BANBANCIN KABILANOVELS

BANBANCIN KABILA COMPLETE

BANBANCIN KABILA COMPLETE HAUSA NOVEL

Da yaje office, yayi attending to patients, lokacin komawa gida yayi, ya dauki briefcase din sa, ya cire coat din sa, ya rike a hannu. Yana kan tafiya, wani ya kira sunan sa “Dr Abdallah!”.
Yana jin sunan sa, ya juya, yana juyawa, yaga abokin shi ne Dr Farouk.
“Bana ce maka akwai magana ba”? Farouk ya tambaye shi.
“Am sorry, na manta ne. Kasan stress din patients dinnan”.
“Gaskiya attending to patients ba karamin aiki ba ne”. Farouk ya fada.
“Wallahi. So what up”? Abdallah ya tambaye shi.
“Muje mu zauna akan bench dinan dake karkashin bishi yan nan”.
Suka je suka zauna, Farouk ya fara magana ” Guy kasan ansa aure na da Nabila bayan sungama wanan semestern, amma yanzu sun chanza, wai inba damuwa, ayi shi nan da two weeks, twoo weeks fa”. Ya fada yana nuna yatsun sa biyu.
“Congrats man, Allah ya sanya alheri”. Abdallah ya fada.
“Am serious fa, kuma kasan worst part din, su Abba sun yarda, wai hakan ya fi”. Farouq ya fada.
“Toh me ke ciki, ayi abun da za’ayi kawai ka huta. Yours is even good, mufa yanzu muka fara hunting”.
“Toh kai aganin ka hakan ya fi kenan”? Farouk ya tambaya.
“Ae, wallahi, na maka murna fa sosai. Ka ce dai mu fara shirin zuwa kano, ko muma zamu samo wata acan”. Abdallah ya fada.
“Toh mashaAllah, tunda abun ya zauna cif, nima nayi relaxing. Amma da’a I was so worried”.
“Kar ka damu, your brother in islam is here”. Abdallah ya fada.
“Yeah thanks for za support. Sai yanzu ma maganan ka ke flashing. So ba ma raka ni zakayi ba, kaima zaka je neman mata ne”?
“Ae mana, ai yanzu na fara wife hunting, kuma I want it soon, bana son ana raina mu iyaye”. Abdallah ya fada.
“Ban gane ba, wake son raina Su Abba”? Farouq ya tambaya.
Nan ya fada mai komai, sai Farouq ya ce “aiko, ko ni am in support. Allah yasa ka samu. Dama ka samu bahaushiya, muga expression din wanan kawun na ku”.
“Amin aboki na, muga iya gudun ruwan sa, muga ko zai kashe ni ne, ko kuma me. Shi din daya ke magana, ai second wife din sa bajara ce. Amma ya bi ya takura mana, wai sai bafulatana dole”. Abdallah ya fada.
“Kyale shi, dan yaga shi ne babba ai, shi yasa yake mulki akan ku yanda yake so. Aboki na, Allah ya baka bahaushiya, muga karke Kawu”. Farouk ya fada.
“Amin ya rab aboki na. Shi yasa neke ji da kai”.

“`Thanks for reading, sharhi is bea, kaman yanda kuka sani.

    ~Zeexee ce~ ????️????️????️
[8/30, 1:21 PM] Abokiyar Fight????????: ????????????????????????
             ????
 *BANBANCIN KABILA* 
      _(Short story)_ 
????????????????????????
             ????

*TAMBARI WRTER'S ASSOCIATION*

*_????((Home of Expert and Talented writers,  da tambarinmu muke tafe domin kawo gyara da cigaban Al'umah))_*

    *T.W.A*

 *WRITTEN BY ZAYNAB* _(zeexee)_

MARUBUCIYAR

  *-RAYUWAR HUSNA* 

  *-MAHAKURCI MAWADACI (2020)*

Dedicating this page to my Kawallie (Hansey)???????????????? and my kanwas(boddi’am). I love you guys soooo much, long live the three musketeers???????????????????????????????????????? .“`

9️⃣&????

