NOVELSUncategorized

YARIMA FUDHAL 26-30

*YARIMA FUDHAL*
Na
FIRDAUSI S.A(QURRATUL-AYN).
NAGARTA WRITERS ASSOCIATION®
SADAUKARWA:-Namesy Phirdauceey Jeebour
26
Shiru ne ya biyo baya illa shash-shek’ar kukan Aynu da ke ta shi, Ummanta keta aikin lallashinta kafin Baban yace.

“Kuma ni duk ba wannan ne abin da yasa na yanke wa Fudhal wannan hukuncin ba, kafin yace zai zo gidan nan da kwana biyu wani saurayi yaje ya same ni a zaune a bakin kasuwa ya kira ni bayan mun gaisa yake fad’amin cewa….!”.
“Ya zo ne wajena da muhimmin abu, abin kuwa shi ne ya kunnamin a cikin wayarsa muryar Yarima ce sosai da abokin nan nasa suna tattaunawa ne a bisa yanda za suyi su shawo kanmu ta hanyar yaudara”.
“Babu abin da yafi d’auremin kai, sai shawaran da suka yanke na cewar zasu sanya Aynu makaranta, sannan zai nemi soyayyarmu daga baya kuma zasu mai da mu masu kud’i…!, wato Ummun Aynu ki fahimci wani abu guda d’aya, da yawan al’ummarmu na yanzu muna mancewa da Allah a cikin dukkan al’amarinmu, shin su Yarima sun mance cewa babu wani mai azurtawa sai Allah?, kuma babu mai talautawa sai Allah!, abin ya d’auremin kai sosai wannan dalilin ya sanya na yankewa Yarima wannan hukuncin amma ba wai dan BURIN FANSA ba..!”
Aynu ta mik’e ta shige d’aki da gudu ta durk’ushe a k’asa tana rusar kuka, kafin ta share hawayenta daga baya tana ganin meye amfanin zub da hawaye akan wanda bai cancanta ba?, a yau ta yanke duk wata damuwa da hawaye indai akan Yarima ne…..!.
SHIN HAKAN ZAI YIYU KUWA?.
***
Yarima ya dubi Anwar yana mai cigaba da fad’in.
“Ko kad’an bani da laifi akan duk kan abubuwan da suka faru Anwar!, tabbas nasan na d’auki mota na fita a wannan rana sai dai ban san yanda akai hakan ta faru ba duk iya k’ok’arin da nayi domin take burki a lokacin gagara yayi ashe burkin ya samu matsala ne?, ban sani ba Allah ne kai ya kai ni gida a lokacin cikin ta shin hankali da tsoro….”.
“Tabbas babu wani bawa da zai iya kaucewa k’addararsa komai k’ank’antarta domin ita k’addarar mutum a rubuce take tun gabanin zuwansa duniya, Anwar Mahaifina shine ummul-aba isin haddasa dukkan a bubuwan daya faru, a ranar da abin ya faru nazo gida cikin rud’u da tsoro fuskantar hakan da Mai Martaba yayi ne kuma yaji dukkan abin da ya faru sabida son da yakemin sai yak’i yarda da abin da aka ce na aikata !, a lokacin nayi k’ok’arin zuwa fada domin in tabbatar da abin da ya faru alokacin da iyayen Aynu suka zo, sai dai Mai Martaba ya sanya aka tsare ni aka hanani zuwa ko ina, a washe garin ranar ya nema min visa da komai domin barin k’asata da kowa a cewarsa kafin dawowata an mance da komai nima kuma na mance, amma bai san hakan babbar matsala ya jawomin ba, sabida ni kai na tun da naje k’asar tsayin shekaru goma sha shida kenan abin yana raina wallahi Anwar k’arshema sanadin hakan ne ya jawomin ciwon zuciya..!”.
“What…!, ciwon zuciya fa kace?”.
“Yes…kana mamaki ne?”.
Anwar mik’ewa yayi a rud’e ya fara duba magungunan da Yarima kesha domin bai tab’a dubawa ba bare har yasan abin da yake damunsa.
“Ban da kai a yanzu nan gida babu wanda yasan abin da yake damuna sai doctor Mansur da ya zo ya duba ni farkon dawowata time d’in da nayi fama da fever shima na rok’eshi kada ya sanarwa kowa kuma bai fad’a d’in ba”.
Shiru ne ya biyo baya kowa yana tunani a cikin zuciyarsa, can Anwar ya nisa tare da duban Yarima.
“Kayi hak’uri komai zai wuce insha Allahu !, zanyi k’ok’ari wajen shawo kan Mahaifin Aynu !, tun da ai abisa kuskure abubuwan suka faru ina ganin idan yasan gaskiya zai sauko !”.
Yarima ya dubi Anwar kamar zai ce wani abu sai ya fasa, ya mai da kai kawai bisa katifa ya kwanta.
***
“Me ki kace Aynu !, ki na so ki cemin Yarima Fudhal ne yayi sanadin mutuwar yayanki?, yayi sanadiyyar rasa k’afar Baba tare da rasa idon Umma?”.
“Ehh haka ne Zainab!, nima ajiya nasan wannan al’amarin”.
Zainab tayi shiru tana duban Ayn cike da tausayawa, kafin ta dafa kafad’arta.
“Kenan ya zama dole ki rabu da Yarima kenan?, ko badan hakan bama iyayenku basa son had’in?”.
“Ehh”.
“Bani da abincewa daya wuce addu’a Aynu, Allah yayi maki zab’i mafi alkhairi!”.
“Amin summa amin”.
Aynu ta fad’a tana mai share kwallar da ta taru cikin idonta.
***
“Ina son ganin Aynu !, Anwar dan Allah ka raka ni!”.
“Kana son ganin Aynu kuma Fudhal?”.
“Ehh haka nace”.
“Amma taya zaka ga Aynu yanzu a cikin wannan halin, kuma da dare haka?, ka da ka mance da a bubuwan da suke faru wa ?”.
“Na sani Anwar amma ko ta wanne hali inason ganinta !, dan Allah muje ka raka ni Allah idan ban ganta a yau ba zan shiga wani hali….!”.
“In baza kaba kaga tafiyata”.
Yarima Fudhal ya mik’e cike da k’arfin hali ya zari key d’in mota zai fita bai ko damu da yanayin jikinsa ba.
Ganin da Anwar yayi tabbasa da gaske tafiya zai yi, kuma a cikin halin da yake ciki, shi yasa Anwar ya mik’e da sauri ya bi bayansa tare da kiran sunansa.
