Uncategorized

TAKUN SAKA 48

 *_Chapter Forty Eight_*…………Duk wanda ya kwana ya tashi a wannan ƙasa yau an wayi garine da babban labarin kama master da iyayen gidansa. Duk da kasancewar akwai sauran duhun asubahi hakan bai hana anguwar cika da mutanen cikinta da jami’an tsaro ba. Hakama ƴan jarida da basu yarda a barsu a baya ba. I.G da C.P ma basu zauna ba nan suka nufo dan case ne babba da kowa ke buri akan ganin wannan rana da za’a kama master. Kowa

ba’a bari ya shiga gidan ba hatta sauran jami’an tsaro, dan Master da yaya Abubakar sai da suka gabatar da sallar asubahin su, sauran yaransu ma sukayi sannan suka yarda suka buɗema su I.G ƙofa. Duk da I.G ya jima da sanin su A.G a cikin tawagar ta bakin Master a yau daya gansu sai takaicinsa ya sake ninkuwa da tsanarsu. Ya kauda kansa hawaye na ciko masa idanu. (Wai fa manyan mutane daya kamata su bama ƙasa kariyane anan tare da ɗan ta’adda mai ruguza ƙasa. ALLAH kaɗai yasan irin ɓarnakun da sukayi a tsahon shekarun da suke tare da shi. Akwai irinsu da yawa kuma dake lulluɓe da rigar mutunci suna cin dunduniyar ƙasa. Ta yaya ƙasa zata gyaru bayan manyan cikinta sune masu bada gudunmawar gurɓatar yaran dake ta’addanci. Kullum aiki sukeyi ƴan ƙasa na ganin gazawarsu da tunanin yaudara a dalilin tufkar da suke wasu na warwarewa saboda makullan madafun iko dake cikin hannayensu ta ɓangarori da dama).         Duk da agalabaice su A.G suke saboda harbin da Master yasa akai musu hakan bai hanasu jin kunyar idon su I.G ba, ga ƴan jarida da aka bama damar shigowa sai ɗaukarsu suke a hoto da video lokacin da ake fiddosu da ga gidan. Master ya bada damar saka hajiya mama a motar asibiti, su Abba kam da su A.G aka tarkatasu zuwa police station jami’an tsaro zagaye da su mota-mota.

_____________________________

         Hibbah da Ammar na zaune a falo tun bayan sallar asuba, Hibbah dake latsa wayar Ammar tana kallon hotunan biki tai wani irin zabura ganin news da ɗumi-ɗuminsa a facebook akan an kama Master. Gaba ɗaya ta rikice dan duk zatonta Master ɗinta ne. Cikin tashin hankali Ammar da yaga yanda ta gigice ya warce wayar ya duba shima, da sauri ya rarumi remote ya kunna ƙaramar television dake a falon, a dai-dai nan su Yaya Usman ke sakkowa da ga sama hakama Ummi. Gaba ɗaya wutar kan kowa ta ɗauke saboda ganin abinda ke faruwa. Hibbah ta sauke wata nannauyar ajiyar zuciya lokacin da ake nuna su A.G da master ɗan ta’adda a galabaice saboda harbin da suka sha. Sai su Yaya Abubakar da Master dake ƙoƙarin zillema ƴan jaridar dake neman titsiyesu nason jin yaya akai suka kama master.

       “Kambu! Da gaske fa Yaya Isma’il jami’in tsarone Ummi”.

     Ammar ya faɗa a zabure yana nuna television ɗin. Hannu Ummi ta ɗaga sama tana godema ALLAH, dan harga ALLAH taji daɗi har cikin ranta, ta share hawayen dake zubo mata na tsantsar farin ciki tana kamo hanun Hibbah ta rungumeta.  

______★

     Cikin ƙanƙanin lokaci duniya ta ɗauka. Hotunan su R.D da Master suka fara yawo a social media ta kowanne ɓangare. Tuni kowa ya fara tofa albarkacin bakinsa akan wannan al’amari mai ban mamaki, musamman ma da manyan ɓarnakun da su A.G suke aikatawa suka fara fitowa a bakunan wasu mutane da suka san sirrinsu. Waɗanda ada tsoro ya hanasu fitowa su faɗa. Musamman ma’aikatan gidajensu na shakatawa. Sai kuma wasu boyayyun mutane da harkalla ta haɗasu da su A.G ɗin suka cutar dasu ko makamancin hakan. Wannan fa shine allura ta tone garma. Dan kuwa har abinda ma ba’ai zato ba sai gashi yana fitowa. Cikin ƙanƙanin lokaci ƴan bani na iya musamman matasa suka fara yo gangami zuwa police station akan a basu su A.G su halaka. Hankalin su Master ya tashi, dan an rasa wanda ya fara fasa zancen su A.G ɗin na Homo. Sai da suka zurfafa binciken gaggawa aka gano a wani shafi na manhajar facebook maganar ta fito, sun bibiyi shafin kuma sunga an buɗesane a safiyar yau dai-dai lokacin da zancen kamasu A.G ɗin ya fito. Babu wani kuma damar da za’a iya bibiyar mai shafin da ita kai tsaye, dan komai bai saka ba. Email ɗin da akai amfani da shi ma babu wani information tattare da shi. Ana cikin haka sai ga wasu hotuna kuma sun fara yawo nasu Halilu da su A.G ɗin tsirara haihuwar uwayensu suna aikata baɗala fami muni da cizon zukatan masu imani.

