BANBANCIN KABILANOVELS

BANBANCIN KABILA COMPLETE

BANBANCIN KABILA COMPLETE HAUSA NOVEL

“Kai gaskiya I really love her.” Nabila ta fada.
“Wallahi me too.” Nafisa ta fada.
“Ya isa, kar ku cinye mun ita da baki please.” Olamide ta fada.
“Mun ji.” Nabila ta fada
“Lokaci yayi fa, ki wuce dakin ki. Nafisa ta fada.
“Gaskiya kam, to 10 fa, ya kamata ki wuce dakin ki.” Olamide ta fada.
“Toh kora na kuke?” Ta tambaya kaman zata yi kuka.
“A’a, amma ya kamata ace kina tare da mijin ki, don’t forget you are now a married woman, and you have responsibilities to take care of, please you should go.” Olamide ta fada.
“Gaskiya kam, you have responsibilities, unlike us.” Nafisa ta fada.
“Toh naji, amma am really really going to miss you girls wallahi, you guys have become a big part of my life, thanks for always been there. Bari in wuce, kuma fa kuyi barci da wuri, kun san da sassafa zaku tafi.” Ta fada hawaye na zuba daga idon ta.
“Dan Allah kar ki sani kuka please, wallahi even we are going to miss our three musketeers circle wallahi. This is how life is, we go from stage to stage.” Olamide ta fada ita idanuwan ta suka cika da hawaye.
“A’a, please no crying, ke kuma Bilatu, ke kika ce kina so, da baki ce kina so ba da ba’a baki shi ba, so ki daina mana fake tears.” Sai kuma dukan su suka fara dariya.
“Gaskiya kam black queen, ke kika ce kina so, toh gashi an baki shi kuma kina kuka.” Olamide ta fada.
“Wallahi baku da dama, kunga bari in wuce, har 10.” Sai tayi hugging din su daya bayan daya, kafun ta masu sai da safe, ta fita a dakin, ta tafi nata.
Data fita, suna hira, suna gyara kayan su. Basu wani dau lokaci ba, suka kammala abun da suke yi, suka yi alwala, suka yi barci agajiye.

〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️

Kafun Abdallah ya koma gida, ya fara tsayawa a nearest masjid, yayi sallan magrib, kafun ya koma gida.
Daya isa gida, ya same iyayen sa a parlor kaman kullum, ya gaishe su, sai Abba yace “daga ina kake ne auta?”
Sai ya sosa kai yace “naje gidan fav ne.”
“Ka same su lafiya?” Abba ya tambaye shi.
“Lafiya kalau suke.”
“Toh mashaAllah.” Abba ya fada.
Sai ya Kalli umma, yace “umma na, yana ga kin yi shuru ne.”
“Bakomai.”
“Toh.” Ya fada, sannan ya zauna kusa da ita, ya rike hannun Umma, ya ce “Umma ta, am so happy today wallahi.”
“Toh mashaAllah, may Allah keep us happy always.”
Suka dan sha hira, kafun isha yayi, su Abdallah suka wuce masjid, ita kuma Umma, tayi a dakin ta.
Da suka dawo dinning suka tafi straight, Abdallah ya shiga kitchen, ya taimaka ma Umma, suka yi setting din dinning, kafun suma suka zauna, Umma tayi serving din su, suka ci abincin su silently. Da suka gama Abdallah ya kwashe kwanuka, ya kai kitchen, sannan suka koma parlor, suka fara wani sabon hira. Sanda Abdallah yaga sun yi nisa cikin hiran, yace ” Abba Umma, kun san me?”
“Ya zamu sani in baka fada mana ba?” Umma ta fada, shi ko Abba inba dariya ba, ba abun da yayi.
“Daman akwai wani aboki na ne, da muka gama secondary dashi, amma muna communicating, shi ne yau muka hadu, sai yace mun wai shi ya samu wacce yake so, amma matsalan wai bayarbiya ce, kuma family din su, suna iya barin mace ta auri koma waye, amma mazan su kam, daga fulani sai fulani, shi ne wai in ba shi shawara, ni kuma na rasa abun da zance masa.”
“Hmmm this is serious. Amma idan iyayen sa are very understanding, zasu iya bari. Amma in tambaye ka mana?” Abba ya fada.
“Toh Abba na.” Abdallah ya fada.
“Ya fada ma iyayen sa ne, kuma me suka ce?”
“Gaskiya kam, ya kamata ya bi umarnin iyayen sa.” Umma ta fada.
“Gaskiya bai fada masu ba, yana tsoron amsan su.”
“Ya dai fada masu, sai yaji opinion din su koba haka ba hajiya?” Abba ya tambaya ya na kallon Umma.
“Haka ne. Amma kuma yabi umarnin iyayen sa, dan a hakan zai samu nasara a rayuwa.” Umma ta fada.
“In Sha Allah zan fada masa, nagode.” Abdallah ya fada.
“Bakomai autan mu.” Abba ya fada, yana ja’a mai kumatu.”
“Awwsh Abba, zaka cire mun kumatun ai.” Abdallah ya fada a shagwabe.
“Sannu auta na, bazan kara ba, kaga daman babu kumatun, kar azo kuma ya cire, ana neman cuko.” Abba ya fada.
“Ko kai ka fada. Mutum siriri haka?
Dama ana iya kyautan kiba ne, dana ce yayyin ka su baka, duk da dai suma ba wani kiba gare su ba, amma sun fi ka, but still banda Fadila, dan itama gata ga irin ta.” Umma ta fada.
“Hahhhhhhhhhh, kai hajiya baki da dama. Wato dukan su ba auki, ai in kika duba, haka yan gidan mu suke, ko wannan fitinan nan tsohon nan ma haka yake, kaman a hure, amma fitinan shi, ya fi most fatest person kiba.” Abba ya fadi.
Abdallah da Umma suka fashe da dariya.
Haka suka ita hira. Sun dade suna hira, dan har 10:30pm suka kai.

