Labarai

Ganduje Ya Sauya Wa Jami’ar Kano Suna Zuwa Aliko Dangote

Gwamnatin Jihar Kano ta amince da sauya wa Jami’ar Kimiyya da Fasaha (KUST) da ke Wudil a Jihar, suna zuwa na hamshakin attajirin nan na Afirka, Alhaji Aliko Dangote.

Daukar matakin, a cewar Kwamishinan Yada Labarai na Jihar, Malam Muhammad Garba, ya biyo bayan amincewar Majalisar Zartarwa Jihar ne yayin zamanta na mako-mako Aminiya ta rawaito.

Ya ce hakan kuma na cikin shawarar da Hukumar Gudanarwar Jami’ar ta bayar.

Muhammad Garba ya tabbatar da hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar.

Sanarwar ta ce yanzu za a rika kiran sunan makarantar da sunan Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Aliko Dangote (ADUST) da ke Wudil.

Kwamishinan ya ce tuni aka aike da bukatar canza sunan a hukumance ga Majalisar Dokokin Jihar ta Kano domin ta amince da shi ya zama doka.

Alhaji Aliko Dangote, wanda shi ne attajiri mafi kudi a nahiyar Afirka dai dan asalin Jihar ta Kano ne.

Jami’ar kuma a daya bangaren na daya daga cikin jami’o’i guda biyu mallakin gwamnatin Jihar.

Ko a shekarar 2018 sai da Gwamnan Jihar, Abdullahi Umar Ganduje, ya canza wa Jami’ar Northwest, ita ma mallakin Jihar suna zuwa Yusuf Maitama Sule.

               

[ad_2]

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button