NOVELSUncategorized

BARIKI NA FITO (BOOK 2) 17

BOOK 2
                    PAGE 17
Tari yake Sosai, bariki kuka ta Fara Tana fad’in Yarima Mai yake damunka?? Tare da tabashi tana son d’ago Shi ,hannunshi da yasa a baki yana tari ya cire ya fara kokarin tureta alaman tabar tabashi, amma jikinshi babu kwari ya kasa tureta din……  Wani irin tari yayi tare da yunkurin yin amai saiga jini nan…..  Wani irin ihu ta saki mai ban tsoro tare da kiran nashiga uku Yarima maiya

sameka?? 

Ganin jinin a bakinshi yana fita yasa ta fita da gudu, tana fita taga fadawa tace dan Allah kuzo Yarima  zai mutu, tana maganan tana kuka da ihu, kuzo mu kaishi asibiti…..  Da sauri suka shiga wasu kuma suka je fad’ama iyayenshi, koda fadawa suka shiga ganin Yarima sukayi a kwance yana wani irin nishi ga jini na zubar mai a baki, da sauri suka D’aukeshi suka fita dashi, suna cikin sashi a mota mum dinshi tazo, ganin halin da d’an nata yake ciki yasa ta Fara fad’in Innalillahi’wa inna ilaihirajiun, Yarima maiya sameka, lokaci d’aya kuma tasa kuka, shiga motar tayi da sauri suka nufi asibiti…… Bariki Kafin ta karaso har Sun wuce dan haka ta Fara cewa sauran fadawan muje ku kaini dan Allah inda suka je…..  Ganin kanta ko dankwali babu yasa wasu kuyangi dake tsaye wajan suka karaso suna fad’in Allah ya taimaki gimbiya, ki koma ki saka mayafi sai a kaiki,.
Sai a sannan bariki tasan a halinda take da gudu tayi ciki, inda ta d’auko mayafinta  tana kokarin fita wayar Yarima dake d’akin ya fara K’ara dole yasa ta koma ta d’auki wayar babu suna number ne ke kiranshi harya tsinke bata d’auka ba…..  Fita tazo yi lokaci d’aya kuma ta tsaya cak domin tunawa da abunda ya faru da Yarima, wanda tunda aka kirashi ta rasa gane kanshi,har wannan abun ya sameshi, danna wayan tayi da nufin ta shiga taga Mai aka turo mishi, gani tayi akwai password, shuru tayi tana nazari Mai Yarima ya gani??  Kodai wani ya fad’a mishi koni wacece??  Gabanta taji ya fara fad’i tunawa da kalaman daya Fara Mata Kafin ya fad’i……  Wani irin kuka ta saki mai ban tausayi, tare da fad’in shikenan2 sunyi nasara Sun fad’ama Yarima koni wacece kuka take Sosai, lokaci d’aya kuma ta fita da gudu inda taga mota na jiranta shiga tayi domin aka kaita asibiti da yake fadawa sun San asibitin da suke zuwa nan aka nufa da ita dan suna da tabbacin can aka Kai Yarima, tana mota tana kuka……
Kafin kace Mai har labari ya bazu cikin masarauta, Yarima Aliyu bashi da lafiya rai a hannun Allah, har wasu na cewa jini ke fita a bakinshi hala amaryanshi ba budurwa bace, wasu kuma suce kodai wani abu tayi mishi??  Haka dai ake ta jita jita, koda kuyangin gimbiya zinatu suka fad’a mata cikin tashin hankali itama tayi asibitin…..
Yarima Aliyu ko Kafin akai asibiti, ya daina koda motsi, ana zuwa akai emergency dashi, likitoci sukai kanshi aka fara dubashi, tare da bashi taimakon gaggawa….
 mum ta kasa zama sai kuka takeyi ga fadawa a wajan da yawa, kowa ya shiga cikin damuwa.
 basu dad’e ba saiga bariki ta karaso Tana kuka, tare da fad’in mum Ina Yarima?? Ina Yarima??  Mum din ri’keta tayi tare da rungumeta, ta kasa ko magana sai shafa ma bariki baya takeyi alaman tayi shuru……
 Suna cikin haka saiga Zinatu tazo cikin Tashin hankali ganin Bariki wajan mum ko ba’a fad’a mata ba tasan itace amaryan da Yarima ya auro, da sauri ta nufi bariki ta fincikota tare da watsa mata Mari Tana fad’in mai kika ma Yarima?? Mai kika mishi?? Kuka ta saki Zinatu tare daci gaba da fad’in Wlh Idan wani abu ya sameshi saina kasheki W…….