Da Abdallah ya shiga dakin shi, yayi realising din time, yasan ko ya kira qalbin sa, ba zata daga ba, dan he is pretty sure tayi barci. Shi ma yayi shirin barci, ya yi azkar kafun yayi barci.
Asuba ta gari.

Thanks for reading, Allah ya bar kauna, zeexee ma na son ku.

Comment
Like &
Share.

Zeexee ce ????️????️????️

[8/30, 1:21 PM] Abokiyar Fight????????: ????????????????????????
????
BANBANCIN KABILA
(Short story)
????????????????????????
????

TAMBARI WRITER’S ASSOCIATION

????((Home of Expert and Talented writers, da tambarinmu muke tafe domin kawo gyara da cigaban Al’umah))

*T.W.A*

WRITTEN BY ZAYNAB (zeexee)

MARUBUCIYAR

-RAYUWAR HUSNA

-MAHAKURCI MAWADACI (2020)

Dedicating this page to sis Khadija (Hadiza). Nagode sosai da encouragement din ki, Allah ya bar dankon kauna????????????????????.

2️⃣3️⃣&2️⃣4️⃣

Da suka shiga, Afra ta ita rarraba ido tana kallon su, Adda fadi tace da ita “baki iya gaisuwa bane?”
Sai tace “ina ini”.
“Ina gajiya, ya kike?” Nafisa da Olamide suka fada tare.
“Lafiya kalau alhamdulilah”. Ta amsa.
Aunty Fadi tace ku zauna mana”. Ta fada tana murmushi.
Da Abdallah ya shigo, Afra taje wajan sa da gudu, tayi hugging din shi, tana fadan “oyoyo uncle’am”.
Shi kuma chewing gum din mummy, ya je ya boye a ta kafan Adda Fadi.
Abdallah ya daga Afra sama, tana ta dariya, sannan shima ya nemi wuri ya zauna. Ya ce “ni kam meye ruwa na da kai, kaje can ka karata da Mummyn ka”.
Adda Fadi tace “oho dai, my son ya fi ka kyau, ko Irfi?” Shi kuma ya kada kai.
Adda Fadi ta tashi, ta je kitchen, ta kawo masu chilled drinks da ruwa, da snacks, tasa masu a gaba.
Sai tace “banda pulako fa, ku fara taba wannan”.
Nafisa tace “toh”.
Abdallah yace da Afra, “kinga amaryar uncle and future mummyn ki In Sha Allah.”
“Wacce acikin su uncle?”
“Kiyi guessing, zan baki dairy milk”.
“Allah zaka bani dairy milk?” Ta tambaye shi excitedly.
“Uncle ya taba saba alkawar?”
“A’a. Bari in nuna maka ita toh.”
All this while, Olamide nata satan kallon su, tana son irin wannan relationship din su, bisa duka alamu, Ife(love) nada son yara, so he will make a good father In Sha Allah.
Tana cikin tunani, taji hannun Afra cikin nata, tace “ita ce wannan ko uncle?”
“Very good, saboda wannan task din da kika yi passing, zan siya maki packet din dairy milk.”
“Woo” ta fada exictedly.
Sai ta kalli Olamide da Nafisa, tace “kuna da kyau sosai kaman uncle dina”.
Kunya ya kama Olamide, Nafisa ko tace “ki dai fadi gaskiya, kice tana da kyau kaman Uncle din ki ” ta fada tana pointing din Olamide.
“A’a tana kama dani dai, ai nafi Uncle kyau, ko Uncle?” Ta fada tana kallon Abdallah.
Duk suka fashe da dariya. Shiko Irfan, ya bi ya makale da mummyn sa.
“Ku ci fa.” Adda Fadi ta fada tana pointing din abun da tasa masu agaba.
“Ai In law din ki akwai kunya.” Abdallah ya fada.
“A’a, kima cire kunyan nan, dan ba inda zaki in baki ci ba.”
“Zan ci.” Ta fada a kunyance.
Da kyar ta bude ruwan, ta sa a cup ta fara sha, Nafisa sai kallon ikon God take, ashe habibty nada irin kunya nan.
“Ya kuke ya school?” Adda Fadi ta tambaya.
“Alhamdulilah.” Suka amsa tare.
“Wallahi da ba dan bro yace mun ke bayarbiya ce ba ko, wallahi da fulani zan kira ki”.
Sai Olamide tayi murmushi, tace “haka ake cewa”.
“Gaskiya kam, dole afada. Amma ke kam fullo ce ko?” Ta tambayi Nafisa.
“Ae daga Bauchi.”
“Ashe ma bamu da nisa. Gaskiya in law, kin shiga mun rai sosai, am sure su Abba ma will be excited ta accept you In Sha Allah. Bari in kira maku Abban su Afra ku gaisa ko?”
“Toh” suka amsa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button