
Lokacin da suke cin abinci, tana ta dannewa, gudun kar Nafisa ta gane. Saboda gaskiya hankalin ta yaki kwanciya kwata kwata.
Da suka gama ci, Olamide ta dauki plates, ta kai kitchen, ta wanke su. Tana ta expecting wayan ta yayi ringing, amma shuru kake ji. Tana wanke wanke, tana duba wayar ta. Wata zuciyar ta ce maybe ya tafi office ne, tunda yau is a working day. Amma yace zai fada masu da safe, maybe bai samu fada ba.
“Wai ni habibty me ke damun ki ne?” Nafisa ta fada.
“Bakomai.” Olamide ta fada, sannan ta ci gaba da wanken wanken ta.
“Ki daina mun karya please. Tun dazu nake nan fa, amma sai tunani kike.” Nafisa ta fada.
“Bakomai fa, am just thinking of how hutun nan will be without you my habibty.” Olamide ta fada.
“Kar ki maida ni karaman yarinya fa, I don’t wear pampers anymore please. If you don’t want to tell me kawai ki fada mun, but ki daina mun wasa da hankali.” Nafisa ta fada.
“Allah sarki my habibty, kar kiyi fushi da ni. Wallahi na gaji da maki complain akan abu daya ne. Ni ke nan kullum cikin yi maki complain akan relationship dina, amma ko sau daya baki taba mun complain ba.” Olamide ta fada.
“Gama wanke wanke, bari in je in ci gaba da gyara kaya na, na san by the time din da zamu gama komai, lokacin zuhur yayi. Kin ga bayan zuhur, sai mu samu muyi maganan nan cikin nastuwa da kwanciyan hankali.” Nafisa ta fada tana robing din bayan ta.
“Okay toh.” Olamide ta amsa.
Nafisa zata bar wajen kenan, Olamide ta kira sunan ta, ta yi hugging din ta, ta ce “na gode sosai Fisa, Allah ya bar mu tare, Allah ya hada mu a jannah.”
“Awwwn amin amin habibty ta.” Nafisa ta amsa, sannan suka daina hugging din juna, Nafisa ta koma dakin su, ta fara gyara kayan ta. Ita kuma Mide, ta cigaba da wanke wanke.
Daman wanke wanke ba yawa, saboda tunanin da take yi ne, da ta gama.
Da suka gama komai, bayan Zuhur, basu ma tashi akan sallayan da suka yi sallah a kai ba, Nafisa ta tambayi Olamide abun da ke faruwa, Olamide ta fada mata, kuma ta nuna tsoron ta, yau din nan dai ya mata ransuwa zai fada masu, kuma ya bata feedback, so tana tsoron result din.
Nafisa ta ita kwantar mata da hankali, tace mata kuma zai kira, maybe yana wajan aiki ne, amma ta kwantar da hankalin ta, everything will be alright.
“I hope so habibty, I hope so. Kema dai kin san mutanin ku da wannan shegen aladan ko?
Da kyar su yarda.” Olamide ta fada.
“Kar ki damu, ai ba duka aka hadu aka zama daya ba. Kuma zai kira ki In Sha Allah, and everything will be the way we want it. In kuma bai kira ki ba, ke ki kira shi. Amma fa ba yau ba, kaman gobe ko jibi.” Nafisa ta fada.
“Jibi kuma! A’a goben dai.” Olamide ta fada.
“Duk wanda kika ga ya kwanta maki, shi zaki yi. Amma fa kin san maybe goben nan you may be tired. Anyhow dai, am sure zai ma kira ki my bibty.” Nafisa ta fada.
“Toh Allah yasa. Nagode sosai da kulawar ki habibty, Allah ya baki lada.” Olamide ta fada, sannan tayi hugging din Nafisa.
“Amin amin, Allah ya bamu lada duka. I love you sooo much.” Nafisa ta fada.
“Me too. Am also sad tomorrow we will be leaving each other.” Olamide ta fada.
“Me too wallahi. I am going to miss you soo much my habibty.” Nafisa ta fada.
Haka suka ita emotional talks akan yanda zasu yi missing din juna.
〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️
Tun da safe Abdallah ya kasa kiran Olamide, ga shi har 9 din dare yayi. Maybe kawai ya kira ta, sai ya dinga canza magana idan zata yi tambayan abun da su abba suka fada. Amma gobe inta koma gida, sai ya fada mata cewa sun ce zasu yi tunani akai.
Haka ko aka yi. Ya kira ta, yayi wishing din ta best in all the exams she wrote, in taso ta tada maganan, sai ya canza topic, har suka gama wayan, bai bata opportunityn da zata tada maganan ba.