Bismillah

Da suka gama hira, Abdallah ya je gidan adda Wasila.
Saboda yanayin sa, ko mai gadin gidan ma bai mai wasan da suka saba.
Da ya shiga ciki, yaran ta na ganin shi, suka san yau kam uncle auta ba lafiya. So they just greeted him, su ka bar wajan. Adda Wasila ma tasan ba kanta.
“Uncle auta! Lafiya kuwa yau”? Adda Wasila ta tambaye shi.
“Ba lafiya, dan na zo ne na miki magana tsakanin kani da yaya”.
“Toh Allah yasa dai inji alheri”. Adda Wasila ta fada.
“Amin. Gaskiya adda, da zaki ji nawa, ki daina wani kula wannan tsohon familyn mu. Bashi da respect for our parents, even an atom. He talks to Abba anyhow, but you always think his decisions are right, duk da kema ya maki rashin mutunci alokacin da zaki auri Uncle Hussain, ba irin wulakanci da ba’a miki ba, amma yanzu kam na kasa gane direction din da kike”. Abdallah ya fada yana huci.
“Toh Abdallah ya kake son inyi, shi ne fa babba fa a familyn mu, so kake inyi disrespecting din sa”?
“Bance kiyi disrespecting din sa ba, amma ki daina sake masu, dan shi ne abokin shawaran ki. Ni ban sani ba ko neman gidin zama kike oho maki. Adda fa duk wanda baya son iyayen ka, baya son ka ne. Kullum fa cikin raina Abba mu yake”. Yana magana duk jijiyoyin wuyan sa na fita.
“Gaskiya Abdallah, bazan bari ka zo gida na ba, ka dinga mu maganan banza ba. Ni yayar ka ce, shekaru kusan hudu ke tsakani na da kai, kasan yanda zaka mun magana. Kuma kana cewa neman gidin zama nake, toh na neman. Idan ka shirya yi mun magana cikin hankalin da natsuwa, ka mun, in kuma baka shirya ba, here is the door, you can leave”. Ta fada tana nuna mai bakin kofa da hannun ta.
“Wow! Wow! Adda, nagode sosai. Wallahi kina bani mamaki, amma dai tunda kin nuna mun kofa, bari in wuce. Amma karki manta, wallahi in baki guje shi ba, wata rana, sai ya wulakanta iyayen mu agaban ki, kuma ki kasa cewa komai. Amma ki sani, duk randa na samu labari, toh za’a yi ta.” Yana gama magana, ya duki wayar sa da ya ajiye akan center table, ya parlor, ya je wajan da suke parking din motoci, ya shiga motar sa. Yanda Lawali yaga yake driving, yasa ya hanzarta, ya bude masa gate. Daya bude masa ma, kaman zai buje shi, sanda ya matsa da gudu.
Idanuwan sa duk sun bi sun kada sunyi jazur, gashi jikin sa sai bari yake. Last time ma saboda maganan kawu Dajjo, su ka samu sabani da ita, kuma fa duk akan wulakancin da yake ma iyayen su ne. Shi bai san wata iri ce ita ba. Wai mutum ka dinga ganin anama iyayen ka nonsense, amma ka dinga jurewa, saboda kana son a dinga yabon ka, toh sun dade basu yabe shi ba.
Driving yake da gudu, ya iso wani green gate, ya fita a motar, ya buga gate, wata farar mace ta fito, mai kama da Abdallah sak, da yaron ta da bazai wuci 2 years ba yana biye da ita.
“Waye ne”?
“Ni ne, ki bude mun”. Abdallah ya fada.
“Aww yau kam an tuna da ni kenan”. Ta fada tana bude gate din.
Data bude, sai ya shigo, ya bude duka gate din, ya shigo da motar sa, ita kuma tana gafe, dan ta na manne da ita.
Da ya gyara parking, ya fito. Yana fita ya ce “chewing gum din Mummy, baza’a gaishe ni bane”?
Yaron ya ki motsawa, instead, ya kara manne ma Mumnyn sa.
“Mu shiga daga ciki, Afran ka na can, ka bar mun da na”.
“Ko baki fada ba, me zanyi da wannan mai kiwan”.

Da duka shiga ciki, ya zauna a parlor, Afra na jin muryar sa, ta fito tana “oyoyo Uncle”. Ta zo da gudu ta rungume shi. Bata wuci shekara hudu ba, tana kama da Umma takwaran ta. Dan asalin sunan ta Rukayya ne, amma suna kiran ta da Afra. Abdallah na mugun son Afra tamkar shi ya haife ta, although niece din sa ce, but he has a fatherly love for her.
“Oyoyo my Afra. Ya kike”? Ya tambaye ta.
“Lafiya kalau Uncle. Baka tambaye ni ya school ba”. Ta fada tana tura baki.
“A’a afuwan Afran Uncle. Ya school”?
“Fine, an bamu homework”. Ta fada.
“Toh mashaAllah, adage da karatu ko my Afra?
Kuma fa a dinga zuwa islamiyya, a daina karyan ciwon ciki”.
“Ina zuwa, ko Mummy”? Ta tambaya, tana kallon wanda ta kira da Mummy.
“Bawani, sai na hada da bulala kike zuwa”. Matar ta fada.
“A’a adda Fadi, bazan yarda kina dukan mun ya ba. Ina yi aure, zan zata fara samun saida, saboda yau tana nan, gobe tana can, dan haka ki rike amana kafun lokacin”.
“Toh Abdul”.
“Yauwa”. Sai ya kalli Afra, ya ce ki tafi daki zanyi magana da Mummyn ki”.
“Toh Uncle, amma baka kawo mun choclate da bobo ba yau”. Ta fada kaman zata yi kuka.
“A’a, kar ki sa hankali na ya tashi, kafun in wuce, zan siya maki”.
“Owk Uncle, mi yatti”. Tana fadan haka, ta wuce daki.
“Kaga ma ko tayin ruwa ban maka ba”. Adda Fadila ta fada.
“Toh ai nayi zaton baza’a bani ba”.
“Ai ban isa ba, bari in kawo maka drink, ko ruwa zalla kake so”?
“Toh kaji jikar Dajjo, ki kawo mun duka biyu. kuma na san baza’a rasa small chops ba, ahado mun, dan nasan ina gama magana, zan bukace su”.
“Shikenan an gama my brother.” Ta tashi, zata bar wajan, dan ta ya rike mata kafa.
Kai! Irfan, kar ka fadar dani fa, kaje wajjan addan ka, nima ka bari nayi attending to my brother”.
“Wannan dan ki mai ido kaman mage zai bar ki ne?
“Kai bro, ka daina zagin heartbeat fa”. Ta fada, sai ta duki Irfan, ta tafi kitchen da shi a hannu.
“Ni kam na ga ikon God yau, naga yanda zaki kawo mun abubuwan nan da shi ahannun ki”. Ya fada.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button