Wani mutum ya rushe gidan da ya ginawa matarsa da babarta bayan ya gano tana shirin rabuwa dashi

Wani mutum dan kasar Malawi mai suna Fransis Banda ya rushe gidan da ya ginawa matarsa da babarta bayan ya gano ta shirin rabuwa dashi ta auri wani.
Fransis ya bayyanawa Malawi 24 cewa sun sunyi aure shekara 13 data wuce shida matar tasa kuma suna da ‘ya’ya uku tare.
Yace tsahon lokacin auren nasu ya ginawa matar tasa gida sannan kuma ya ginawa babarta gida itama a kauyensu.
Daga baya kuma sai fara cin amarsa tana soyayya da wani daban inda ta tattara kayanta ta fice tabar gidansu na aure ta koma kwana a gidan saurayinta.
Yace nayi kokarin kiran matata da surukata ta waya amman amman sabon saurayin ya kwace wayoyinsu hakan ni kuma ya bata mun rai naje na fara rushe gidanjen da na gina musu tare da taimakon yan uwa da abokan arziki.
Watch the clip below,
asha kallo lafiya