     Tuni komai ya sake birkicewa, matasa da dama ƙiris suke jira sun sake harzuƙa akan infa ba’a basu su Abba ba to lallai zasu ƙona ofishin ƴan sandan. Duk yanda su Master sukaso controling mutane cikin sauƙi hakan ya gagara, dole aka haɗa da barkonon tsohuwa mai saka hawaye sannan suka tarwatse, jami’an tsaro ta kowanne fanni suka maye gurbin harabar station ɗin dama titin baki ɗaya. Amma duk da haka fama aketayi da matasa.

         I.G da yaga abin na neman zama babban al’amari dole ya fito yay magana ga ƴan jarida cikin lallashi, ya tabbatar ma da jama’ar gari basuyi ƙasa a gwiwa ba wajen miƙa su A.G gaban alƙali, dan haka su kwantar da hankalinsu gaba ɗaya suspects ɗin zasu sami hukunci dai-dai da ɓarnar da suka aikata. Zakuma a zurfafa bincike domin cigaba da zaƙulo duk waɗandama suke tare da su da ba’a kamaba a yanzu haka.

       Bayanin I.G ɗin ya ɗan kawo lafawar tarzomar, sai dai fama matasa nata kaikawo a media cewar inhar ƴan sandan basuyi wani abu da wuri ba to lallai su zasu ɗauka hukunci a hannunsu, kuma zasu tabbatar da shi.

        Da ga Master har yaya Abubakar a jigace suke, tun daren jiya suke abu guda babu hutu, ga Master dama ba isashen lafiya ne da shi ba. Dauriyace kawai da jarumta da son sauke aikin nan ya hutama ransa. Idanunsa kawai ka kalla dake cikin mask zaka tabbatar da yana buƙatar hutu, sai dai kuma babu damar hakan. Sai da I.G ya fahimci kamar jiri na neman ɗibar Master ɗinne sannan ya kamosa ya zaunar yana masa faɗa.

        Koda yasa aka samo masa abinci tea kawai ya iya sha, ya samu yasha maganin da Habib ya kawo masa da ga gida da ƙyar bisa taimakon Abdull. dan su tun jiya da suka kammala aikinsu suka koma gida suka koma kallo da jiran news. Sai da suka fahimci Master bashi da niyyar fasa ƙwai akan ƙazantar su A.G ne yasasu buɗe shafi suka saki hotunan su A.G ɗin da suka taɓa samu a camara ɗin Master batare daya sani ba tsahon lokaci. Sai dai kuma kafin su saki nasu sai ga wani shafin ya saki zancen su A.G ƴan homo ne. Hakan ya musu daɗi dan sun samu abokin ritatawa. Yanda garin ya hargitse da yunƙurin mutane na abasu su A.G su halaka ba ƙaramin daɗi yay musu ba a rai da zuciya.

  

            ★★★

    A nan wajen su Ummi ma Ammar da Hibbah suna a cikin kwatankwacin farin cikin da su Habib ke ciki, dan kuwa ita da Ammar ɗinne suka buɗe shafin farko wajen bayyanama duniya su Halilu ƴan homo ne. Kasancewar Hibbah kwararriya ce mai ƙwazo ta tabbatar za’a iya bibiyan shafin koda badaga jami’an tsaro ba tabi matakai na ɓoye kai da bin hanyoyin da labarin zai saurin yaɗuwa ga al’umma. Sai ko gashi bukatarsu ta biya. Dan ko mintuna ashirin cikakku basuyi ba zancen ya fita. Har manya-manyan shafukan sada zumunta na yaɗa labarai irin su bbc suka ara suka yafa suma.

___________________

         Kwatanta muku irin baƙin tashin hankalin da iyalan Halilu da nasu A.G dake hannun Master suka shiga ma ɓata lokaci ne, tsabar firgita na shigar al’amarin cikin kunnuwansu wasu har yanke jiki suke suna faɗuwa musamman akan zancen Homo ɗin nan. Dan masu guntayen hawan jini dana suga tuni sun haura dubu bisa dubu ma ba ɗari biyu ba. 

1 2 3 4Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button