Mum sai yanzu ta iya magana, tace Zinatu kina da hankali kuwa?? A gabana kike wannan abun??  Shi Yarima dinne yace miki ita ta mishi wani abu??
Cikin kuka tace mum, daka ita sai shi, Nasan wani abu tayi mishi……
Mum tace ya isa haka, plz ki barni inji da abunda yake damuna ban son rigima….
Bariki kam tunda zinatu ta mareta take ri’ke da wajan Tana kuka, ko bata tambaya ba tasan itace Uwar gidan Yarima Aliyu……  Bariki tasan lallai ko ba’a fad’a ba dole kowa yayi zarginta, abunda Zinatu ta fad’a gaskiya ne….. Kuka tayi k’asa tanayi tare da fargaban Kar wani abu ya sami Yarima dan bazata iya jura ba…..
Kowa na cikin Tashin hankali, ga doctors har yanzu basu fito ba……  Suna nan zaune saiga Mai martaba shida Hafsat Sun zo cikin Tashin hankali.
Mum ganin Mai martaba yasa ta tashi ta nufeshi tana kuka, tare da fad’in ina jin tsoro Kar Yarima ya mutu Aman jini yakeyi Ina tsor…..
Toshe mata baki Mai martaba yayi, tare da fad’in ki daina fad’in haka, Hafsat itama kuka ta Fara cikin Tashin hankali…..
Duka kowa shuru yayi babu Mai rarrashin wani, suna nan tsaye d’aya daka cikin doctors din ya fito, suna ganinshi suka nufeshi tare da fad’in Dr ya ake ciki, ganin Mai martaba yasa yace ranka ya dad’e wacece Zainab a cikin nan?? 
Da sauri mum tace ga tanan tare da nuna bariki, yace ok tare da kallon Bariki yace taso muje……
Da sauri ta tashi tabi Dr, kowa da abunda yake sakawa, Zinatu ta Fara fad’in mum kin gani ko kin gani wlh itace tayi mishi wani abu…..
Kowa shuru yayi ya kasa cewa koda uffam…. Suna jira suga ikon Allah……
Koda Bariki suka shiga oxygen din da akasa ma Yarima yana k’asa alaman yana son d’aukewa, kuma yana saka zero shikenan mutum ya mutu, da sauri Dr yace plz ki mishi magana sunanki yake ta kira pls say something karku rasa shi…….
Da sauri ta ri’ke Mai hannu tana kuka tare da fad’in Yarima karka bari wani abu ya sameka…..  You know that I can’t live without you, plz Yarima ka tashi kasan ina Sonka kaine rayuwa na, wlh bazan iya juran inga wani abu ya faru dakai ba…… 
Lokaci d’aya oxygen din ya fara k’aruwa alaman numfashin shi yana son dai daituwa….  Likitocin ganin haka yasa suka fara kallon juna alaman jin dad’i an fara nasara….. Bariki kuka take Sosai tana fad’in karya mutu ya barta….
 Idonshi dake rufe ya fara zubar da hawaye……  Lokaci d’aya numfashin shi ya dai daita……
D’aya daka cikin doctors din yace ma Bariki yauwa komai yayi dai dai mu jira muga kuma yanda Abun zai kasance amma muna bukatar ki zauna har muga farkawanshi, muna nufin Kar kibar asibitin nan har sai munga ya farka ….
Cikin kuka tace babu inda zani Ina nan tare dashi
Dr din fita sukayi, inda suna fita Mai martaba yace ya akayi?? Mai yake faruwa dashi??
D’aya daka cikin Dr din yace ya samu bugawan zuciya ne, ina tunanin yaga abunda ya bashi tsoro ko mamaki, kuma daka duka alamu abunda ya gani ko yaji yana d’aya daka cikin abu masu muhimmanci a rayuwanshi, hakan yana faruwa wasu ma rasa ransu suke, a gskya masu rasa ransu ma sunfi yawa amma shi yayi Sa’a ko ince mun samu mun ceco rayuwanshi tare da taimakon Allah da kuma wannan baiwar Allah dake ciki, magananta da yaji shine yasa zuciyarshi ta Fara harbawa, inda badan ita ba toh gaskiya dasai dai kuji mummunan labari , dan haka dole ta zauna dashi muga yanda Allah zaiyi…..
Mai martaba godiya yayi ma Dr din tare da fad’in zamu iya ganinshi?? Sannan kana ganin zai tashi babu wani matsala??