Tafe suke a mota Anwar ne ke driven d’insu babu mai cewa da wani komai, har suka isa unguwarsu Aynu Anwar yayi parking dai-dai layin gidan nasu, Yarima har ya riga Anwar fitowa sai da Anwar ya d’an taka da gudu kafin ya taddashi yana fad’in.
“Wai kai lafiyarka kuwa?”.
Yarima bai ko kalleshi ba bare ya kulashi.
Tsaye take k’ofar gidan nasu tare da Ya Sayyadi Umar suna hira, galabin hiran shine domin Aynu daga uhmmmm sai uhm-uhmm abin da take furtawa kenan domin ko kad’an hiran ba tayi mata dad’i, Allah-Allah takema taji yace zai tafi.
Tana wannan halinne taji k’irjinta ya tsananta bugu da sauri, k’amshin turarensa taji ya daki hancinta kamar ance ta d’ago kanta, tana d’agowa suka had’a ido duk da garin da d’an duhu amma akwai hasken farin wata, a tare zuciyoyinsu suka buga lokaci guda Aynu ta mai da kanta k’asa da sauri ba tare data sake marmarin sake kallon inda yake ba!.
Ya Sayyadi Umar ne ya lura da cewa wajenta suka zo, kuma ya gane Yarima ne ya dubi Aynu yana fad’in.
“Zo muje mu gaisa da alamu wajenki ya zo?”.
“Kaje kawai ni babu inda zanje!”.
“A’a kada kiyi haka Aynu bak’onka fa Annabinka, kinsan kuma babu kyau wulak’anci, ki taimaka dan Allah ki saurareshi ki ji da abin da ya zo kinji?”.
Bata kuma cewa komai ba tabi bayansa, Ya Sayyadi Umar ya mik’awa Anwar hannu sukayi musabiha ya mik’awa Yarima Fudhal amma Yarima ko kallon inda yake baiyi ba, Ya Sayyadi ya sauke hannunsa cike da murmushi yana mai da kallonsa kan Aynu.
“Zan jira ki”.
Haka yace da ita ya koma inda suke tsaye ya tsaya yana zaman jiran Aynu.
Aynu ta kau da kanta gefe ba tare da ta ce da su komai ba, har tsayin wani lokaci shi Anwar yama rasa ta inda zai fara domin Aynu ayau sai yaji tayi masa kwarjini da yawa gashi kuma ta had’e girar sama da ta k’asa alamun babu wasa, Yarima kuwa ya kafeta da ido babu ko k’iftawa sai faman doka murmushi kawai da ya keyi wani sanyin dad’i na ratsa dukkan sassan jikinsa, Anwar ne yayi k’arfin halin fad’in.
“Sannu Gimbiyarmu, kina lafiya?”.
“Lafiya k’alau”.
Hakan da tace ne ya bashi damar ci gaba da fad’in.
“Kina neman zauta Yariman mu da soyayarki ko?, yanzu dai gashi nan ya tasomu cikin daren nan ya ce inbai ganki ba babu zaman lafiya….!”.
Kallon data watsa masa ne ya sanya shi tsuke bakinsa tun kafin ya k’arasa maganarsa.
“Yanzu ai ya ganni ko?, to zaku iya tafiya daga yau bana k’aunar sake ganinku k’ofar gidanmu har a bada !, wancen shine wanda zan aura nan da lokaci k’ank’ani fatan kun gane?”.
Bata jira mai zasu ce ba tajuya abinta, ba Anwar ba hatta Yarima mutuwar tsaye yayi a wajen, yama rasa ta cewa domin dama kasa furta komai yayi sabida bai san mai zai ce da ita ba, amma ko babu komai ya d’anji sanyi a cikin ransa domin yaga farin cikin rayuwarsa Qurratul-aynun sa (Sanyin idaniyarsa).
Anwar ne ya ja shi har zuwa mota suka shiga Anwar ya tada mota suka bar layin.
“Yanzu kenan Aynu ta san komai?”.
Cewar Yarima kenan yana mai duban Anwar, Anwar bai dube shi ba ya fara fad’in.
“Ai ba sai ka tambaya ba, daga maganganun da take da irin kallon da take jifanmu da shi wannan kawai ya isa ka bawa kanka amsa…!”.
Yarima Fudhal yayi a jiyar zuciya tare da kwantar da kansa bisa kujerar motar ya lumshe ido sai ga hawaye na bin gefan idonsa a hankali ya furta.
“AYNUL-HAYAT fountain of life…..!”.
*YARIMA FUDHAL*
Na
FIRDAUSI S.A(QURRATUL-AYN).
NAGARTA WRITERS ASSOCIATION®
SADAUKARWA:-Namesy Phirdauceey Jeebour.
27
BAYAN SATI ‘DAYA…!
Cikin satin abubuwa da dama sun faru ciki kuwa har da d’an samun sauk’in jikin Fudhal, hakan ya sanya aka gudanar da bikin bud’e sabon asibitin Yarima Fudhal da mai martab’a ya gidana masa, an fara aiki gadan-gadan kwararrun likitoci aka d’auka domim taya Yarima Fudhal gudanar da asibitin yanda ya kamata.
Duk irin dauriya da dannewa da Yarima ya keyi amma hakan na neman fin k’arfinsa, domin wani lokacin yakan kasa daurewa zuciyarsa daga abin da take muradi, har sai ya d’auki mota yaje layin gidansu Aynu ya tsaya har lokacin zuwa islamiyyarta sai ya ganta sannan yakan d’anji dama-dama cikin ransa, Aynu da Zainab basu tab’a gane shine a cikin motar ba domin yakan d’auko d’aya daga cikin motar abokan aikin sane baya d’aukar motarsa sabida gudun kada su gane shi.
Al’amarin Aynu kuwa a kullum burinta bai wuce tamance da Yarima Fudhal ba, tana so tasa aranta tamkar mafarkinsa tayi ta farka, sai dai hakan ya gagara a gare ta, sau tari idan suka zo wuce wa ta inda Yarima ke tsaye Aynu takanji bugun zuciyarta ya tsananta sosai kuma tanajin k’amshin turarensa sai dai Zainab takance ba shi bane kawai dai har yanzu tana son sane shiyasa takeji kamar shine a motar, batun turare kuma ai bashi ka d’ai ne ke amfani da irin saba, ba shi kad’ai campany suka yiwa ba, ita dai Aynu tana barin zancen ne kawai domin Zainab ba ta yarda amma tanaji a cikin ranta tabbas Yarima ne.
