BANBANCIN KABILANOVELS

BANBANCIN KABILA COMPLETE

BANBANCIN KABILA COMPLETE HAUSA NOVEL

Su Abdallah na ganin iyayen su sun tashi, suma suka taso da gudu. Abdallah da hamma Sudais suka je wajan abba, ita kuma adda Fadi, ta je wajan umma.
“DanAllah abba kayi magana, wallahi ina son ta, kuma tana so na, gashi tana da hankali, kuma tana da tabi’a mai kyau. Ku bata chance, zaku ji dadin ta.” Abdallah ya fada.

“Wallahi umma tana da dabi’a. Ki bar ganin bayarbiya ce, tama fi wasu fulanin hankali. Wallahi umma zaki ji dadin ta, dan Allah ku ba soyayyan su chance dan Allah.” Adda fadi ta fada. Da umma ta wani harare ta, ta cire hannayen ta a jikin ta, ta ce “in kika gama, ki wuce gida, ki gaida mun namesake dina da Irfan.” Umma na gama magana, ta wuce dakin ta.

Shima abba, duk rokon da su Abdallah suke yi, sai shiga ya ke ta kunne dama, yana fita a na hagu, dan daman sun rike shi ne, sai ya balla hannayen su, cikin sukuni ya bar wajan. 

Zai bar parlorn kenan, Abdallah yace “kar ka manta, ku kuka ce kowa na samu, indai ta zauna mun, then you guys will support my decision.” Abdallah ya fada idonuwan sa jazur.

Abba bai ma bashi amsa ba, ya bar parlorn, ya wuce daki.

Su Umma na barin dakin, Abdallah ya tsuguna kasa, yaji jiri na daukan shi, ya dafa kai. Su Hamma Sudais da Adda Fadila suka zo kansa da gudu.
“Common be a man, kayi hakauri ka basu time. Kasan basu taba ganin irin haka ba a family, kai ne na farko, so they have to think, kafun su iya baka amsa.” Adda Fadila ta fada.
“Gaskiya kam, you should give them time, kaman yanda Fadila ta fada, ka kyale su for sometimes, In Sha Allahu everything will be alright, yanzu kam they are in shock.” Hamma Sudais ya fada.

Suna cikin lallaban shi, wayar sa ya fara ringing. Da kyar ya iya ciro wayan daga aljihun sa, ya duba screen, yaga sunan Adda Zaynab ya fito.
Da kyar ya iya daga kiran. Muryar sa kaman zai yi kuka, ya ce “assalamu alaikum adda!”
Adda Fadila ta mai signal ya sa a speaker, sai ya sa.
“Waalaikumus salaam mijin Faiza, amma ya naji muryar ka haka.”
Sanda Abdallah yayi nishi, sai yace ” Adda am not good at all, nothing went well. Gwanda Umma ma tayi magana, tayi objecting. Amma kin ga abba, bai ce komai ba, he just stood up and left.” Abdallah ya fada idanuwan sa cike da ruwa.
“Subhanallah! Ya za’ayi kenan?
Ina hamma da Fadila ma tukun?” Ta tambaya.
“Gamu.” Su biyu suka amsa.
“Me kuke yi da baku sa baki ba.” Adda Zaynab ta tambaya.
“Ban gane me muke ba, ke kin tambaye shi kuma yace maki bamu sa baki ba?” Hamma Sudais ya tambaye ta.
“Kayi hakuri Hamma, amma dai you all know it that I hate to see auta miserable, that why I said that. Amma toh yanzu ba abun da zamu iya yi ne?
Ko in masu magana ne?” Adda Zaynab ta fada disturbed.
“You should, ala in suka ga kema kin sa baki, maybe su yarda. Dan yanzu kam basu ma son su ga fuskokin mu, dan umma harta sallame ni.” Adda fadi ta fada.
“You should also try your luck.” Hamma ya fada, sai ya kalli Abdallah, yace ” we are with you, everything will be alright In Sha Allah.”
“Yes we are.” Adda Zee da Adda fadi suka fada.
“Nagode maku sosai, Allah ya saka maku, ya raya zuriya, ya hada mu duka a jannah.” Abdallah ya fada da jajjayen idanuwan sa.
“Amin amin autas.” Suka fada.

“Toh auta, anjima zan masu magana, kaga by that time maybe sun sauko.” Adda Zaynab ta fada.
“Toh. Allah yasa su ji naki.” Abdallah ya fada.
“Amin” yayyin sa suka amsa, adda Zee kuma tayi hanging up.

Su Hamma Sudais sun kai 30mins, suna kwantar ma Abdallah hankali, da kyar suka samu ya daidaita.

Da suka wuce, shima ya koma daki, ya hau kan gado, ya jingina da pillow, sai tunanin Olamide ya fado mai. Me zai ce mata yanzu in suna waya?
Inma ya fada mata, hanya bai zai yi loosing din ta ba?

Haka ya ita tunani, har lokacin sallah yayi, yayi sallah acikin dakin shi.

Daya idar, yana cikin addu’a, wayar sa ya fara ringing. Ya duba wanda ke kira, sai ya ga sunan Olamide (my qalbi) boldly akan screen, nan ya fara jin heart din sa na beating, yama rasa mai zai yi, ya daga ne ko ya bari.

〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️

Sanda Nafisa ta bari bayan 30mins, sai taje kusa da Olamide akan katifan ta, Olamide na ganin ta, ta juya fuska. Yanzu kam tama daina tunanin yanda iyayen Abdallah zasu yi reacting, haushin Nafisa take kawai, saboda ita baza ta iya fada mata haka ba, ko suggesting din shi baza ta yi ba.
Da Nafisa taga ta juya kai, sai ta juyar mata da kai tana kallon ta, tace “Allah sarki habibty, wallahi I care for you, I care about everything about you, bana son ganin hawayen ki. Kuma na fadi hakan ne saboda I really care about you. Kuma indai kin saurare ni da kyau, toh bance kuyi breakup ba, cewa nayi da baki son shi yanda kike son shi haka, dana ce maki kuyi breakup.”
“Toh naji ki, sai da safe.” Olamide ta fada, ta juyar da fuskan ta zuwa dayan gefen.
“Haba habibtyn Fisa, I really care about you, shi yasa kika ga na fada haka. Wallahi na tsani inga kina cikin damuwa, balle azo ga kuka, amma ina mai baki hakuri, kiyi hakuri da wannan stupid friend din naki, bazan kara ba.” Nafisa fada.
“Toh naji.” Olamide ta fada.
“Baki ce kin hakura ba.” Nafisa ta fada.
“Ban hakura ba.” Olamide ta fada.
“Haba habibty na, wallahi I care about you, kin ga idan kika ci gaba da haka, education din ki ma zai yi slacking. Bana son situation din da zaki dinga slacking a komai.” Nafisa ta fada.
“Toh naji na hakura, shikenan?” Olamide ta fada ta juya kai tana kallon ta.
“A’a, ina son ki hakuran gaske, ba irin wannan ba.” Nafisa ta fada a shgwabe.
“Wani irin hakuri ne yafi wannan, har ina amsa maki, toh na hakura, amma I don’t want to talk to you.” Olamide ta fada, ta tashi ta zauna.
“Haba habibty, so kike inyi ciwo, ya zaki ce kin hakura, amma baki son yin magana da ni, ki tuna fa I love you more than you can imagine, your happiness is my, and your sadness worries me too.” Nafisa ta fada kaman zata yi kuka.
“I know you love me, and I also love you too, you mean a lot to me, but you should have consoled me, bawai ki dinga bani irin advice din nan ba at that moment. Wallahi alokacin nan, comfort nake so, ina bukatan ki kwantar mun da hankali ne. Ko kin san idan iyayen sa basu yarda ba, hakan na iya zama sanadiyan rabuwan mu, so I need comfort, not that type of advice. You can advice me that any day, banzan yi fushi ba, but I was hurt when you deed it at that time.” Alokacin Olamide tana magana tana kuka.
“Ban san abun daya sa nake da saurin kuka ba, amma this is me.” Olamide ta kara fada.
Nafisa bata san lokacin da ta yi hugging din ta ba, ta ce “am very sorry habibty, bazan kara ba, I just said it, ban yi tunani ba, danAllah kiyi hakuri.” Nafisa ta fada.
“Nayi, amma Fisa na dauke ki as sister ta, ko kin mun laifi, bana iya fushi dake.” Olamide ta fada.
“Am very sorry, banzan kara ba.” Nafisa ta fada.

Da suka gama koke koken su, su dan yi hira, Nafisa ta ita kwantar mata hankali, su kayi barci.

Da suka tashi da safe, suka yi dutyn su, suna ta hira, ranan ya kasance Saturday, gashi basu da lectures, so suna ta huta duka gajiyan da suka yi tun monday. Ana cikin haka, Abdallah ya kira ta, ya sanar mata da cewa bayan asr zasu fada masu Abba, tun lokacin mood din ta ya canza, amma tana ta kokarin danne shi, not to make anyone around her worried.

Around 3 data ji shuru,  sai Nafisa ta bata advice wai ta kira shi, da tana ta contemplating. Sai bayan sallan asr ta yi concluding kawai ta kira shi, kawai ta kira shi.

〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️

Sanda wayan ya kusan tsinkewa, ya daga.
Daya daga bai yi magana ba, sanda ta ita sallama, kafun ya yi clearing din muryar sa kafun ya amsa.
“Baka amsa mun ba tun dazu ina ta salama.” Olamide ta fada.
“Kiyi hakuri, yanzu na tashi daga barci shi yasa.” Abdallah ya fada.
Allah ya ga baya son yin karya, amma ya ya iya, ba zai iya fada mata abun daya faru ba.
“Toh yayi, shi ne ka bar ni da damuwa ko?” Ta tambaye shi.
“Kiyi hakuri, su adda could not make it, shi yasa muka chanza timing din, sai duk ran da they are free again.” Abdallah ya fada.
“And you didn’t bother telling me. Kasan yanda na damu kuwa?
Gashi instead ace muna progressing, sai baya mu ke zuwa. Gaskiya ni bazan iya irin relationship din nan ba, our parents need to know about us. But if you don’t want that, we can call it a quit.” Olamide ta fada, sannan ta kashe wayar.
She was soo frustrated, ta rasa abun da yasa Abdallah yake mata haka. Shi ya sata agaba, sanda ta sanar ma mummy, amma ya sanar ma iyayen sa ya zama matsala.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button