NOVELSUncategorized

NI DA AMARYATA 23

*_????KAINUWA WRITERS✍???? ASSOCIATION_*????????
“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`
????????????????????????????????
*NI DA AMARYATA*


Na
Khadeeja Usman


2⃣3⃣_2⃣4⃣


          Alhaji yayi tafiya, yayin da Hajiya kaka ke kula da wasu abubuwa na gidan,Dan tasa ido sosai.Ita Kam Hajiya Hafsa ta zuba ido ne taga iya yadda abin na Alhajin zai tsaya,Dan Sam Bata hango wani ci gaba da za’a samu game dasa Nihila a makaranta ba,dan sosai tasa su Ummi suke wasa da hankalinta,Sam Bata maida hankali gurin karatu,tafi mayar dashi gun wasan ‘yar baby,da Kuma gayyato yaran makwabta su kusan yini suna Abu Daya,Wanda wani lokacin saita kwanta ta lafke tace batada lfy,Dan Kar taje makaranta,ita kuwa Hajiya kaka tace kada a takura Mata,Amma ita kanta wani lokacin hayaniyar yaran da Suke tana damunta matuka,haka zasu hanata bacci.

A bangaren Aunty Hama yanzu ta rage zuwa gidan Nihila,danta koya Mata wasu abubuwan yanzu wanka tana yi da kanta,shiyasa ta mayar da hankali gurin jinyar ‘yar uwarta,yayin da Alhaji kabeer yake taimaka Mata sosai,duk da ya bijiro Mata da maganar Yana son ya aureta,ta Nuna Masa bazata iya aure yanzu ba,Dan halin da ‘yar uwarta ke ciki,sosai ya Nuna Mata ba wata matsala inda zata tare saisu tafi da Amina,amma ta Nuna Masa yayi hakuri kawai,duk da hakan amma Bai gaza da su ba,Yana kokarin ganin sun Sami cikar buri,Wanda a yanzu kiris ya rage su Gama hada kudin aikin,Wanda koshi Yana son ya cika musu wasu kudin sa yake jira shiyasa.

******
Satin Alhaji Sani biyu a tafiyar da yayi ya dawo,inda girkin Hajiya ne,Dan dama shi a tsarin gidansa babu me aiki,amma dole saboda Nihila yasa aka samo wata Mata Mai suna Sehra ‘yar kabilar inyamurai,ita keyin girki yanzu a gidan.koda ya dawo ya tarar da Nihila zaune a compound suna ‘yar carafke ita da wasu yara, kasancewar yamma ce,musu ya turnuke a tsakaninsu,inda aka Fara fada kan kace me ya hango an kacame da danbe,shi Sam da farko baima gane su waye a wajen ba,Saida ya hango Nihila tana tufke kanta tana bala’i,Dan Zahra gashinta ta rike,aikuwa dai-dai Yana karasowa yaji tana fadin,

“Na rantse da Allah,yau Banga Wanda zai hanani ninnika ki ba a gidan nan!Dan wallahi saina ci kaniyarki dai-dai gwargwado,yadda ko mamanki sai tayi da gaske kafin ta ganeki”….

Aikuwa  Bai Gama jiba,yaga ta wajen Nasa takai wa yarinyar bugu,Nan suka Kara kacamewa.Da sauri ya karaso wurin ya dauke Nihila cak,wadda ta Fara kuka,Dan dama ita ba karfi ba,amma Kuma Bata barin ta kwana,a haka ya shige da ita falon tana ta zunduma ihu tana dukan kirjinsa tana fadin ya sauketa ita fa saita rama,a lokacin Daya shiga falon su Hajiya kaka da su Hajiya Hafsa na zaune zaman jiran shigowarsa Dan sunyi waya dashi ya sanar musu Yana airport,hakan yasa Hajiya Hafsa ta shirya yadda yakamata,aikuwa sai ganinshi sukayi dauke da Nihila tana wannan borin.Hajiya hafsa tayiwa yaran alama dasu tashi su shige ciki,aikuwa duk suka mike sukayi ciki,Amira ce ma ta tsaya yima Abban nasu sannu da zuwa,sannan ta shige tana Mai Jin kunyar abinda mahaifin nasu yakeyi a yanzu. Hajiya kaka ko banda dariya ba abinda takeyi,Nan ta shiga fadin ” Ah lallai! Yau akwai aiki,wato rigimar ta motsa kenan ! Da baka Nan ai batayi ba,sai yanzu ja’ira dataga ka dawo,Kai ‘ya’yan zamani anyi fitinannu,ai indai kaga yarinya na irin wannan a farkon aurenta,to maza za taita Haifa,da wuya ma ta haifi mace,Dan haka sai anyi hakuri da irinsu ka Kara hakuri kaji me albarka!..”