“Wai Uwar soro har yanzu aikin yak’i samuwa ne?”.
Uwar soro ta d’an risina tana fad’in.
“Wallahi ranki ya dad’i duk iya k’ok’arin da nakeyi abin ya faskara na rasa yanda zanyi insamo…!”.
“Kinga idan kawai bazaki iya ba ki sanar dani tun da wuri !, abu kusan wata guda amma ya gagara?”.
“A k’ara hak’uri dai ranki ya dad’e insha Allah cikin satin nan komai zai kammala”.
“To babu damuwa amma fa kiyi aiki da nutsuwa da kulawa”.
“Babu matsala ranki ya dad’e kada ki damu”.
“Shi kenan tashi kije”.
Uwar soro ta mik’e tabar d’akin, Jalila dake zaune gefan Fulani Sokoto tana faman danne dannan wayarta tayi tsaki tare da wurga wayar kan kusun tana fad’in.
“Aikin banza!, Wallahi Mama ke ki ke yarda da aikin wasu bare, ni da kin yarda da tuni anyi komai ya wuce munriga munsan matsayar da muke”.
Fulani tayi murmushi tare da fad’in.
“Jalila kenan !, Ke fa yarinya ce har yanzu , amma bazank’i ta taki ba, me kike ganin zaki wanda bazamu iya ba?”.
Jalila gyara zama tayi tana fuskantar Mahaifiyarta sosai.
“Yauwa Momy abin da ya kamata ki ce kenan tun d’azu, ki bani kwana biyu cikin kwanakin tabbas zan samo maki takun k’afar Fudhal”.
“To amma ta yaya?”.
“Momy…! Ke dai kawai ki zuba ido”.
“Bawai nak’i ta taki ba ne, inajin tsoron al’amarin ne kawai, amma dai kiyi komai cikin nutsuwa da taka tsan-tsan, domin kinfi kowa sanin yanda Fudhal da d’an’uwanki suke, ban-bancin kamanni ma kad’anne haka wajen kayansu zuwa takalmi kinsan abune da sai mutum ya lura sosai da kulawa sabida ka da a samu miskila”.
“Haba Momy…!, Ni har sai anmin wannan baya ni, idan ni ban iya tan-tance Fudhal da Jalil ba waye zai gane?”.
“Uhmm to haka ne kuma Jalila”.
“Yauwa wai Mama ina Jalil kuwa?, kusan 2week fa kenan bana ganinsa cikin gidan nan?”.
Fulani tayi ajiyar zuciya tare da tab’e baki tana fad’in.
“Ni ina zan sani Jalila..! komai ina yi ne domim gobenku, amma shi baya fahimta kullum al’amarin nasa k’ara gaba yake yi, shi da ya kamata ace yana girma yana hankali amma ina…!, waye zai yarda abashi ragamar Sarauta a cikin wannan halin nasa?”.
“Ka da ki damu Momy komai zai dai-dai ta”.
“Fatana kenan Jalila”.
***
Dawowarsa kenan daga asibiti lokacin kusan k’arfe biyar da mintuna na yamma ya zauna gaban Fulani Bingel tare da fad’in.
“Wash Hajiya wallahi nagaji yau sosai”.
“Kai dai ka shigesu da lalaci kamar ba namiji ba?”.
“Namiji baya hutu kenan Hajiya?”.
“Ni dai bance ba, amma kai kullum ka dawo wash ne sallamarka cikin falon nan tun da ka fara aiki”.
Yarima Fudhal yayi murmushi wanda ya baiyana hak’oransa waje, amma daka kalli fuskarsa zaka san yana k’ok’arin danne damuwar da ke kwance bisa fuskarsa ne.
“Au.. Magaji ai kuwa zama bai ganka ba, yanzu akayimin waya Sadiya ta haihu “.
“Masha Allah mai ta haifa Hajiya?”.
“Yan biyu ne aka samu mace da namiji”.
“Allah ya rayasu yanzu kuwa zanje, fatan tana lafiya dai ko?”.
“Lafiya k’alau ta haihu har an sallamesu daga asibitin sun koma gida”.
Yarima Fudhal ya mik’e yana fad’in.
“Bari inje inshafo maki kan jikokin naki”.
“Ko dai kaje ganin ‘ya’yanka dai?”.
Nan ma dariya sukayi a tare, tana bashi sallahun ya gaishe da su tare da mik’a masa wata k’atuwar leda fara ta ce ya kai mata, Yarima Fudhal ya amsa ya fice, Fulani Bingel ta bishi da fad’in.
“In kaje ka samu kaci abinci dai”.
Ya amsa da “to Hajiya”.
Bayan fitarsa Fulani Bingel murmushi tayi a fili take fad’in.
“Ina ruwan Magaji…! shi dai yana son yara sosai, Allah dai ya nunamin ranar da zanga naka yaran kai ma”.
Baki har kunne ya shiga cikin gidan, da sallama ya sanya kai cikin falon mijinta ne zaune shi da yaransa guda biyu mata kusan kansu d’aya ga kuma mugun kama da suke yi, yaran tubarkalla gasu da kyau, da gudu yaran suka taso suna fad’in.
“Oyoyo Uncle..!”.
Suka rungumeshi ya tsunna ya rumgumosu jikinsa yana fad’in.
“Saleema da Saleena anyi k’anne kuma baki ba rufuwa”.
Dariya suka yi atare suka sumbaci kumatunsa, shafa kansu yayi yana fad’in.
“Nagode yara na !”.
Ya mik’e ya k’arasa wajen Baban nasu suka gaisa, yana tambayarsa .
“Ina Maman tasu?”.
“Suna ciki ka shiga ku gaisa mana”.
Yarima Fudhal ya kama hannun yaran suka shige cikin d’akin, Aunty Sadiya na kwance bisa gado sai jariran agefan ta, gefe guda kuma Aunty Sa’ida ce da wasu mata su biyu, suka gaisa da matan suka fice.
Yarima ya gaishe dasu Aunty Sadiya ya d’auki yaran yana mai k’are musu kallo, kafin yayi murmushi yana duban Aunty Sa’ida.
“Aunty na sai nakejin yaran nan kamar Aynu d’ita ce ta haifamin wallahi, shi yasa Hajiya na gayamin na kasa daurewa sai nazo na gansu”.
Aunty Sa’ida ta tab’e baki kawai tana dubansa cike da takaicin maganar da yayi.
