
Ita kuma Nafisa, tama rasa abun fada, saboda Olamide bata fahimce ta ba.
〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️
Da Abdallah ya tashi, yayi routine din sa, yau din sai yaji duka jikin sa a mace, yana jin wani iri, Allah yasa yayi nasara, Allah yasa su Umma su yarda.
Banyan zuhur suka ce zasu zo (hamma Sudais da adda Fadila), so ana idar da sallah, da suka dawo daga masjid da abba ya ji hankalin sa ya kara tashi, kawai ya yanke hunkuncin instead ya dinga tada hankalin sa, why not ya ita addu’a saboda du’a is the sword of every muslim, and with Allah everything will be alright.
Da su hamma suka zo, sun samu umma da abba da Abdallah zaune a parlor.
Da suka zauna, adda Fadila ta je ta kawo masu drinks ita da hamma, suka sha. Sanda suka bari sun yi nisa sosai da hira, kafun hamma Sudais yace ” Abba, Umma, kuma kun san wannan zuwan mu kam da dalili, saboda jiya muka zo, kuma ace gamu kuma yau.”
“Tabbas, ina son ma in tambaye ku ne.” Abba ya fada.
” Abdallah ne yake da magana da ku, amma our presence is needed.” Hamma ya kara fada.
“Toh kai Abdallah, me kake son ka fada mana ne da har sai yayyin ka sun zo?” Umma ta fada
“Daman, daman akwai. Abdallah ya kasa ci gaba da magana.
“Kayi magana mana?” Umma ta fada.
“Na samu wace ……….”
Thanks for reading, please kuyi maneji.
Comment
Like &
Share.
~Zeexee ce~ ????️????️????️
[8/30, 1:21 PM] Abokiyar Fight????????: ????????????????????????
????
BANBANCIN KABILA
(Short story)
????????????????????????
????
TAMBARI WRITER’S ASSOCIATION
????((Home of Expert and Talented writers, da tambarinmu muke tafe domin kawo gyara da cigaban Al’umah))
*T.W.A*
WRITTEN BY ZAYNAB (zeexee)
MARUBUCIYAR
-RAYUWAR HUSNA
-MAHAKURCI MAWADACI (2020)
3️⃣9️⃣&4️⃣0️⃣
Bismillah
*BAYAN WATA DAYA*
“Baza mu yarda ba and that is final.”
“Abba dan Allah, am begging you guys please.”
“Wai kai wani baza mu yardan ne baka gane ba?”
“Dan Allah umma kar ku mun haka, one month kenan fa ina rokon ku, dan Allah, kuyi ma Allah da manzon sa ku yarda, wallahi Olamide is not like that, kuma yanda kuke cewa yarbawa basu da dabi’a haka ma wasu fulanin.” Abdallah ya fada da hawaye a idon sa.
“Toh masani fada mana, ka san ni da Abban ku bamu san komai ba.” Umma ta fada.
“Wallahi umma ba haka bane, am just trying to make you guys understand that’s why. Dan Allah ku yafe mun indai magana na ya bata maku rai, amma dan Allah ku yarda da ni, wallahi bazan yi disappointing din ku ba.” Abdallah ya fada.
“Ka tashi ka fita kafun rai na ya kara baci inyi abun da dukan mu zamu yi regretting.” Abba ya fada rai abace.
Jiki a sanye Abdallah ya mike daga inda ya tsuguna, ya fita a dakin, hawaye na zuba shar shar a idon sa.
Yana fita Abba ya ja wani irin tsakin da har Umma ta firgita.
“DanAllah ka yi hakuri Alhaji, na rasa me yar yarbawan nan ta mai. Ala ma asiri ta mai, ka san yarbawa da asiri.” Umma ta fada.
“A’a Hajiya, kar ki fadi abun da baki sani ba. Ina jin zan neman mai yar aboki na ne kawai. Bana son auren hadi, amma he has left me with no choice.” Abba ya fada.
“Am in support, indai bai daddara ba, kawai ka neman mai wata acikin yaran aboka, zai fi mana da ya kawo mana yarinya marasa tarbiya.” Umma ta fada.
“That is what I will do kawai.” Abba ya fada.
Shi kuma Abdallah, daya shiga dakin sa, ya rufe kofan. Although ya kamata ace yana shirin zuwa aiki ne yanzu, but he has no energy for that, so sai ya ki Farouq, yace ya mai reporting cewa baya jin dadi. Ya zauna akan gadon sa, ya fara kuka, me yasa hakan ke faruwa da shi ne?
Ba Allah ya hallice mu duka ba?
Toh me yasa mutani ke haka ne?
Me yasa mutani basu son yaran su na auran kabila ne haka?
Haka ya ita tunani, yana hawaye. Daya ga hawayen sa baza su chanza komai ba, sai ya tashi ya shiga toilet, yayi alwala, ya fara nafl.
Daya idar, ya fara tunanin abun da zai fada ma Olamide in sun yi waya. Gashi yau yace mata zai ma su Umma magana, and to make matters worst, tace this is the last time, saboda for one month yanzu ce mata yake bai samu time din fada masu ba, aiki ya mai yawa.
