BANBANCIN KABILANOVELS

BANBANCIN KABILA COMPLETE

BANBANCIN KABILA COMPLETE HAUSA NOVEL

Ana gama lectures, suk fita. “Yauwa my ore’s, yaushe zaku fitar anko ne, kun san kune manyan kawaye fa”. Nabila ta fada.
“Ko gobe ko jibi”. Nafisa ta fada tana kallon Olamide.
“Ae hakan yayi. Kuma mu sanar ma yan dept din mu, da kawayan mu”. Olamide ta amsa
“Toh mashaAllah. Ba zaku zo gaida hajiyar ku bane”. Nabila ta tambaya.
“Ai gaisuwa ya zama dole, ala ma mu biki yau ko habibtyn Fai’za”. Olamide ta tambayi Nafisa.
“Hakan ma yayi”. Nafisa ta amsa.

Thanks for reading.

  ~Zeexee ce~ ????️????️????️

[8/30, 1:21 PM] Abokiyar Fight????????: ????????????????????????
????
BANBANCIN KABILA
(Short story)
????????????????????????
????

TAMBARI WRITER’S ASSOCIATION

????((Home of Expert and Talented writers, da tambarinmu muke tafe domin kawo gyara da cigaban Al’umah))

*T.W.A*

WRITTEN BY ZAYNAB (zeexee)

MARUBUCIYAR

-RAYUWAR HUSNA

-MAHAKURCI MAWADACI (2020)

Dedicating this chapter to my jikoki, Fatima and Ayusha (Jiks 1 and 2)????????????????????????????????. Your comments make my day.

1️⃣1️⃣&1️⃣2️⃣

Bismillah

Suka fita daga school premises, suka nemi kekeh da zai kai su anguwan su Nabila.

Da aka sauka su awani dan madaidaicin gida, amma fa gidan akwai kyau sosai, tun daga wajan gidan har ciki, akayi decorating din shi da flowers, so flowers din sun fito da kyaun gidan sosai.
Nabila ta kwankwasa kofar, aka mude masu.

“Sannu baba” suka fada a tare.
“Yauwa sannun ku, kunzo lafiya”? Ya tambayi su Olamide.
“Lafiya kalau”. Nafisa da Olamide suka amsa.

Cikin wani kofa suka shiga, nan suka cire takallaman su, sannan suka shiga parlor da sallama.
Suna shiga, suka samu mahaifiyar Nabila, kanwar ta Safina da yayan ta Faeeq.
Da sallam suka shiga, Hajiya Hajara na ganin su, ta ce “sannu ku da zuwa my daughters”.
A kunyance suka tsuguna a gaban Hajiya, suka gaishe ta. Ita kuma Safina, ta rungume su, ta ce “nayi zaton ko ba zaku zo kuga autar Hajiya bane”.
“Mun isa”? Nafisa ta tambaya.
“A’a bamu isa ba” Olamide ta fada.
“Toh ni baza ku gaishe ni bane?
Especially wannan bayarbiyar”. Yaya Faeeq ya fada.
“Ina wuni yaya Faeeq. Ni dai na gaishe ka, saura yoruba princess din ka”.
“Tab!! Allah ya kiyaye”.Olamide da Yaya Faeeq suka fada tare
“Ni kam Faeeq ka bar mun ya’a fa. Zo ki zauna kusa dani yar’lele ta”. Hajjiya ta fada. Da sauri Olamide taje ta zauna kusa da ita.
“Ni wallahi Ummi shiyasa bana son zuwa gidannan in yaya Faeeq na nan”. Ta fada a shagwabe.
“Ki kyale shi. Ni nasan yana son ki ne, kuma bazan bashi ke ba”. Hajiya ta fada tana murmushi.

Duk yanda yaya Faeeq yake da keyi da Olamide, dukan su ke noticing. Abun kadan sai yayi maganan ta, ko tana nan ko bata nan. Ga shi yanayi da yake mata magana ma ya bayyana.

“Allah ya kiyaye, me zanyi da ita”. Yaya Faeeq ya fada.
“Nima Allah tsare ni nayi soyayya da kai”. Olamide ta fada tana hararrar sa.
“Ki shiga hankalin ki dani, ki bar ganin ke ba muharama ta bace, zan dake ki ne black and blue”. Ya fada yana ya making serious face.
“Kai!! Wani baku gajiya ne?
Kullum ku dinga fada kaman cat and dog. Yaya Faeeq mun san kana son Olamide ne, ba sai kamana corner corner ba. So ka fada mata kawai, kunga sai ahada auran ku”. Safina ta fada.
Tas taji abayan ta. “Ina wasa dake ne”? Yaya Faeeq ya tambaya.
“Faeeq!! Bazan yi tolerating din haka ba. Ka tashi ka bar mana parlor, I want to have a girlie moment with my girls, kaga ya dade bamu hadu ba”. Hajiya ta fada.
“Bai sai kin fada ba Ummi, daman ina da niyyan tashi, amma naso in koyama bayarbiyar nan hankali. But anyways gwanda in bar ta da halin ta”. Yaya Faeeq ya fada. Sai yayi pointing din Nafisa, ya ce “ke kuma lokacin biki, kar ki yi wuf da wani ki gani, zan neman maki tsoho. So it’s better ayi da yaro kafun ran Faeeq ya baci. Yaya Faeeq na gama magana, ya bar wajan.
Yana tafiya kaman wanda kafafuwan sa bazasu taba kasa ba, yi yake kaman yana tsoron in suka taba kasa, zasu bata.