“Au wai kai har yanzu baka bar maganar yarinyar nan ba?”.
Cewar Aunty Sadiya kenan tana daga kwance.
“Taya kuwa zan barta Aunty na, baki san yanda nake jinta ba a cikin raina Allah”.
“Sai kayi kuma, iska na wahal dame kayan kara”.
Aunty Sa’ida ta fad’a tana mai jan hannuwan Saleema da Saleena suka fice daga d’akin, Yarima Fudhal ya bita da kallo ko kad’an bayajin dad’in yanda take yi masa akan Aynu, Aunty Sadiya ta dafa hannunsa tana fad’in.
“Kar ka damu k’anina, komai zai wuce soyayyarka ta gaskiya ce insha Allahu zaka sameta idan har matar kace, idan kuma Allah bai k’addara matar ka bace kayi hak’uri kaji sai Allah ya musanya maka da mafi alkhairi”.
Yarima Fudhal murmushi yayi cike da jin dad’in maganar Auntyn tasa, bai ce komai ba illa mai da kallonsa kan ‘yan Jariran da yayi yana mai kai musu kiss a goshinsu cike da so da k’auna sosai yakejin yaran cikin ransa.
Hello
Kuyi hak’uri da wannan dan Allah babu yawa rashin chaji yaja nayi muku typng kad’an dan kada kuji ni shiru.
Nagode sosai da sosai masoyana kuna raina ko da yaushe.
*YARIMA FUDHAL*
Na
FIRDAUSI S.A(QURRATUL-AYN).
NAGARTA WRITERS ASSOCIATION®
SADAUKARWA:-Namesy Phirdauceey Jeebour.
28
“Wannan shine gaskiyar abin da ya faru, please Baba..! Dan Allah ka taimaka kajanye hukuncin da ka d’auka, ka san gaskiyar abin da ya faru yanzu wallahi Yarima yana son ‘yarka da gaske so na tsakani da Allah”.
Baban Aynu shiru yayi kansa na k’asa, tsayin lokaci ya shafe yana tunani kafin ya d’ago kansa ya kalli Anwar dake zaune yana jiran yaji amsar da zata fito daga bakinsa.
“Yaro kayi hak’uri kuje ku sake wata shawaran wannan ba zata samu karb’uwa ba, domin nasan ka zo ne da silar yaudara kamar yanda kuka zo da farko”.
“Baba wallahi dukkan abin da na fad’a a yanzu gaskiya ne, idan da farko munzo da yaudara wallahi tallahi Allah d’aya ne Baba bazan yi rantsuwa akan k’arya ba dukkan abin da na fad’a a yanzu babu haufi a cikin sa”.
Shiru ne ya sake biyowa baya kafin Baban Aynu yace.
“Shikenan kaje zan neme ka”.
Anwar yayi godiya tare da mik’ewa ya bar wajen zuwa cikin motarsa ya tada ita ya bar bakin kasuwar, Baban Aynu ya shafe tsayin lokaci zaune yana nazari a kan maganar da Anwar ya sanar da shi yanzu, kafin ya mik’e ya nufi gida zuciyarsa cike da wasi-wasin al’amarin.
***
“Kayi farin ciki Yarima na sanarwa Baban Aynu gaskiya da dukkan alamu kuma ya yarda damu yanzu, ya kayi tsaye kana kallona baka farin ciki ne?”.
Yarima ya ajiye wayarsa dake rik’e a hannunsa kan table d’in gabansa ya dubi Anwar cike da kulawa kafin ya fara magana.
“Me zance to Anwar?, zai nememu fa kawai ya ce da kai, inajin tsoron abin da zai biyo baya ne, kana da tabbacin ya yarda da abin da ka gaya masa?”.
“Ehh mana, ya kamata kayi kyakykyawan zato Yarima”.
“Hakane nagode sosai Anwar”.
“Haba dai mene abin godiya kuma?, ai ana tare”.
***
Baban Aynu ne zaune bisa tabarma da Umma a zaune gefansa suna tattaunawa kan batun Aynu da Ya Sayyadi.
Baba ya dubi Umma cikin kulawa ya ce.
“Ya kamata a ce da Umar ya fito ayi magana, ko ya kika gani Umman Aynu?”.
“Haba dai Malam..! Me zai hana a d’an k’ara kwana biyu, kana ganin yarinyar nan fa yanda ta koma har yanzu ta kasa mai da walwalar jikinta”.
“Ehh haka ne, amma ni ma a son raina dama ba yanzu ba, to wancan yaron ne ke neman canjamin a kalar maganata ne, kinga idan aka riga akayi baikon ya hak’ura ai”.
“Haka ne kuma, amma malam kamarya yana neman canja akalar maganarka?”.
“Ehh to d’azu a kasuwa a bokinsa ya zomin da maganar dukkan abin da ya faru a shekarun baya, ba na so tausayin yaron yayi tasiri araina incanja maganata”.
Nan dai ya kwashe komai ya sanarwa Umman Aynu, Umma ajiyar zuciya tayi tana fad’in.
“Allah sarki yaban tausayi sosai wallahi, a she ba shi da laifi laifin duk na mahaifinsa ne?, yanzu mai ka yanke akan hakan?”.
“Maganata babu canji Aynu Umar zata aura, domin shi yafi dacewa damu da rayuwarta, yaron d’an mutunci wanda ya san mutunci taya zamuyi sake ya sub’uce mana a matsayin suruki?”.
“Gaskiyarka Malam domin duk wata uwa ta gari burinta ‘yarta ta auri miji nagari, haka kuma duk wata uwa ta gari burinta d’anta ya auri mata tagari, nima har cikin raina Umar ne zab’ina”.
Aynu dake zaune cikin d’aki duk tana jin tattaunawar da iyayenta keyi, tana faman share kwallar dake zubo mata bisa kan fuskarta a fili ta furta.
“Yanzu ya zama dole inkoyawa zuciyata son Ya Sayyadi Umar, kamar yanda ya zamana dole in fidda son Yarima a cikin raina..!?”.
Ta kifa kai bisa tabarmar da take zaune a kai tana shash-shek’ar kukan da babu mai lallashinta.
BAYAN KWANA UKU.
Zaune yake a office d’insa kamar kullum yayi nisa cikin tunani sosai, ya yin da k’asan zuciyarsa keta faman azal-zalarsa da son ganin Aynu, har sai da ya kasa jurewa bare ya iya sarrafa kansa wajen bawa zuciyar tasa hak’uri.