Dr yace zaku iya ganinshi amma plz Kar kuyi magana, sannan zai tashi insha Allah Indai yarinyar na kusa dashi kuma yana jin magananta a kusa dashi…..
Mai martaba yayi ma Dr godiya, sannan suka shiga d’akin, ganin Bariki sukayi a zaune kusa dashi hannunta na ri’ke da nashi tana kuka…..
Kowa tsayawa yayi yana mamakin irin wannan Abun musamman mum damai martaba, ita dama zinatu bata shigo ba domin maganan Dr yasa taji wani iri tare da takaici….. Mum ce ta k’arasa kusa da inda Yarima din yake tare da kamo d’ayan hannunshi, fuskanshi tayi fayau ga hawaye a idonshi na zuba…..  Mum itama hawayen ne yake zuba daka idonta, kowa dake wajan ya tausaya mishi……  Mai martaba ganin mum nason kuka mai sauti yasa ya kamota sukai waje, Hafsat da Bariki suka zauna a d’akin
Zinatu ce ta shigo d’akin ganin zinatu yasa bariki tashi tabar d’akin domin irin kallon da taga zinatu din nayi mata, kuma ko babu komai ya kamata ta dan bata waje ta gana da mijinta duk da bai farka ba…..
Fita Bariki tayi tana fita, Mai martaba yace Zainab ya kika fito??  Ko wani abu kike bukata??
Tace a’a Abba cikin jin kunya, na d’an basu waje ne…..
Mai martaba ya gane ta fito ne saboda Zinatu…….
Mum tace Zainab bai kamata ki fito ba ai, maza ki koma Kinji…..
Tace toh mum jiki a sanyaye Bariki ta shiga, abubuwa sun mata yawa, na farko Tana zullumin Mai aka fad’ama Yarima a waya, sannan maiya gani, duk wannan Abun suke ta faman Mata yawo a Kai….. Koda Bariki ta shiga zintau fita tayi
Bariki zama tayi kusa da Yarima tare da kurama fuskanshi ido, har yanzu yana hawaye, gaba d’aya zuciyarta ta tsinke, shidai har yanzu bai farka ba, toh wannan hawayen fah????…..  Kiran Hafsat akayi a waya ta tashi tabar d’akin Tana fita kaman ance Yarima ya bud’e ido , a hankali ya bud’e idonshi ya sauka akan na Zainab wacce itama shi take kallo tana murna tare dason yin magana murna ya hanata……
Murmushi ya sakar mata, tare da kamo hannunta ya ri’ke tare da matse su…..
 A hankali tace Yarima Ina Sonka I can’t live without you, tana maganan tana kuka, tace I was scare with your condition I……
Hannunshi yasa ya rufe Mata baki yana kokarin yin magana ya tsaya alaman ya tuna da wani abu…….  Lokaci d’aya ya sake mata hannu tare da fad’in leave from hare I hate to see your face……..
Cikin kuka tace Yarima zainab din’ka ce Yarima nice maina……
Ya daka mata tsawa tare da ri’ke kirjinshi yace I said leave from here ……. Su mum dake waje Suka shigo harda su zinatu,  ganin Bariki na kuka Yarima shima hawaye ne ke zuba a idonshi gashi ya ri’ke kirjinshi……  Kallon iyayenshi yayi tare da fad’in mum tell her to leave from here…….  Kowa kallonshi yake cikin mamaki da sauri Hafsat ta fita kiran doctor……  Mai martaba yace Aliyu matarka ce kake koranta?? Maita maka??……  Yace Abba plz tell her to leave I don’t want to see her face….  Why am I still alive…. Dai dai lokacin doctor yazo yace kowa yabar d’akin……..  Bariki da sauri ta fita Tana kuka lallai ta tabbatar an fad’ama Yarima  ko ita wacece kuka take Sosai tare da barin asibitin ba tare da sanin kowa ba……
Hmmmm Ashe masoya novel’s din bariki suna da yawa?? Ban taba sani ba sai jiya???????????? lallai kuna son posting naga ruwan comments harda Wanda ban San suna karantawa ba, jiya Sun zuba comments, tunda hakane nima daka yanzu zan daina posting kullum Indai bakwa zuba comments kunga 50 50 kenan kuyi rowan comments inyi rowan posting???????????? Ina sonku masoya novel’s dina
MARYAM OBAM

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button