NOVELSUncategorized

BARIKI NA FITO (BOOK 2) 12

BOOK 2
                   PAGE 12

Idonta na kanshi ganin dagaske yake zai iyayi mata komai yasa tayi gaba tare da tsayawa wajan kofa tace Yarima nika saka?  Auren dako wata d’aya baiyi ba amma ace harka sakeni? Lallai kayi babban kuskure a rayuwanka

daka furta min wannan Kalman, sannan inaso ka jira Kaga Mai zai biyo baya tunda har ka karya wannan dokar ta masarauta….. Fuuuuuu ta fita

Yarima Aliyu yace mad girl tare da saka, saka jallabiya ya kwanta danya huta domin yayi matukar gajiya gashi wannan matar tashi ta kara jagula Mai lissafi, yana kwanciya yaji Phne dinshi na ruri kallon wayar yayi tare dakai hannunshi kan wayar, Sunan Mai martaba ya gani, d’auka yayi ban San mai mahaifin nashi yace mishi ba naga yace gani nan zuwa…..
Tashi yayi ya canza kaya sannan ya nufi gefen mahaifin nashi inda yaga mum dinshi damai martaba a cikin bedroom dinshi…..  Yana kokarin gaida mahaifin nashi Kafin ya karasa sai saukan Mari yaji tas tas har guda biyu abunda ba’a taba mishi ba tunda ya taso gashi yau mahaifin nashi yayi mishi….. 
Cikin fushi da bacin  rai Mai martaba yace ka zubar min da k’ima, saki cikin wannan masarautar?? Bayan kasan sai an Kama mutum ya aikata laifi biyu ake saki????
Yarima Aliyu yace Abba Ina Mai neman gafaran ka, Abba zagin iyay……. 
Mai martaba ya daka Mai tsawa Wanda ba Yarima ba harta mum dinshi saida ta tsorata da irin tsawar damai martaba yayi ma Yarima Aliyu……. Yace na baka umarnin Ka maida matarka, sannan daka yau Indai harka K’ara Karya wannan dokar ban yafe maka ba duniya da lahira…..  A haka kake kokarin K’ara aure??? ….. Mata d’aya ma ka kasa da ita ko wata d’aya bakayi da itaba amma har Kalman saki ya shiga?? Am really dissapointed with you…… Ina son daka yau kaje ka zauna kaida matarka karka K’ara taso da maganan auranka dan banga alaman zakai adalci ba ko kad’an……  Sannan wannan al’adan daka karya saina hukunta ka, kaje kaida kanka kasa a rufeka sai kayi sati biyu Kafin ka fito mutumin banza……
Tunda Mai martaba ya fara magana kan Yarima Aliyu na k’asa, har Mai martaba ya kammala, sannan Yarima Aliyu ya fara magana da fad’in Allah ya huci zuciyar Mai……  Dakatar dashi Mai martaba yayi tare da fad’in tashi kaban waje……. Ban son jin komai daka gareka….
Yarima Aliyu jiki a sanyaye ya tashi ya fita direct cikin kurkukun masarauta yaje tare da bada umarnin a rufeshi…….  Fadawa babu daman tambaya face aiwatar da abunda Yarima ya basu umarni…….
Bayan fitan Yarima Aliyu mahaifiyar Yarima tace ma Mai martaba hukuncin da aka yanke ma Yarima yayi tsauri da yawa ya……  Mai martaba dakatar da ita yayi tare da fad’in banso ki kuma saka baki cikin wannan maganan, kije ki fad’ama zinatu ta koma d’akinta……
Mum din Yarima amsawa tayi da Toh tare da fita dan tasan mijin nata yayi fushi Sosai….  Kuma tasan Kafin ya sauko sai anji jiki mutun ne mai hakuri amma bai iya fushi ba, ta tabbata tunda har Ya iya rufe ido ya hukunta Yarima tasan dakyar ya saurareta yanzu……  Koda ta koma gefenta taga zinatu nata kuka rarrashinta tayi akan tayi hakuri tare da fad’in ta koma d’akinta komai ya wuce, kiran Hafsat tayi tace ta raka gimbiya gefenta…..
