BABU SO HAUSA NOVEL

BABU SO….. 12

Typing????

  *_❤‍????BABU SO....!!❤‍????_*
             _(Miya kawo kishi?)_



          *_Bilyn Abdull ce????????_*

12

……….A karon farko ta ɗago ta kallesa da mamaki ganin inda yay parking. Magana take so tayi, sai dai ta kasa. Shi kuma yaƙi cemata komai, sai ma wayarsa daya ɗauka yay ƴan danne-danne yakai kunensa. “Fito”. Kawai ya faɗa ya yanke wayar. Ba’a rufe minti uku ba wata budurwa mai tsananin iyayi ta fito daga shagon saloon ɗin tana tafiya kamar tarwaɗa. Haka kawai abin nata ya bama Anam haushi, taja siririn tsaki da taɓe fuska ta janye idonta. Duk da tayine a hankali sai da yaji, sai dai bai nuna yajinba balle ya tanka, sai ma faman daƙilar waya yake, amma ya buɗe murfin kafarsa ɗaya a waje take.
      “Assalamu alaikum Yah Musty barka da zuwa”. Budurwar ta faɗa murya a lanƙwashe lokacin da take isowa wajen. Kansa kawai ya jinjina mata yana janye kunne ɗaya na earpiece dake a kunnensa. Kamarma bata damu da abinda yay matan ba. Murya ta ƙara tausasawa cike da iyayi tace, “To Bismillah muje ko”.
       Nan ɗinma bai tankaba, sai da yaja wasu sakanni ma sannan yay yunƙurin fita a motar.
    Baƙin ciki, haushi da takaicin ballagazanci na wasu mata ya tokare maƙoshin Anam. Lokaci ɗaya taji tama tsani budurwar.
         “Sai an fito da ke ne?”.
Ya faɗa cike da gatse idonsa akan Anam. Jitai kamar karta fita ɗin, amma sai yaci darajar Yaya da yake gareta tabi umarninsa. Yanda budurwar batai mata magana ba itama bata nuna tama san da zamanta a wajen ba. Gaba sukai tana binsu a baya, budurwar sai ƙoƙarin dai-daita tafiyarta take da shi tamkar dole, ga baki ta saki sai surutu kai kace hanyar kasuwar wanbai aka buɗe da safe. Sosai wajen Saloon ɗin ya haɗu dan yaɗan birge Anam kaɗan, sai dai bata nuna a fuskaba saima kicin-kicin data sakeyi da fuska duk da gaisuwa da ma’aikatan wajen ke musu na girmamawa daya bata mamaki matuƙa. Wajen zama aka basu, harda ajiye musu abinsha kafin budurwar da taji ma’aikatan sun kira da aunty Deena ta dubesa cike da yauƙi da shauƙi.
          “Sir za’a mata kitso ne?”.
    Bai jita ba, saboda earpiece dake manne a kunnensa. Hannu takai ta cire kunne ɗaya, ya ɗago ya dubeta yana sake tsuke fuska. “Am sorry, nayi magana ne bakaji ba, nace za’a mata kitsone?”. Idonsa ya ɗauke daga gareta ya maida ga Anam datai kicin-kicin da fuska fiye da yanda suka shigo dan ta fahimci ita ya kawo kenan. “Komai ma daya dace kumata”. Ya faɗa a taƙaice da maida earpiece ɗinsa.
        “Ni wlhy bance inaso ba. Kuma kaina a wanke yake, hakama……” Hararta yay yana mai zare kunne ɗaya na earpiece ɗin, tai saurin sake haɗiye maganar tana matso hawaye. Ɗauke idonsa yay kamar baima ganta ba. Tanaji tana gani aka kwance mata kalbar kanta aka saka mata relaxer aka wanke fes. Bayan an rage ruwan da towel akai steaming ɗinsa. Wadda take mata gyaran tambayarta tai tana son kitso ne? Amma tai mata banza. Ganin haka ta juya ga Shareff dake zaune komai anayi gaban idonsa.
      “Sir za’a mata kitson ne ko a barta?”.
        “Barta kawai a mata lalli”.
Yay maganar batare da ya kalleta ba yana maida earpiece ɗin kunensa.
       Ana fara wanke mata ƙafa da gyaran farcen hanunta ya miƙe ya fita, Anam ta bisa da harara ƙasa-ƙasa tana tura baki. Cikin ƙunƙunai tace, “Gwarama da zakai aure mu huta da baƙin halinka”.
    Murmushi mai mata wankin ƙafa tai saboda jin abinda tace. Lokacin da aka fara zana mata lalle harda ɗaukar video, dan tana son lalli sosai kitsone dai kam saida dambe da Mamie tsaye kanta, dan ko Mamie ce tace zata mata ba yarda take ba da arziƙi. Abie kam lallaɓata yake ko yace a barta sai wani lokaci tunda bata so.
       Sosai ta fito ras tai ƙyau tamkar wata sabuwar amarya. Sai faman kallon kanta take a manyan mirrors na wajen tana murmushi da ɗaukar hoto kamar ba’itace ta gama rikiciba yanzun. Sai da tai mai isarta sannan ta fito waje kamar yanda Deena ta tabbatar mata Yaya Shareff na nan na jiranta a waje. “Okay”. kawai tace mata tai ficewarta. Deena da yaranta suka bita da kallo baki taɓe. Fuska ta haɗe tamau tana cika baki da iska lokacin da take fitowa, ta buɗe motar ta shiga tana wani kauda kai taƙi kallon inda yake.
        A jiyar zuciya ya sauke a hankali yana ɗagowa daga kwanciyar da yay jikin kujerar, murmushin daya tsaya iya laɓɓansa ya ɗan saki ganin yanda taketa faman kauda kai gefe wai ita a dole haushi take da shi. Hanunsa ya kai ya zame veil ɗin, tai saurin riƙewa tana tura baki. Kallon daya wulla mata ya sata sakin masa babu shiri, sai da ya gama ƙarema gashin kallo cikin ɗan lumshe ido da buɗewa ya maida mata ya rufe. Sosai gashin nata yasha gyara sai ƙamshi mai daɗi da ƙyalli yake.

