe da dariya. 

“Bani ya kamata ina barcin nan ba”? Nabila ta tambaye su tana daga gira.
“Dan Allah Bilatu ki kyale mu, wallahi ba zaki gane irin gajiyan da mukayi ba, gashi in muka koma gobe Monday, Tuesday zamu je school “. Nafisa ta fada tana mutsuka ido. Olamide ko sai hamma take.
Nabila na jin maganan Nafisa, ta zauna akan gado, ta ce “wallahi in nace maku ban ji dadin abubuwan da kuka mun ba, toh nayi karya. Kun yi kokari sosai akai na, kuma bani da abun da zan ce maku ko inyi maku inba godiya ba, nagode maku sosai, kuma nagode ma Allah daya hada ni da ku, Allah ya bar zumunci, ya bada lada, ya bar kauna, ya hada mu a aljannah, Allah ya kai mu ranan na ku ma, nagode nagode, nagode maku sosai, wallahi bazan iya paying din ku abun da …….” Basu bari ta gama magana ba, su kayi hugging din ta.
“Dan Allah godiyan ya isa haka, fisabilillah muka maki komai, so bamu bukatan godiyan ki ko habibty”? Olamide ta tambayi Nafisa.
“Haka kam”. Nafisa ta amsa.
“Bari in bar ku kuyi waka, abokanan yaya na zuwa, kuma su Nana ma sun zo. Kuyi wanka, zan aiko Nana da abincin ku”. Nabila ta fada, sai ta bar dakin.

Olamide ta fara shiga wanka, Nafisa ma tazo ta shiga. Suna cikin shiri, cousin din Nabila Nana, ta shigo masu da abinci, ta fara gaishe su, kafun ta ajiye masu abincin, ta juya.
Suna gama shiri, suka fara cikin breakfast, alokacin ma har 10 yayi. All this while, Olamide bata ma duba wayar ta ba, ita dai lokacin data bude wayar da asuba dan tayi amfani da Islam pro, taga notification din missed calls, da message, amma bata duba ba.
Sun gama cikin abinci kenan, suka fito rike da plates a hanu, suka samu Farouq da Nabila a parlor, da su Nana, Mufida, da Humaira, duk suna zaune, nan suka gaida Farouq, Nana da Humaira kuma suka karbi plates din a hannaye su. Ana karban plates a hannun su, Olamide ta juya, ta koma guestroom, ita kuma Nafisa, ta samu wuri, zata zauna kenan, taji muryar gardawa har 5 sunyi sallama, ta daga kai, suka hada ido da Asim, ai bata san lokacin data maida kan ta kasa ba. Su kuma suna shiga, su Nana suka gaishe su, su ka bar parlorn, suka koma guestroom. Nafisa tama rasa daga inda zata fara, sai ta bone Kawai, ta gaishe su, ta bar parlorn ita ma, ta wuce dakin da su Olamide suke, tana maida numfashi.
Olamide ta kare mata kallo, sannan tace “lafiya?”
“Ba lafiya, yanzu su Asim suka shigo”.
“Toh sai suka cije ki ko me?” Olamide ta tambaya.
“Ba zaki gane ba, I felt uncomfortable, I can’t wait for tomorrow morning, mu koma Kano”. Ta na fadan haka, itama ta zauna akan gado.
“Gaskiya me too, am feeling uncomfortable”. Olamide ta fada.
Nan suka fara hira, su Nana nata sa su dariya. Suna cikin hira notification ya shigo mata na new massage. Ta duba, sai taga Abdallah ne, alokacin ma taga ashe shi ya kira ta, kuma ya riga ya mata message da’a.
Sai ta karanta na jiyan, sannan ta karanta na yau. “Haba qalbi, har kin gaji dani ne? I know I can be a pest, at least reply, in san kina lafiya. Nasan kin san muna gidan nan, amma yanzu zamu wuce, kuma muna fita In Sha Allah, zan je gidan Adda Fadila, to tell her about our relationship like you requested. Although na san kin ce parents, amma I think I should tell her first, sai in kai ki kuga juna, amma ki fada ma habibty ma ta shirya, saboda tare zamu, kin san ba kyau ace opposite sex na tare without someone been with them, because shaidan is the third party there, kuma ba abun da bazai iya samu yi ba. I hope you will understand, waiting for Abdallah’s qalbi reply.”
Sai tayi murmushi, a cikin zuciyar ta tace “mashaAllah, I love his manners.”
Sai tamai reply, tace “Okay, we will be ready, and I will only inform my Mum about this relationship when I see your sisters reaction, and it will have to wait sai na koma school.” Tana tura massage din, ta kara murmushi.
“Murmushin me kike ne madam”? Nafisa ta tambaye ta.
“Mele. Ki shirya, zaki raka ni wani wuri, amma ba yanzu ba, sai ya kira ni”. Olamide ta fada.
“Baza ni inda ban sani ba, so gwanda ki fada mun”.
“Ko mu bar maku dakin ne”? Nana ta fada tana murmushi. Daman ita ce babban cikin su, bazata wuce 14yrs ba.
“A’a no need”Olamide ta fada tana hararan Nafisa.
“Aww ba zaki fada ba kenan, wato baki yi trusting dina ba kenan”. Nafisa ta fad rai abace.
“A’a ba haka bane, I trust you sosai wallahi. Kuma fa hmmm hmmm.” Olamide ta fada tana sosa kai, sai ta ce “ai dai kin gane shi, ya ce wai zamu je gidan addan sa”.
“Ni dai ban san hmmmm ba. Wace aciki?” Ta tambayi Olamide.
“Wai adda Fadila”.
“Toh Allah ya kai mu”. Nafisa ta fada.
“Amin”. Olamide ta amsa, sai Nabila ta bude kofan, tace “sun wuce, shima yaya ya fita. Kan nan sa zasu kawo mana lunch bada dadewa ba.
“Okay toh”. Olamide da Nafisa suka amsa tare.
Sanda suka bari ta zauna, Olamide ta ce
“Ammm Ore, anjima zamu fita.”
“Ina kuka sani a gari Gombe da zaku”? Nabila ta fada tana zare ido.
“Hmm, hmmmm, wai zamu je gaida Adda Fadila.” Olamide ta fada.
“Toh! Sunan Abdallah kika kasa fada?”
“Toh ai shi ne, nima hmmmm ta fada mun.”
“Toh Allah ya kwata. Allah ya kuma kai mu anjima.”
“Amin suka amsa.”
Suna cikin hira, text ya shigo Mata (Olamide) daga Abdallah, yayi replying.
“Ba damuwa qalbin Abdallah, sai yanzu na isa gidan ta, In Sha Allah, everything will be alright, ki jira sai na zo”.
Olamide na karanta Sms din, ta yi numfashi, acikin zuciyar ta tace “Allah yasa relationship din nan ya zo to past, saboda irin abubuwan nan da mutum zai ce sai yayi shawara da wani da dai sauran su, ke sa take loosing din masoyan ta, yanzu dai addu’an ta shi ne Adda Fadila kar ta nun banbanci tsatanin su, gashi ita ce best din sa, kar tazo tayi convincing din shi yazo ya dai na son ta.” Hmmm, taja numfashi, sai ta kwanta, tama manta su Nabila na daki, tayi lamo kaman marasa lafiya. Allah yasa dai komai yayi dai dai, kar Allah yasa dai karshen maganan ta kenan da shi, dan gaskiya ta fara son shi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button