Ya d’ago jajayen idanuwansa dai-dai lokacin da agogon office d’in ya buga k’arfe shida da ‘yan mintuna, sai lokacin ya san irin dad’ewar da yayi a zaune yana aikin tunani, tattara komai yayi ya mayar inda yake ya fice da sauri zuwa wajen motarsa ya tayar da ita ya fice daga cikin harabar asibitin.
Kai tsaye gida ya nufa bai tsaya ko ina ba sai cikin d’akinsa yana shiga ya fad’a toilet y sakarwa kansa sassanyan ruwan shower, wai dan ya d’anji sanyi a ransa amma duk da haka bai samu yanda yake so ba.
Fitowa yayi bayan ya d’auro alwala ya ta da sallar maghriba domin lokacin anata kiraye-kirayen sallar shi kuma baijin zai iya zuwa sabida yanda yake jin jikinsa, ya jima kan sallah yana jero tarin addu’o’i wanda zan iya cewa addu’artasa duk a kan Aynu ce, sai a lokacin ya d’anji dama-dama a cikin ransa.
Yana shafawa ya janyo wayarsa ya kira number Anwar amma switchoff hakan yasa ya wurga wayar kan katifa ya mik’e ya shirya cikin k’ananun kayan riga T.sheet fara da adon bak’i a jikinta sai ya sanya bak’in wando jeans bai damu da ya gyara sumarsa ba kamar yanda ya saba ya d’auki key d’in motar ya fice daga gidan.
Duk a bin da yake Jalila na lab’e tana kallonsa, domin yau taci alwashin sai ta samu abin da take so, har sai da ya fice sannan ta fito daga mab’oyarta ta koma part d’insu tana zaman jiran dawowarsa.
A k’ofar layin nasu ya tsaya yayi parking ya fito ya kulle motar ya taka har zuwa k’ofar gidansu unguwar shiru kamar anyi shara ya shafe tsayin lokuta a tsaye amma babu ita babu labarinta kuma ya rasa wanda zai aika zuwa gidansu, domin yau yaci alwashin kome zai faru sai yaga Aynunsa.
Yayi nisa cikin tunani yaji ana fad’in.
“Lafiya dai Yarima?”.
D’ago kai yayi da sauri domin a tunaninsa Aynu ce sai dai yaga sab’anin haka Zainab,murmushi ya saki wanda bai wuce kan leb’ansa ba yana fad’in.
“Alhamdulillahi gara da Allah ya kawo ki”.
“Lafiya wani abun ya faru?”.
“A’a babu komai, kawai dai wani taimako nakeso kimin dan Allah”.
“Taimakon me fa?”.
“Ki fitomin da Aynu “.
Zainab ajiyar zuciya tayi kafin ta ce.
“Ai kuwa Aynu bana jin zata fito yanzu, dama dai kayi hak’uri kuma kasan a gida ma ba za’a bari ta fito ba”.
“Please dan Allah ki taimake ni”.
Yayi maganar kamar zai yi kuka, sosai tausayinsa ya kama Zainab ta ce.
“To jira mugani Allah yasa ta fito”.
Ta juya ta shige cikin gidan ta bar Yarima nan tsaye yanata zuba addu’o’i cikin ransa akan Allah ya taimake shi ta fito.
Kusan mintuna goma sha biyar suka shud’e ba amo babu labarinsu can dai kamar ance d’ago kanka ya gansu sun fito tare Aynu na faman turjewa Zainab na rok’onta, cikin d’acin rai Aynu ke fad’in.
“Kema kin koyi mumafunci ko?, ki ka cemin Ya Sayyadi ne”.
“Yi hak’uri dan Allah ki saurare shi”.
Aynu ta dubi inda Yarima yake shek’ek’e ta buga tsaki ta juya zata koma, Yarima yayi saurin kamo hannunta tare da shan gabanta yana fad’in.
“Kiyi ha’uri dan Allah ki saurare ni”.
Yayi maganar cikin sanyin murya, Aynu ta tsaya tana kallonsa kawai nan suka hau kallon kallo tsayin wasu lokuta kafin Aynu ta fizge hannunta tana yi masa wani irin kallo daya kasa fassara kona mene.
Tsaki taja kafin tace.
“Ka b’acemin da gani Yarima..! Na tsaneka..! Bani son ganinka ko kad’an acikin rayuwata domin ka jiwa zuciyata ciwon da banajin akwai maganin warkewarta, me ya sa..! Me yasa…!! Me yasa Yarima?”.
Sai kawai ta fashe da kuka, sosai Yarima kejin kukan Aynu har cikin zuciyarsa, a hankali ya cire hannunsa da ke cikin aljihun wandonsa yakai hannun da niyar share mata hawayen sai kuma ya sauke hannun da k’yar yayi k’arfin furta.
“Kiyi hak’uri Aynu…!, Ki sani ina sonki har cikin raina wallahi, dukkan abubuwan da suke faruwa har yanzu ban fidda rai da ke ba, domin inajin a raina ke tawace har abada kuma zamu rayu tare, amma yau she ne wane lokaci ne abubuwan zasu dai-daita ban sani ba?”.
Aynu ta d’ago jajayen idanuwanta tana kallonsa cike a takaijin jin maganar da yake yi.
“Kama daina wannna mafarkin, domin Aynu nan da wasu watanni matar wani ce, kalamanka banjin zasuyi ta siri a raina Yarima, kamar yanda kuka so yi da farko sai dai Baba ya taka muki burki, to nima inaso kamanta da ni…!”.
Kafin ta kai ayar maganarta sai ganin Yarima Fudhal tayi tsugunne a gabanta bisa gwiyoyinsa idanuwansa fal da hawaye.
“Kiyi hak’uri dan Allah da Annabinsa nasan nayi kuskuren da babu abin da zanyi domin gyaransa amma ki sani Aynu babu wani bawa da zai iya kaucewa k’addararsa, nasan na zalunce ku ke da iyayenki amma ki sani komai muk’addari ne daga Allah, dan Allah ki janye daga batun auren wani bani ba, Aynu inasonki wallahi zan iya rasa raina Ayn…!”.