Gaskiya he doesn’t want to loss her, ya zai yi yanzu.
Yana cikin tunani wani idea ya shigo mai, maybe ya fada mata, amma ba zai fada mata everything ba, kawai dai zai fada mata sun ce zasu yi tuni akai, saboda ta san first time din su kenan.
〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️
〰️〰️〰️〰️
“Habibty ki yi sauri fa, time is not by our side.” Nafisa ta fada.
“Toh naji, bag dina kawai zan dauka.”
“Oho ni dai kiyi sauri, su Hafsah ma na jiran mu.” Nafisa ta kara fada.
Baa fi 3mins ba, Olamide ta fito. “Toh gani uwar masifa.”
“Wani masifa ta maki, so kike muyi laty ko?” Halima ta fada tana daga mata gira.
“Ya isa dan Allah, ku din ma da kuke magana zaku samu latty.” Hafsa ta fada.
Suka kama hanya suka fita, suka nemi keke, ya kai su har school.
Yau been the last paper din su na semester, kuma ya kasance papern da safe ne, yasa suke ta sauri, ga zumudin zasu koma gida.
Suna isa school, suka tafi inda zasu rubuta exams, suka samu ma har anfara shiga, suma suka yi joining din queue, nan Nabila ma ta zo ta same su, itama tayi joining din queue.
“Wow! Today’s exams was superb wallahi.” Nabila ta fada tana hugging din Oamide.
“Yes it was.” Olamide ta fada moodly.
“Habibty yana ga reply din ki bai zauna mun ba, ko exams din bai maki honey bane?” Nafisa ta tambaye ta.
“Bakomai, yayi dadi sosai kaman taliya da manja da yaji.” Ta fada tana faking din murmushi.
Ita Nafisa ta san ba lafiya, amma sai ta share, ta kudura a ran ta in suka koma gida zata tambaye ta, tunda su gobe zasu koma ba yau ba.
Suka taka zuwa inda ake samun keke, Olamide ta ce ” Bila yau zaki koma ko?”
“Ae In Sha Allahu. Yaya yace kar in kwana, in dawo yau tunda papern safe ne. Ko akwai sakon da zaki bani ne na ba.” Nabila ta fada tana kashe mata ido.
Nafisa kuma ta fashe da dariya, tace “gaskiya kam, ko akwai message for ife ne.”
“Kar kiyi coverup da ita, in kema kina da sako ne, ki bada atoh.” Nabila ta fada.
“Ai shi ne. Wallahi ko Bila, habibty is too secretive with her relationship, ko tana da shi baza ta fada ba.” Olamide ta fada tana hararan Nafisa da wasa.
“Zan fasa maki ido fa.” Nafisa ta fada ta buga ma Olamide ido da wasa.
“kan balai, zan karya ki fa idan kika kara taba mun ido na.” Olamide ta fada.
“Ya ishe ku. Ku daina wasan manya please.” Nabila ta fada.
“Wallahi nayi zaton wasan yara zaki ce, dana fasa maki mouth.” Nafisa ta fada.
“Ki fasa ma Farouq baki, sai dai ki gan shi a nan.” Olamide ta fada.
“Ko kunya, ki kira sunan miji na gatse haka?” Nabila ta fada.
Inda su biyu ke arguing, Nafisa ta tsare keke, duk basu sani ba, suna can suna arguing, harta shirya da me keken. Da ta gama shiryawa da mai keken, ta daka masu tsawa. “DanAllah ni ku daina wannan abun kuzo mu tafi.”
“Kai har kin tare keke?” Olamide ta tambaya.
“In muka shiga zaki tabbata koma meye.” Nafisa ta fada.
Da suka isa gida, suka dan huta, Nafisa ta sa masu abinci a wuta, ita kuma Olamide ta cigaba da shirya kayan ta.
Although da Nafisa ta tambaye abun da ke damun ta, ta ce bakomai, ta fara wasa so that zata yi covering up, deep down she was feeling anxious, kuma her anxiety akan abun da Abdallah yace zai fada ma iyayen sa ne. For a month yanzu yana ta mata yawo da hankali, and within these one month, soyayyan sa ta kara karfi a zuciyar ta. Amma tana tsoro, kar azo yanzu ace ba zai aure ta ba, gashi ta gama fadawa cikin tarkon kaunan sa.
Tana aiki tana tunani. Hanya zata taba samun Abdallah a matsayin mijin ta kuwa?
Ita kam bata jin shi ajikin ta cewan zai zama mijin ta, kullum ji take kaman they only have a little time left before they part ways.
Tana cikin tunanin, taji wani abu mai sanyi a jikin ta. A zabure ta ce “subhanallah!”
“Matsoraciya. Ni ce toh.” Nafisa ta fada.
“Kin tsorata ni fa sosai. Me yasa hannun ki yayi sanyi haka ne?”
“Oho mai. Tunanin me ma kike hakan, na kira sunan ki fa almost sau biyar, amma baki amsa ba.” Nafisa ta fada.
“Bakomai, just normal thinking ne.”
“I see, continue normal thinking. Amma kafun ki ci gaba, mu ci abinci, saboda ni kam yunwa nake ji.” Nafisa ta fada.
“Nima haka.”