Hafsat ta amsa da toh tare da cema gimbiya zinatu muje…..  Direct gefen gimbiya suka shiga suna shiga gimbiya ta wuce sama tabar Hafsat nan…..  Hafsat tace kina da aiki……
Hafsat komawa tayi wajan mum din tasu Tana tambayarta maiya faru,?
Labarin abunda ya faru mum taba Hafsat.
Hafsat cikin tashin hankali tace Abba da kanshi yasa Yarima yaje kurku?? Bari inje in ganshi mum tana maganan tare da fita
Direct kurkun ta nufa inda taga Yarima a ciki a rufe, kuka ta saki tare da bada umarnin a bud’e ta shiga.
D’aya daka cikin fadawan yace afuwa gimbiya Mai martaba ya bada umarnin Kar a bud’e kofar nan sai yayi sati biyu……
Yarima Aliyu murmushi yayi cikin takaici tare da ganin ba’a mishi adalci ba danya karya dokar daba addini bace, sannan abunda yafi d’aga mishi hankali yanda mahaifin nashi yayi amfani da mummunan kalma wajan cewa inya K’ara Karya al’ada bai yafe mishi ba, hakan bai isa ba saida Ya fad’a Mai ya dakile maganan auranshi da zainab…… Ido Yarima ya lumshe lallai mahaifinshi yana son rasa shi, domin a yanda yake ji,  bazai iya rayuwa ba tare da Zainab ba, bazai ma iya ganin wani ya aureta ba inba shiba, inko hakan ta faru baya ganin zai iya jura ko kad’an……
 Muryan Hafsat ne ya Katse Mai tunani da take fad’in bros Tana tsaye a waje tana kallonshi tace haka zaka kwana a nan? Tana maganan ne cikin tausayawa tare da kuka
Yace lil kin San ban son kuka koh?
Tace Bros taya bazanyi kuka ba, mai yasa Abba zaisa a rufeka danka saki matarka aiya kamata aji maita maka…..  I dnt knw why Abba yake d’aukan al’ada kaman addini yake daraja wannan al’adan ya kamata duk a barshi is not fai……..
Yarima Aliyu sa hannunshi yayi a bakinta tare da toshe mata yace enough lil sis, karki kara fad’in haka Kinji??….  Abba yana da ilimin addini Sosai baki ga duk cikin al’adan da yafi bashi muhimmanci shine na saki ba, karki manta Idan akayi saki sai al’arshan uban giji ya girgiza….. Abunda Abba yayi shine dai dai bai kamata inyi saki ba duk da raina ya baci…..  But thank god saki d’aya ne and kuma na maidata but I will teach her a big lesson for insulting my parent…..  Zan iya tolerating komai but banda zagin iyaye koci musu mutunci….. Yanzu Ina son kije ki zauna da ita Kafin in fito
Hafsat kallon Yarima tayi tace bros gskiya ban tunanin zan iya zama da ita, matarka she use to show her attitude to anyone ,and ni kuma I won’t tolerate it, in Naje haushinta zanji coz saboda ita kake nan
Yarima Aliyu yace lil wani attitude??
Tace dazu fah mum tace in rakata d’akinta muna shiga ta wuce ta barni, ko magana babu ai wannan haline mara kyau….
Yarima duk da ranshi a jagule yake saida yayi murmushi, kaf sisters dinshi yafi son Hafsat tana sashi nishad’i, yace lil ki daina sawa a ranki haka ne, kina jin haushinta kawai dan tasa an rufe miki bros d’inki…..
Hafsat tace uhm uhm Dan tasan ya ganota…  Tace Bros sauro zai dameka bari insa a kawo maka magani
Yarima Aliyu yace Nop leave it ko kin Kawo zasu shigo tunda kofar abude take….
Hafsat shuru tayi tana kallon d’akin da babu haske saina fitila domin ba’a Kai hasken huta ba dan dai kawai a horar damai laifi da duhu….. Gashi babu katifa balle filo, Hafsat ajiyan zuciya ta sauke tare da fad’in ina zuwa…….