“Naji kana so na..!, amma duk kai kaja dukkan abubuwan nan suke faruwa, Babana bawai yana da burin d’aukan fansa bane, haka ni ma bana da burin fansa cikin raina, amma me yasa Yarima kayanke shawaran azurtamu da kud’inka kamance Allah ke azuratawa ba bawa ba, kai ma da kuke tak’ama da kud’i da mulkin ai duk Allah ne ya baku ayau in yaso sai ya karb’e abinsa, mai yasa kazo wajen Baba da fuska biyu?, mai yasa baka zo kanka tsaye ba domin kafuwar soyayyar da kakemin idan har gaske ne?, ina ji a raina bani kake so ba akwai dai abin da kake so, domin idan har ni kake so ba zaka yi tunanin amfani da kud’i ba zakayi ne domin yak’ini da zuciyarka”.
Yarima kamo hannun Aynu yayi yarik’e k’am ba tare da ya lura da hakan da yayi ba.
“Ki fahimce ni Aynu, sonki shine yafi tasiri a zuciyata fiye da komai, sonki ne ya sanya zuciyata ta rufe, tunani na ingyara kuskuren da nayi, amma mai makon in gyara sai in k’arawa kaina wani laifin ba tare da nasan hakan ba, ki ga farce ni dan Allah ka da kiyar da ki auri wani ba ni ba Aynu zanyi k’ok’arin ganin na gyara kuskure na…!”.
“Taya zaka gyara kuskuren naka?, Kuskure ka riga kayi ai sai dai ka kiyaye gaba , amma ka sani har yau ba zan dai na fad’a maka ba, gobe za’ayi bai kona da Ya Sayyadi nan da watanni ni mata ce a gare shi, ina so ka manta da ni kasa wa ranka tamkar mafarki na kayi ka farka…!”.
Aynu ta fizge hannunta ta shige gida da gudu tana kuka, Yarima zaman dirshan yayi a wajen zuciyarsa na zafi da k’una, har ya naji dama Allah ya d’auki ransa a dai-dai wannan lokaci akan yana ji yana gani Aynu ta auri wani ba shi ba, duk abubuwan da suke faruwa Zainab na gefe tana kallo har sai da suka sanyata zub da hawaye ita ma.
Yarima da k’yar yayi k’arfin halin mik’ewa yana jan k’afa cike da tangad’i kamar wani d’an shaye-shaye ya bar layim gidansu Aynu zuwa inda yayi parking motarsa ya bud’e ya shiga ya zauna tare da kifa kai bisa sitiyarin motar.
*YARIMA FUDHAL*
Na
FIRDAUSI S.A(QURRATUL-AYN).
NAGARTA WRITERS ASSOCIATION®
SADAUKARWA:-Namesy Phirdauceey jeebour.
29
Ya shafe tsayin lokaci a zaune a cikin motar ya rasa abin da yake masa dad’i cikin duniya, ji yayi baki d’aya bazai iya driven ba hakan yasan yashi fara lalub’en wayarsa domin kiran Anwar ko Jalil wani yazo ya d’aukeshi amma sai bai ganta ba, sai can ya tuna yabarta agida.
Da k’yar ya iya sanyawa motar key ya kunnata tare da barin layin gidan nasu Aynu.
A wannan lokaci Allah ne kad’ai ya kai Yarima gida lafiya, domin tun kafin ya kai ga k’arasawa yaji idanuwansa na dishi-dishi har dai yayi parking a harabar gidan ya kashe motar kawai ba tare da ya cire key d’in ba ya nufi part d’insa, yana shiga falo kuwa ya zube k’asa lokacin agogon da ke falon ya buga k’arfe sha biyu da rabi dai-dai, da rarrafe ya k’arasa cikin bedroom d’in zuwa wajen drower da yake adana magungunansa ya nufa ya d’auko ya fara had’iyarsu d’aya bayan d’aya ba tare da ruwa ba, sai da ya tabbatar ya gama had’iya sannan ya rarrafa ya d’auko gorar ruwan faro mara sanyi ya sha, a wajen ya zube a kwance.
Tsalle tayi tare da fad’awq kan cinyar Fulani Sokoto tana fad’in.
“Na samo Momy na samo burinmu zai cika Momy”.
Cike da murna da garin ciki Fulani Sokoto ta karb’i k’unshin k’asar dake d’aure hannun Jalila tana fad’in.
“Alhamdulillahi…! lallai Jalila kin cika ‘yata nayi murna sosai wallahi, ai da nasan zaki iya da tun farko aike zan sanya aikin”.
Jalila tayi murmushi cike da jin dad’in kalaman yaban da Mahaifiyarta ke yi mata.
Sun shafe tsayi lokaci suna hira kafin Jalila ta mik’e ta nufi d’akinta tana fad’in.
“Asuta gari Momy”.
“Mu tashi lafiya Jalila”.
Ta shige d’akin ta bar Fulani Sokoto zaune falon cike da murna harta matsu taga gari yawaye .
Aynu kuwa tana shiga gida d’aki ta wuce da gudu ta zube kan katifar dake yashe tsakar d’akin tana shash-shek’ar kuka, a haka Ummanta ta tadda ita ta zauna zaman lalashinta, Aynu ta d’ora kanta kan cinyar Umman ba tare da ta ce komai ba, illa sharar hawayen da take kawai Ummanta na aikin bata hak’uri.
Zainab ita dai daga wajen bata koma gidansu Aynu ba gida ta koma jikinta yayi sanyi sosai tausayin Yarima yake kamata domin ita ayanzu tafi jin tausayinsa akan Aynun.
“Wayyo Allah na Momy…!”.
Jalila ce ya farka daga bacci agigice sai faman zufa take baki d’aya ta rud’e, Momy da ke zaune falo har lokacin ba tayi bacci ba ta shigo d’akin da gudu tana fad’in.
“Lafiya Jalila..!, Mai ya faru?”.
Jalila dake faman muzurai ta k’ank’ame Fulani Sokoto tana zubar hawaye.
“Kinga dan Allah karki damu mafarki kikayi ne?”.
Jalila ta gyad’a mata kai domin ta kasa d’aga harshenta bare harta furta wata kalma.
“Aiba komai bane yi shiru kinji, mafarki ba gaskiya bane maza koma kiyi baccin ki babu abin da zai faru”.
Fulani ta kwantar da ita tare da rufa mata bargo tana fad’in.
“Kiyi baccinki ‘yata karki damu, da safe mayi magana”.
Ta juya ta fice daga d’akin tare da ja mata k’ofa ta rufe, Jalila ta kalli inda agogon d’akin yake kafe agogon ya nuna k’arfe uku da ‘yan mintuna na dare, amma sam Jalila ta kasa komawa baccin da take sosai tsoro yake ratsata tasan da wuya Mahaifiyarta ta fahimceta.
