BANBANCIN KABILANOVELS

BANBANCIN KABILA COMPLETE

BANBANCIN KABILA COMPLETE HAUSA NOVEL

Shi kuma Abdallah, data kashe wayar, ya rasa yanda zai yi da rayuwar sa, the pressure is too much, ya rasa abun yi, ji yake kaman ma ace he is not Abdallah any more.

Thanks for reading

Comment
Like &
Share.

~Zeexee ce~ ????️????️????️
[8/30, 1:21 PM] Abokiyar Fight????????: ????????????????????????
????
BANBANCIN KABILA
(Short story)
????????????????????????
????

TAMBARI WRITER’S ASSOCIATION

????((Home of Expert and Talented writers, da tambarinmu muke tafe domin kawo gyara da cigaban Al’umah))

*T.W.A*

WRITTEN BY ZAYNAB (zeexee)

MARUBUCIYAR

-RAYUWAR HUSNA

-MAHAKURCI MAWADACI (2020)

3️⃣7️⃣&3️⃣8️⃣

Bismillah

Da su umma suka shiga ciki, Umma tace "wai ni alhaji me ke damun yaran nan ne in aka zo zancen aure?" 

“Ai kuma ba ni zaki tambaya ba Hajiya, su zaki tambaya. Ina ganin sakewan dana masu ne yayi yawa.” Abba ya fada rai abace.
“Gaskiya kam, sai ko wannan su zai yi aure ake meeting akan mu kullum.” Umma ta fada.
“Hmmm bama wannan ba. Kin san me Abdallah ya fada?” Abba ya tambayi umma.
“A’a alhaji.” Umma ta amsa.
“Kin tuna ran da na dawo nace baffa Dajjo ya mun maganan auren shi, kuma muka ce mai koma waya ya auro, in dai ta mai?” Ya tambaye ta.
“Haqqun na tuna. Kar dai shiyasa ya nemo mana bayarbiya. Yarbawan da basu da tarbiyan?”
“Shi nake gani nima ai, saboda da na kusan fita a parlor, yake cewa ai mun ce ya auri koma waye, indai ta zauna mai.” Abba ya fada yayi tsaki.
“Toh shine yaje ya samo bayarbiya, yarbawan da kowa ya san halin su?
Be ma nemi yar arewa ba, yar kudu ya nemo.” Umma ta fada takaici na kama ta.
“Ai shi ne. Ni fa when we said that, I only thought about someone from arewa, me zamu yi da yar kudu?” Abba ya fada ya dafa kai.
“Ai shi ne na gani. Me ma ya kai tunanin sa zuwa nan?” Umma ta fada.
“Oho masa.” Abba ya fada.
“Ni kam gaskiya bazan yarda ba, saboda gaskiya yanda mutum ke jin labarin yarbawa, they are not people we can live with.” Umma ta fada.
“Gaskiya they are not people to live with.” Abba ya fada yana kada kai.
“At all. Kuma kar mu yarda gaskiya alhaji, saboda ban zan yarda ace mu zama abun zagi a gari ba.” Umma ta fada.
“Ai baza mu yarda ba, ya ma san inda dare ya ma sa.” Abba ya Fada.
“Ai kuwa.” Umma ta fada.

Haka su Abba da Umma suka ita maganganu.

Abdallah ya kara kiran Olamide, bata daga ba, ya kira ta yafi sau bakwai amma ta ki dauka, sai ya kira Nafisa. Olamide ta tambaye ta ko shi ne, ta ce ae, Olamide tace mata kar ta daga. Har sau uku ya kira ta, itama bata daga ba.
Although ta so dagawa, amma Olamide ta ki, tace kar ta daga, inba haka ba zasu yi fada. Ita kuma gudun kar kawar ta tayi fushi, ta ki dagawa, amma ta kuddura a ran ta, anjima zata kira shi.

Rashin dagawan da suka yi, ya tada ma sa da hankali sosai, yaji ba abun da ke mai dadi. He felt so heart broken, ya rasa inda zai sa kan sa. Olamiden da ta kamata ta kwantar masa da hankali, ita ma tana fushi da shi.

Aranan kam Abdallah ya rasa yanda zai yi da kan sa, dan su abba ma sun ki kula shi. Inma ya masu magana ba kula shi suke ba. Abun duniya duk yabi ya ishe shi, ji yake kaman ya je tsakiyan compound din gidan su, ya dinga ihu, ko zai dan ji relief.