Sun dade a gidan su Nabila, dan sai bayan isha, Hajiya tace ma Yaya Faeeq ya mai da su. Nan ma sanda Nafisa ta ita raba fada. Shi Faeeq, baya gajiya da tsokanan ta, ita kuma bata gajiya da bashi amsa, so shi yasa suke prolonging din issue.
“Wallahi Olamide, in kika bani haushi, anan zan sauke ki. Kuma kin san baki son a bun da zai sa dare ya same ki a waje, zanga yanda zaki koma gida”. Faeeq ya fada a fusace.
“Ka sauke ni mana, sai me?
Ai ba mutuwa zan yi ba. Inada kudi na da zai kaini har gida”. Itama ta fada tana huci.
“Sai ya tsayar da mota, ya fita, ya je side din da take. Daman tana back sit ne, Nafisa kuma na passenger’s sit. Kuma anyi hakan ne, saboda kar suyi fada, amma ina abun nasu a cikin jini yake.
Daya tsaya abakin kofar, ya bude, sai ya ce “ki fita”.
Kaman jira take, ta yi hanging din jakarta , dan daman tasa jakar saman cinyar ta ne. Tana hanging din jakar, ta fito. Nafisa na ganin haka, ita ma ta fita. Sai ya ce “baki da case Nafy, ki koma ciki. Daman wannan yar rainin hankalin ne”.
“Gaskiya bazan iya kallon habibty na haka ba, so duk hukunci daka dauka akan ta, kaman akai na ka dauka. Ka wuce kawai, mun gode, dan na san da kyar in habibty zata kara shiga motan nan”. Nafisa ta fada.
“A’a ke ba ruwan ki, ki shiga, kuma ita din ma, nasan zata shigo ai, ba yau muka fara ba”. Yaya Faeeq ya fada.
Faeeq da Nafisa annan suna settling matter, ita ko tana can tana neman adaidaita.
Tana samu, tayi ciniki da shi, sai ta ce “habibty kizo na saman mana adaidai ta, kizo mu wuce time na tafiya”. Ai ko tana jin haka, ta taho, suka shiga keken, ya wuce dasu.

Shi kuma yaya Faeeq, takaici ya kama shi, bai yi zaton zata samu abun hawa ba, gashi shi yaso ko in zata wuce, ta bar mai Nafisa. Kowa na ganin kaman Olamide ya ke so, but in real sense Nafisa yake so. Me shi zaiyi da yar yarbawa, su da akace suna da masifa, ga fada. Ai gashi ma ajikin Olamide, yarinya sai shegen tsiwa. Allah ya tsare shi, yaje ya aure ta, duk randa yan’borin ta suka tashi, tasa shorts, suyi fada. Gwanda ma Nafisa.

Suna sauka a bakin gate, Olamide ta ciro kudi ta ba shi, sannan suka shiga ciki. Suna shiga, Allah yayi akwai wuta, sai suka kunna fanka, kowanan su ta cire hijabin ta, ta ninke, ta cire bag, suka yi hanging din shi, suka sa takalman su a mazaunin su. Sannan Olamide tayi plugging din ruwa acikin kettle.
Tunda suka shigo, ba wanda ta ce ma wata kala, kowannan su nata harkan gaban sa. Ita dai Nafisa, bata son ta fadi abun da zai bata ma Olamide rai ne, ita kuma madam, sai huci take, tana regretting din zuwan su gidan su Nabila. Ita bawai ta sake masa ne ba, amma ita gaskiya ba zata bari yana zagin ta tayi shuru ba, lokacin da suke 100l, ta na dan jin kunyar sa, bata maida mai magana. Amma yanzu kam she can’t take it. Mutumin da ba akan ta zagin ya tsaya ba, ya zage ta, ya zagi yaran ta, kuma abun da bai sani ba is that she is very proud of her tribe, duk da dai bata san garin su ba, amma she is still proud. Kuma ai Allah ya halice mu, yanda Ya halici baki, haka ma fari, ya halice mu in different nations, state, colours, tribes e.t.c, why not mu dauki juna as one, we are all Allah’s creation. Amma wasu kam baza su iya ba. Inba racism be, toh tribalism, kuma yana everywhere. In yana ma wasu, suna barin shi, toh ita baza ta bar shi ba. Tana cikin tunani, wayar ta ya fara ringing. Data duba, taga sunan daya fito kan screen, tayi murmushi, ta daga. “Assalamu alaikum Ummi”.
“Waalaikumus salaam ya’a. Kun isa gida lafiya”? Hajiya Hajara ta tambaya.
“Lafiya kalau Ummi”. Ta amsa.
“Toh Masha Allah. Ina Nafisa”? Hajiya Hajara ta tambaya.
“Gata”. Olamide ta fada, ta mika ma Nafisa wayar. Suka gaisa da Nafisa, kafun ta sa masu albarka, suma suka mata godiya, sannan suka kashe wayar.
“Habibty danAllah kiyi hakuri ki daina fushi please”.
“Ba fushi nake ba. Kawai dai Ina regretting ne. Da ban san Nabila ba, da bazan hadu da tribalist dinnan ba. I hate his character wallahi. He should even thank his stars, ya girme ni, inba haka ba, daya fi haka shan maganganu a waje na, dana masa tas wallahi” Olamide ta fada.
“Kiyi hakuri kawai, ki dubi relationship din mu da Nabila, ki yafe mai”.
“Daman ai saboda Nabila nake ragan masa, inba haka ba, dana dinga bashi amsoshin da zai kasa sa kan sa a pillow”. Olamide ta fada.
“Ko ni, bana jin dadin yanda yake maki”. Nafisa ta fada.
Suna cikin magana, kettle din ruwan da Mide tayi plugging, ya masu signal. Da sauri Mide ta kashe, ta zuba cikin bokiti, ta kara cika shi da ruwa, ta yi plugging.
Ta dauki bokitin ruwan zafi, ta wuce toilet, tayi wanka, sannan ta fito. Tana fita, Nafisa ta shiga, itama.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button