“Meke shirin faruwa ne?”.
Ta furta hakan cikin ranta tare da mik’ewa zaune tana karanto addu’a cikin ranta.
Yarima kuwa tun da yayi wannan zubewar ya kwanta bai tashi farkawa ba, sai da garin Allah ya waye kusan k’arfe goma na safe ya bud’e ido tare da k’arewa d’akin kallo ya sauke dubansa kan Anwar dake zaune gefansa ga kuma Doctor Mansur yanata faman aunashi.
K’ok’arin mik’ewa Yarima Fudhal ya hauyi hakan ya saka suka fahimci ya farka, kamashi sukayi tare da jinginashi jikin pillow, Doctor Mansur ya zauna gefansa yana k’aremasa kallo kafin ya bud’e baki ya fara magana.
*YARIMA FUDHAL*
Na
FIRDAUSI S.A(QURRATUL-AYN).
NAGARTA WRITERS ASSOCIATION®
SADAUKARWA:-Namesy Phirdauceey Jeebour
30
Am so sorry abisa jina da kukayi shiru kwana da yawa wlh fever ya rik’eni…amma yanzu Alhmdlh ngd sosai da call naku zuwa text message ubangiji Allah yabar kauna amin kuna raina any time ana mugun tare.!
***
“Haba Yarima ka da ka mance kaima Doctor ne?, amma ya kake k’ok’arin jawa kanka matsala ne?, ka fini sanin illar da ke tattare da ciwonka fa…!, Please Yarima kayi k’ok’arin cirewa kanka damuwar da ke tattare cikin zuciyarka tun da wuri domin kana dab da fuskantan babbar matsala?”
Yarima Fudhal bai ce komai ba illa kafe Doctor Mansur da yayi da shanyayyun idanuwansa babu ko k’iftawa, Anwar ne ya dubi Doctor Mansur cike da kulawa yana fad’in.
“Insha Allahu zamuyi k’ok’arin kiyayewa Doctor zan fahimtar da shi da yardar Allah komai zai yi normal”.
“Ok babu damuwa tun da kai ka fahimce ni zaka iya fahimtar da shi, Allah ya k’ara lafiya ni zan koma?”.
Sukai sallama da Anwar ya fice daga d’akin ba tare daya sake duban Yarima ba.
Yana fita aka sake turo k’ofar Yarima Jalil ne ya shigo cikin shiga irin ta Yarima Fudhal farar T.sheet da bak’in wando Jeans har adon rigar da komai iri d’aya.
Zama yayi a gefan da Fudhal ke kwance bayan ya mik’awa Anwar hannu sun gaisa yana fad’in.
“Ya dai Bro bakajin dad’i ne?”.
Yarima Fudhal ya gyad’a masa kai alamun E .
“Ayya am sorry..! Jalila ma nacan kwance da alamu ko magana bata iyayi amma ta matsa a kirawo mata kai”.
Yarima Fudhal ya kafe Jalil da ido yana fad’in.
“Meke damunta?”.
“Waya sani?, Momy dai ta ce tun dare ne tayi mafarki shikenan take ta aikin kuka har safe bata koma bacci ba, amma kuma tak’iyin magana “.
“Subhanallahi…bari intashi muje to !”.
Yarima Fudhal ya mik’e da k’yar suka fito daga d’akin dukansu a hanyar zuwa part d’in Fulani Sokoto ne yake tambayar Yarima Jalil.
“Wai kai ina kake zuwa ne? ina lura da kai kusan 2week kenan baka gidannan, yaushema ka dawo ne?”.
Yarima Jalil sosa k’eya yayi tare da wata ‘yar guntuwar dariya.
“Naje hutu ne kawai, jiya da dare na dawo na shiga d’akinka baka nan ai”.
Yarima Fudhal ya watsa masa wani mugun kallo kawai ya d’auke kansa, a can k’asan ransa bak’aramin ciwo yakeji ba akan munanan halayen Jalil bai san meya sa baki d’aya ya gama lalacewa shine shaye-shaye neman mata duk ya had’a kamar ba jinin sarauta ba?.
Suna shiga falon babu kowa kai tsaye d’akin Jalila suka nufa da sallamarsu Momy ce zaune gefan Jalila ita ce ma ta amsa musu sallamar, dukansu suka gaisheta tare da tambayar jikin Jalila, ita kuwa Jalila tun da suka shigo take bin Fudhal da Jalil da wani irin kallo kamar yau ta fara ganinsu.
Yarima Fudhal ya zauna gefanta yayin da Anwar da Jaleel suka nemi gefe guda suka zauna Momy ta mik’e ta fice daga d’akin.
Fudhal ya rik’o hannunta yana fad’in.
“Ya jikin naki?”.
Kai kawai ta gyad’a amma babu bakin magana.
“Bakya iya magana ne?”.
Nanma kan ta sake d’aga masa.
Yarima Fudhal shiru yayi kawai yana dubanta tausayin k’anwar tasa ya kamashi yama rasa mai ya kamata yayi mata?.
Mik’ewa yayi ya fito daga d’akin zuwa falo dai-dai lokacin da Momy ke fad’awa Larai baiwarta.
“Kiyi maza ki kai masa sak’on dan Allah bana son a samu kuskure kice a yi aikin cikin gaggawa dan Allah…!”.
Maganarta ta katse dai-dai sanda Fudhal ke fitowa zuwa falon, Fulani Sokoto tayi wani mayaudarin murmushi tana fad’in.
“Har ka fito Magaji?”.
Fudhal ya nemi guri ya zauna ba tare daya bata amsa ba, Larai kuma tamik’e da sauri ta fice daga d’akin.
“Momy ta fad’a miki abin da tayi mafarki ne?”.
“A a nidai ihunta kawai naji cikin dare ina shiga d’akin na lallasheta tayi bacci na koma d’akina da nufin da safe na tambayeta amma da safen duk yanda naso tabud’e baki tayi magana amma abu ya faskara”.
Yarima Fudhal yayi shiru nad’an wani lokaci kafin yace.
“Bari musan abinyi to a tafi da ita hospital d’inmu domin akwai kayan aiki sosai, zamu gano inda matsalar take”.
Fulani Bingel ce tayi sallama dai-dai wannan lokacin Fudhal ya amsa fuskarsa fal murmushi ya durk’usa ya gaishe da ita, suka gaisa da Fulani Sokoto tana tambayar.
“Ina mai jikin?, naji ance Jalila ba taji dad’i ba”.