Bayan isha ya kira adda Fadila, yayi ringing sau uku, ta daga.
“Assalamu alaikum auta.”
“Waalaikumus salaam. Wallahi tunda abun yau ya faru kuka koma gidajan ku ko, ke kadai kika mun magana normal. Ko qalbin Abdallah ma fushi take dani.” Abdallah ya fada sadly.
“Don’t be sad brother, your fav sis na tare da kai in every situation. Ka fada ma qalbin ka abun daya faru ne?
Indai ka fada ne, toh baka kyauta ba kwata kwata.” Adda Fadi ta fada.
“No, ban fada mata ba, yama zan fada mata irin wannan abun, ita da tsoron ta kenan, shi yasa tace na fada masu, mu san inda muka dosa.” Ya fada weakly.
“Kai ! Subhanallah, this is not good at all, gwanda ma da baka fada mata ba. Gashi tsoron ta yazo true, kuma am pretty sure in ta sani, maybe tace kuyi breakup. Kuma wallahi ba zan ga laifin ta ba, what is the need of staying in a relationship din da yan uwan guy din basu son ki. Amma yayi kyau da baka fada mata ba, maybe su zo su yarda in adda Zee ta masu magana.
“Toh Allah yasa su yarda, saboda da ta kira ni, ta tambaya ko na fada masu Abba, sai na mata karya nace a’a, shi ne fa tayi fushi, wai ni na takura mata, har sanda ta fada ma mahaifiyar ta, amma ni in fada ma su Umma ya zama matsala. Wai ina mata wasa da hankali.” Abdallah ya fada.
“Allah sarki, ta matsu ne ta san level din relationship din ku, if it’s going to make a progress or not. Amma it’s still good da baka fada mata ba, muma sai muyi kokarin ganin su abba sun yarda, saboda gaskiya ni kam ina son ta, bazan iya jure rashin ka da ita ba, wallahi ta gama tafiya da zuciya na.” Adda Fadila ta fada.
“Da zuciyar ki ko nawa. Ai irin soyayyan da nake ma qalbi, in su abba suka hana ni ita na auri wata, toh ko min son da nake mata ba zai taba kai na qalbi na ba, saboda she owns my heart.” Abdallah ya fada.
“Allah sarki kani na, kar ka damu, komai zai yi daidai, ka kwantar da hankalin ka, saboda Olamide taka ce In Sha Allah.” Adda Fadila ta fada.
“Amin, nagode sosai da support din ku, Allah ya bar mun ku.” Abdallah ya fada.
“Amin amin.” Adda Fadi ta fada.
“Toh mu kwana lafiya, bari in kira qalbi na.” Abdallah ya fada.
“Toh, agaishe ta, mun ma dade bamu yi waya ba, maybe in kira ta gobe.” Adda Fadi ta fada.
“Okay. Dan Allah in kun yi waya, ki kara kwantar mata da hankali please, kice mata ta daina damuwa, very thing will be alright In Sha Allahu.” Abdallah ya fada.
“Toh naji, amma in kun yi waya, kai ma ka kwantar mata da hankali.”
“In Sha Allah. Bye.” Abdallah ya fada.
“Allah ya tashe mu lafiya, bye.” Adda Fadila ta fada, sai ta kashe wayar.

Da suka gama waya, sai ya nemo sunan qalbin sa, yana gani, zuciyar sa ya fara tsinkewa, Allah yasa dai ta daga. Yayi dialing din numbern, ya ita ringing baa daga ba, Olamide ta gani, ta ki dagawa, sanda ya kira sau uku, Nafisa tayi forcing din ta ta daga. Rai abace ta daga, tayi sallama.
“Waalaikumus salaam qalbin na.” Abdallah ya amsa sallaman ta.
Sai kuma shuru ya biyo baya, ba wanda yayi magana acikin su, da abun ya ishi Mide, tace “daman ka kira ni ne kawai, ba dan kayi magana da ni ba ko?
Toh na gode, bari in kashe…..” Bai bari ta gama magana ba, ya ce ” ba haka bane qalbi, wallahi I just became speechless ne, amma am sorry for the silence.” Abdallah ya fada.
“Toh. Ina jin ka.” Olamide ta fada without emotion.
“Daman na kira ne in baki hakuri qalbi na.” Abdallah fada.
“Hmm ifemi kenan, lokacin da zan fada ma mummy, ka sani a gaba, in dai fada. Amma ka fada masu abba ya gagara. Toh me kake son inyi, dole nayi fushi ai. Ni wallahi gani nake kaman kana wasa da hankali na ne kawai.” Olamide ta fada.
“Haba qalbi, me zai sa inyi wasa da hankalin ki, you are too specially in maki haka.” Abdallah ya fada.
“Am not! Because if I was ba zaka dinga mun haka ba. Kullum sai kace you love me, amma you are finding it hard ka fada ma su abba mu san inda muka dosa. Bana son situation din da zan zo in sake da yawa, su zo su ce basu son ka auri kabila.” Olamide ta fada.
“Kar ki damu masoyiya ta, hakan ba zai faru ba, ina son ki kara hakuri, nida siblings dina mun na plan ne akan yanda zamu fada masu da baza’a samu damuwa ba.” Abdallah ya fada.
“Ni kam ban yarda ba, gani nake kaman kana wasa da hankali na ne kawai. Amma ba damuwa, I will be patient, but you should know, next time ba zan ji komai ba, we will just find our ways kawai.” Olamide ta fada.
“Hakan ma bazai taba faruwa ba In Sha Allah. Ki kwantar da hankalin ki please, saboda kwanciyan hankalin ki shi ne nawa.” Abdallah ya fada.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button