“Allah sarki my qalbi, Allah ya ga bana son in maki karya, amma yana iya, iyaye na basu son union din mu. Duk da cewa basu san ki ba, sun bi sun sa tsanan ki a zuciya, saboda BANBANCIN KABILA. Amma karki damu, zan san yanda zan yi dasu.
Haka Abdallah ya ita tunani, har barci ya dauke shi.
〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️
Tunda suka tashi around 4, ba wace ta kara runtsawa. Suna ta shirye shirye. Suna idar da sallah, suka karanta qur’ani, suka yi addu’an safe, Nafisa ta fara shiga wanka, Olamide ma tazo ta shiga.
Suna gamawa, kowannan su ta shirya, suka rurufe ko ina, su ka kashe duka sockets, sannan kowannan su ta dauki jakar ta, sanan suka yi sallama da sauran mutan gida, kowannan su ta nemi keken da zai kai ta tasha, nan suka yi hugging din juna, kaman baza su bar juna ba, kafun suka shiga, suna waving din juna.
Olamide na isa tasha, luck was on her side, saura mutum daya motan ya cika.
Ita kuma Nafisa, saura mutani hudu.
“Madam what are you looking at, have been calling your name.”
Olamide ta ji tap din mutum a shouldern ta, tana jin muryar, tasa this is definitely her mum. Da sauri, ta juyawa tayi hugging din ta.
“Mummy mi, nayi missing din ki sosai.”
“Me too. Muje mu shiga mota. You look tired baby girl.” Mummy ta fada.
“Muje. Kaman kin sani mummy, na mugun gaji.” Olamide ta fada.
Da suka isa gida, Farida ta fito da gudu, tayi hugging din Olamide, itama Mide tayi farin cikin ganin kawan wata.
Duk sunyi complete, amma banda Hakeem, sai next week zai dawo.
Ta shiga dakin ta, taga an gyara ko ina, sai ta kwanta saman gadon ta, ta ce “wow home sweet home.” Ta dan huta akan gadon, kafun taje ta shiga toilet, ta dan watsa.
Sun dade suna hira, aka maida Mide yar’lele. Da suka gaji da hira, mummy ta wuce dakin ta, Mide ta Farida ma suka tafi nasu.
Farida ta kwanta a nata gadon, Mide ma ta kwanta a nata, tana kwantawa, taji idanuwan ta na rufuwa, tama manta da zance iyayen Abdallah, saboda tsabaragen gajiya.
Asuba ta gari.
Da suka tashi da safe, suka yi morning routine din su, suka yi wanka, suka hadu a dinning, suka yi breakfast. Suna gamawa, ta ki Nafisa, Nafisa ta gaisa da mummy da Farida, itama Mide, suka gaisa da Ummi da abba. Nafisa ta tambaye ta ko Abdallah ya kira, tace ae, amma lokacin tayi barci, so zata kira shi idan sunyi hanging up.
Sun dade suna hira, kafun suka yi sallama.
Da suka gama waya da Nafisa, Olamide ta koma dakin ta, nan ta kira Abdallah.
” Assalamu alaikum ifemi”
“Waalaikumus salam yide’am. An tashi lafiya, kin same su lafiya?
Ya gjiyan hanya?
“Fyn alhamdulilah. Kaima ka tashi lafiya?” Olamide ta tambaya.
“Lafiya kalau.” Abdallah ya amsa.
“Baka je wajan aiki bane?” Ta tambaye shi.
“A’a, yau ina afternoon duty ne.” Abdallah ya amsa.
“Okay toh, Allah ya kaimu afternoon.” Olamide ta fada.
“Amin amin yide’am.” Abdallah ya amsa.
Sai kuma shuru ya biyo baya kafun Abdallah yayi breaking din silence din.
“Akan maganan nan, na fada masu.” Ya fada zucuyar sa na bugawa.
“Okay, me suka ce toh, I hope it’s not what am thinking.”
“Nope it not. Kin san this is the first time this is happening in our family, toh wai zasu yi tunani akai.” Abdallah ya fada yana runtsa idanuwan sa, yana astagfirullah a zuciyar sa. Allah yaga baya son karya, amma at this point, this is the only way out.
“Hmm toh shikenan, at least basu zage ni ba, kuma basu ki ni ba Alhamdulilah, Allah yasa suyi thinking positively. Kaga sai anjima, yanzu mummy zata fara kira na, inta ga na dade ban fito daga daki ba.” Olamide ta fada.
“Okay bye qalbi’am. Abdallah ya fada, sannan ya kashe wayar.