      Koda suka iso a gate yay parking, tana fita yaja motar yay gaba abinsa. Da harara ta raka motar, sai kuma ta kalli hanunta da ƙafa da sukasha lalli tai murmushi. Gidansu tai shigewarta. Dan cikin gida tun daga waje kana iya jiyo hayaniyar daya sake ɗauka alamar baƙi sun ƙaru kenan. Gidan nasu ma cike ta sameshi da baƙin da suka iso bayan fitarta. Sai su Aysha dake shirin komawa gidansu amarya bayan magrib Arabian night. Tambayarta wanda yay mata ƙunshi suka shigayi kowa na yaba ƙyan da yayi. A takaice tace musu Yayane ya kaita wani waje kawai. Koda suka buƙaci jin wane Yaya a ciki bata amsa musu ba tama shige toilet dan son watsa ruwa kasancewar gab ake da kiran sallar magrib saboda sun jima a wajen ƙunshin nan ba laifi, gashi ko sallar la’asar batayi ba.    
      Ana idar da sallar magrib ƴammatan gidan suka sake ficewa wajen event na arabian da aka shirya amma banda Anam yanzu ma. Dan kwanciyarta taima tana kallo a lap-top hankali kwance kamar bata san bikin da akeyi ba. Har magana Amrah tai mata amma tace karta dameta. Yanda tai maganar cikin masifa yasa kowa bai sake magana ba sukai shirinsu suka fice.

          ★★★★★

Washe gari kam gida ya sake cika danƙam da ƴan uwa da abokan arziƙi na nesa dana kusa. Abokan Yah Shareff na Nigeria da wajenta duk wanda ya iso anan ake saukarsa gidansu Anam a sashen Shareff ɗin da tuni Abie ya ware dominsa duk da ba zama yake ba a hanunsu yanzun. Duk hidimar da ake Anam na ɗaki batako fitowa sai yunwa ta isheta. Bamai ganin ko fara’arta. Mamie tayi faɗan harta watsar da lamarinta, hakama Aysha fushi take da ita dan ita bataga mi Anam ɗin kema fushe-fushen ba tunda babu wanda ya mata wani abu ai. Aima gaba ɗaya ta tsame kanta daga shagalin bikin tamkar Shareff ba ɗan uwanta ba. Da yamma kusan rabin jama’ar gidan suka wuce gidansu Fadwa amarya kamu amma nanma Anam bataje ba. Kai barci ma suka wuce suka barta tana sha hankali kwance. Koda suka dawo kuma su Aysha nata labarin yanda kamu ya kasance da ƙayatarwa Anam sai tai tsaki tama fice a ɗakin gaba ɗaya. Da kallon mamaki duk suka bita, sai dai babu wanda ya kawo komai a ransa game da al’amarin nata tunda ansanta da miskilanci da kuma tsanar da sukaima juna ita da ƴan gidan su Fadwa batun yanzu ba.