“E tana d’aki “.
Cewar Fulani Sokoto kenan, Fulani Bingel ta mik’e ta nufi d’akin yayin da Fudhal da Fulani Sokoto suka take mata baya.
“Allah sarki !, Sannu kinji Jalila Allah k’ara sauk’i”.
“Amin”.
“Amma mene yake damunta?”.
Fulani Sokoto ta d’anyi dariya tare da bata amsa.
“Mafarki ne tayifa shine baki d’aya ta koma haka”.
“To a san abinyi tun da wuri mana”.
Fudhal ne yayi saurin bata amsa a wannan lokacin.
“E muna kanyin hakan kika shigo, nace a kaita hospital namu sai induba inda matsalarta take”.
Fulani Bingel ta gyad’a kai tare da mik’ewa suka fito daga d’akin dukansu, tayiwa Fulani Sokoto sallama ta fice daga part d’in yayin da Fudhal da Anwar suka tako mata baya.
Sai da suka raka ta har cikin falonta sannan suka fito suka koma d’akin Fudhal domin ya d’an kwanta ya huta sabida shima ba lafiyarce gareshi ba.
Kwanciya yayi bisa carpet tare da d’ora kansa kan kusun, Anwar ya zauna kusa da shi yana mai k’are masa kallo kafin ya bud’e baki ya fara magana.
“Wai Fudhal mene matsalarka ne?”.
Fudhal ya bud’e ido a hankali tare da saukesu kan fuskar Anwar yana mai jifansa da wani guntun murmushi da bai wuce kan leb’ansa ba.
“Tambayarka nake, wai ina kaje ma jiya da dare ne?”
“Wajen Aynu”.
Ya bashi amsa a tak’aice.
“To amma meye dalilin tashin ciwonka, kasan a halin da nazo na tadda kai kuwa?”.
“Koma a wanne yanayi ne nasan zaka iya tadda ni, sabida abin da ya faru ajiya bana sonma ina tunashi ko kad’an”.
“Aynu da bakinta tace bata sona ta tsanane ita bazata aure ni ba, tariga ta tsai da wanda zata au…!”.
Maganar ta mak’ale a mak’oshinsa sabida numfashinsa da ke barazanar d’aukewa, hakan ya sanyashi yin shiru ya mai da idonsa ya rufe yana fitar da wani irin numfashi mai zafi.
Sosai tausayin Fudhal ya kama Anwar sai binsa da kallo kawai yake, mutumin da in banda Mahaifiyarsa bai d’auki mace wani abuba arayuwa, yau gashi mace na wahalar da shi kuma macen ma ba ‘yar gidan kowa ba ‘yar talakawa, shi da ya d’auki soyayya kamar shirme ko hauka yau gashi a kanta yana neman rasa rayuwarsa, dama bahaushe yace komai lokaci ne abin da kake rainawa wata rana shine zai baka tsoro.
Yarima Jaleel ne ya shigo falon yana fad’in.
“Broda anshirya Jalilah inji Momy”.
Sai lokacin Fudhal ya sake bud’e idonsa daya kad’a yayi jajir ya dubi Jaleel tare da fad’in .
“Ku wuce kawai zan biyoku a baya”.
Jaleel ya fice daga d’akin cikin sauri domin jiransa suke a mota.
Bayan fitar Jaleel Yarima ya shafe tsayin lokuta ba tare daya mik’e ba, da k’yar dai ya mik’e ya shige bedroom nasa domin ya d’an watsa ruwa yabar Anwar zaune a falo.
Cikin mintuna kad’an sai gashi ya fito cikin k’ananun kaya duk da cewa ba wani tsayawa yayi yin gwalli ba hakan bai hana kyawunsa da b’oyayyar damuwar dake kwance k’asan fuskarsa baiyana ba, Anwar ya jefawa key d’in mota tare da fad’in.
“Tashi mu tafi”.
Anwar bai ce komai ba yamik’e yabi bayan Fudhal don shi tuni yayi waje abinsa.
Suna isa asibitin Jaleel da Momy na zaune zaman jiran zuwansa, bai tsaya wani b’ata lokaci ba ya nufi d’akin da aka kwantar da Jalilah domin gwajin da za’ayi mata.
Sun shafe kusan a wanni uku zuwa hud’u duk abin da ya kamata ayiwa Jalilah anyi amma hakan bai sanya angano takamai-mai abin a yake damunta ba, abin da result ya bayar kawai maleria ke damunta.
Ko da Fudhal ya fito ya had’a zufa sosai ga kuma kansa dake matsanancin sara masa, bai bi takansu Momy ba kawai office nasa ya wuce yana goge gumin da ke tsatstsafo masa, ya zauna kan kujera tare da k’aro sanyin A.C da ke office d’in, ya kwantar da kansa kan kujerar tare da lumshe ido yana aikin daya saba.
Turo k’ofar da a kayi ne tare da kiran sunansa ya sanyashi d’ago kai yana mai k’are masu kallo, Anwar da Jaleel suka zauna akan kujerun da ke gaban table d’in Yarima suna mai binsa da kallo suma.
“Lafiya Yarima ya jikin Jalilan?”.
Anwar ya jefa masa tambaya, Yarima ya gyara zamansa tare da janyo file d’in Jalilan yana dubawa can ya rufe yana mai mayar da kallonsa kansu.
“Al’amarin ne yake d’auremin kai Anwar duk iya binciken da mukayi maleria kawai result yake bamu”.
Fudhal yayi maganar murya a sanyaye, Jaleel ya gyara zama sosai yana fad’in.
“Maleria kuma?, ba’a gano dalilin da yasa bata magana ba?”.
“Wallahi munyi iya yinmu Jaleel nima abin da yake damuna kenan”.
Shiru ne ya biyo baya kafin Anwar yace.
“Kuma ban da maleria babu wani ciwo da ke damunta?”.
“E”.
“Abin da mamaki fa?”.
Cewar Jaleel ya fad’a tare da mik’ewa yana mai cigaba da fad’in.
“Bari inje insanarwa Momy to”.
“Zaku iya wucewa da ita gida, nima yanzu zan tawo domin nafara jin fever wallahi”.
“Ok Allah yak’ara lafiya sai kun dawo”.
Ya fice daga office d’in ya barsu.
KUYI HAK’URI DA WANNAN.
NAGODE SOSAI DA SOSAI MASOYANA MASU BIBIYAR LITTAFINA INA K’AUNARKU NIMA HAR A ZUCIYATA.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button