Yarima Aliyu yana nan zaune shi d’aya…… Hafsat bata dad’e da tafiya ba saiga wani daka cikin fadawa yazo yana fad’in Allah ya taimaki Yarima Mai martaba ya bada umarnin a amshi wayoyin hannunka domin cikin nan ba’a shiga da waya……
Yarima shuru yayi tare da d’auka wayan yayi dialing number din Zainab ( bariki ) harya tsinke bata d’auka ba, kara kira yayi shuru, dan tsaki yaja kad’an Kafin ya kashe wayan ya mi’ka musu……
Hafsat direct gefen Mai martaba ta nufa, inda tayi sallama…. Amsawa yayi cikin sakin fuska tare da fad’in Hafsat baki bacci ba??
Tace eh Abba
Yace lafiya??
Tace Abba nazo neman alfarma ne
Yace Hafsat alfarman me?
Tace Abba dan Allah Nasan baka taba ce mana a’a ba akan duk abunda muke so, Abba kayi hakuri kasa Yarima ya fito dan Allah Abba, ta karasa maganan cikin kuka….
Mai martaba yace Hafsat tashi kije ki kwanta sannan daka yau karki kara zuwa inda Yarima yake daka yanzu na hana kowa yaje inda yake.
Tace Abba d……
Yace tashi ki tafi
Tashi tayi jiki a sanyaye domin dama tasan dakyar ya yarda dan tasan mahaifin nasu bai iya fushi ba…. Tasan mutum d’aya ce zata ma magana Indai tayi ma Mai martaba magana zai yarda a fito da Yarima itace gimbiya zinatu…..  Toh amma bata son zuwa wajanta dan bata son raini, dan haka ta nufi gefen mum dinsu a falo taga mum din na zaune tana karanta al’qur’ani…… 
Mum din ajiye al’qur’ani din tayi ta kalli Hafsat tare da fad’in baki je kin kwanta ba??
Tace mum taya zan iya bacci Yarima na kulle, mum wajan fah ko katifa babu babu abun rufa ga sauro….  Dan Allah mum kije Kema kiyi ma Abba magana….
Mum tace Hafsat tunda Mai martaba yace a rufeshi ko Nayi magana bazai sa a bud’eshi ba, so Kinga gwara kije ki kwanta zaifi miki….
Hafsat cikin kuka tace haba mum, wajan fah akwai sauro Wlh ciwo zai Kama shi Dan Allah m…..
Mum ta dakatar da ita da fad’in go and slp plz.
Hafsat fita tayi direct ta nufi gefen gimbiya zinatu koda ta shiga haurawa tayi har bedroom dinta taje tana mata nocking……  Ta dad’e tana nocking saiga Gimbiya zinatu ta fito tana fad’in lafiya cikin wannan daren? Maiya faru?
Hafsat tace kin San mai martaba yasa a rufe Yarima kuwa??
Gimbiya zinatu tace ban sani ba, amma Nasan zai iya zama gaskiya tunda ya karya al’ada…..
Hafsat tace kiba Mai martaba hakuri yasa a bud’e shi
Gimbiya zinatu tace hakuri akan a saki Yarima? Dariya tayi tare da fad’in Aiko bazai fito ba, gwara yaji a jikinshi koda na kwana biyu ne Kafin a fito dashi…… Karki manta yau ko wata d’aya Banyi ba amma yayanki yamin saki d’aya….  Ke kina ganin yamin adalci?  And akan wani dalili zanje ince ma sarki a sakeshi tunda gani mara kunya ni Uwar son miji ko??
Hafsat kallonta take cikin mamaki, tace amma Banyi zaton haka ba, kina maganan kunya AI baki dashi tunda har kika iya zagin iyayen mijinki…..
Gimbiya tace kin fad’i gskya, gashi na zagi iyayen nashi kuma har yanzu ina matsayin matarshi, sudai iyayen nashi su suka dawo dani….
Hafsat tace banyi mamakin jin haka daka gareki ba, and bazan biye miki ba domin irin tawa tarbiyan daban take, da taki……  Tas takai ma Hafsat Mari tare da fad’in karki manta koni wacece yayanki nake aure nafi karfin raini a Wajanki har abada……… 
zadai kuga typing error yau sosai domin typing din gaggawa Nayi yau

MARYAM OBAM

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button