        _WASHE GARI ta kama ranar ɗaurin aure, har sha biyu Anam na ɗakin Abie tana shaƙar barci. Dan tun bayan sallar asuba ta gudo daga ɗakinsu saboda hayaniya tafi ƙarfi acan downstairs. Duk tashin da Mamie ta mata taƙi, sai kawai ta shareta ta cigaba da hidimar baƙinta, dan nan ɗinma dai ya cika taf da dangin Mamie da ƴan uwa da abokan arziƙi kasancewar wannan shine karo na farko da zata fara aurarwa, duk da ba’ita ta haifi Shareff ba an mata karar riƙesa da tai tamkar ɗanta auren ya koma tamkar a hanunsu ne.
      Mutane sai tambayar ina Anam akeyi, sa’ointa ma na family ɗin sunata zuwa nemanta. Bata tashi ba sai kusan ƙarfe ɗaya, batare da tayi ko brush ba ta fito sanye cikin kayan barci fuska a kwaɓe dan yunwa takeji. Fitowar tata yayi dai-dai da shigowar ango da tawagar abokansa, yayi ƙyau har ya gaji cikin ɗanyer shadda fara tas sai baza ƙamshi yake yi. Ga wani kwarjini na musamman da kwalliyar ta basa tabbacin yau ɗin ta daban ce a garesa. Hakama abokansa kowa ya sha ƙyau.
     Anam ta kafesa da manyan idanunta da barci ya sa su yin wani luf-luf da sake girma, shima tunda ya shigo nasa idon a kanta suke, sai dai lokacin ɗaya ɗan murmushi dake a saman fuskarsa ya bace ɓat, ya ɗan harareta ya ɗauke kansa kasantuwar caa da ƴan uwan Mamie sukai masa kowa na faɗin albarkacin bakinsa cikin yabawa.
     Murmushi ya ƙaƙaro yana kaiwa rissine domin gaishe su kamar yanda abokansa sukayi suma, kafin ya miƙe zuwa gaban Mamie da tun shigowarsu idonta ke kansa tana murmushi. Gabanta ya durƙusa ciki sanyin murya mai nuna rauni yace, “Mamie zamu tafi masallaci”.
      Hannu ta ɗora saman hularsa, itama muryarta a raunane da sanyi  tace, “ALLAH yay maka albarka Al-Mustapha. ALLAH yasa a ɗaura a sa’a, kuma yasa abokiyar arziƙinka ce har a aljannah”.
    Gaba ɗaya falon aka amsa da amin. Shareff da kansa ke ƙasa ya kasa ɗagowa, hakan yasa Mamie kamo haɓarsa da yatsunta biyu ta ɗago fuskarsa. A hankali hawayen dake maƙale a idanunsa suka gangaro, murmushi ƙarfin hali tayi da ƙoƙarin son danne nata hawayen dake son zubowa amma hakan ya gagara. Itama sai kawai ta saki kuka mara sauti tana goge masa nasa hawayen da hanunta duka biyu. Sun birge kowa, sun kuma bama kowa tausayi, duk da wasu basu san dalilin kukan nasu ba kai tsaye.
    Mamie dake murmushi ga hawaye tace, “Tashi kuje karku makara su Abie ɗinku sun wuce tun ɗazun. Kai Shareff ya gyaɗa a hankali, sai kuma ya kai hannu shima ya share mata nata hawayen, ta saki murmushi da shafa kansa. “ALLAH yay maka albarka”.
      Da amin aka sake amsawa. Ya miƙe idonsa na kallon ɗan lungun da zai sadaka da hanyar upstairs inda Anam take. Har yanzu tana gurin, hasalima leƙensu take baki a taɓe dan ita bataga miye na kuka ba inba gulma ba. Harda faɗin, “Su Mamie an iya kalan dangi, Mommyn sa batako kallona da arziki amma ke kinama ɗanta wannan kulan”. Ganin ya miƙene yasata komawa ta maƙale, jin kamar sun nufi hanyar fita ta sake leƙowa. Ido suka haɗa dashi yana tsaye shi da Aunty Mimi suna magana. Fuska ta taɓe da murguɗa baki tabar wajen. Numfashi ya saki a ɗan fisge da lumshe idanunsa ya ɗauke kansa shima. Aunty Mimi da duk taga komai tai murmushi kawai tana kallonsa.
      Fuska ya ɗan kwaɓe. “Miye kuma small Mom?”.
   Dariya tayi da faɗin, “A’a babu komai My son. Kuje karku makara ALLAH yasa a ɗaura a sa’a.”
     “Humm”
kawai yace mata yay gaba abinsa. Ta sake ƙyalƙyalewa da dariya. “Ita dai wannan Humm ɗin bata magani Yarona”.
       Murmushi kawai yay batare daya juyo ba ya fice abinsa. Dr Jamal da Fharhan da suka rage na take masa baya..

1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button