“Ai dole Kam ayi hakuri Hajiya,Dan wannan ‘yar taki akwai rigima,Bari kiga inje in rarrasheta….”ya karasa maganar Yana haurawa sama,inda ita Kuma har yanzu Bata daina kukan ba,tana Kiran ya sauketa saita rama.
     Tsananin takaici da bakin ciki yahana Hajiya Hafsa yimasa Koda sannu da zuwa,kawai saita mike ta nufi sashenta,Hajiya kaka ta rakata da harara,tare da fadin,”haka dai! Sai bakin kishin jaraba,ta ciki na ciki,ga mahaifa Kuma madaukiyar ‘ya’ya mata,su dinma bada yawa ba duk sun girma sun Zama gotai-gotai dasu,sun wuce ai musu wasa,Ni yanzu ‘yan dagwai-dagwai nake so,wadanda zasu dinga hawa kaina,Ina dagasu Ina caballi,ba wadan Nan guma- guman ba da duk wadda tayi yunkurin hawa cinyata daga ranar na tashi da Hajiya Luba! Sai dai a kirani da lubabatu gurguwa! Dan haka sai dai bakin ciki ya kasheki amma Zama daram,aita zazzago min Koda masu sanko ne,ai dama kyan namiji kudi!”

Ita dai tuni ta shige,tabar Hajiya kaka ta luguden lebe.

*****

Suna shiga dakin direct saman gadon ta ya ajiyeta,kallonta ya tsaya yi ganin yadda duk ta hade fuskarta da hawaye da majina,girgiza Kai yayi a ranshi yace”Ni Kuma wannan shekarar tawa kaddarar kenan!hmmmm…ya sauke numfashi,kafin ya karasa gareta tare da Kama hannunta yace,”haba baby! Ke Wai Baki San kin girma bane? Kullum Baki da aiki sai Zama da yara Kuna wasan yara, ke fa yanzu ba sa’arsu bace,kamata yayima ki daina wasa dasu,kawai su dinga ce mike Aunty!,Jin ya ambaci Wai zasu rinka ce Mata Aunty yasata tsagaitawa daga sasshekar kukan da takeyi ta dago ido ta kalleshi,shima din ita yake kallo,sai yaga ta Kara mishi kyau da Kuma girma a iya sati biyun da baya Nan,katse tunanin shi tayi yaji tace,” dagaske zasu rinka cemin Anty,bayan Kuma khairat da saudat sun fini girma”?

“Eh mana! Dole ai su rika ce Miki Aunty,saboda ke kinada aure,ko sun girmeki to ke yanzu kin girmesu a yanayin rayuwa,Dan haka dole su girmama ki” 

Bata san lokacin da murmushi ya subuce Mata ba,jin Wai wadan Nan gandama gandaman Wai zasu ce Mata Aunty,Dan haka cikin farin ciki ta shiga goge hawayenta,tare da kallonshi tace,”shikenan na daina wasa dasu,zance musu ai na girmesu a rayuwar da muke ciki,amma to Kuma a lahira ma na girmesu?” Tayi Masa tambaya!

“Dariya yayi, sannan yace,”eh to in kin mutu yanzu,ta yiyu ki girmesu tunda ke kinada aure!”

“Kenan aure ne banbanci yanzu a tsakanin mu?”ta sake jefo mishi wata tambayar.

“Ah ah,ba iya aure band,akwai abubuwa dayawa,Zan fada Miki sai kin Kara girma tuku “

Ji yayi tace,”Allah yasa nayi saurin girma kamarka” 

Dariya maganar ta tabashi,amma Saiya basar tare da fadin “tashi kije kiyi wanka,Kinga kin Bata fuskarki”

“Ah ah ni yau bazanyi wanka ba gaskiya,shekaran jiya nayi fa,jiya kuma nayi kwaskwarima,yau ba sai in huta ba” Dan Kar inyi mura”,zaro ido yayi waje,sannan yace” lalalah! Yaushe baby ta Zama kazama ne? Keda in son samu ne kiyi wanka sau uku a rana”?

“Bafa kazanta bace Daddy,kaga in mutum ya fiya zubawa kanshi ruwa Allah Yana mura”.

“Badai Dan wanka ba,tashi maza kije kiyi wanka,Kar in Kara ganinki bakiyi wanka ba zamu Bata”.

Zumbura Baki tayi tare da fadin,”gaskiya Ni fa ban iya wankan bane sosai,dama a gida Anty Hama ce kemin,Kuma ko’a Nan ma fa,tana zuwa a sace tayimin,to kwana biyu kuma jikin mamanmu ne ya tashi Wai injita,shine tace inyi da kaina Kuma fa bana iya cuda bayana,shine nakeyin fashi,tunda Naga ban kware a wankan ba”.

Rasa ma me zaice Mata yayi,Dan haka yace,ta tashi suje yayi Mata wankan,aikuwa batare da tayi gardama ba,ta mike,suna shiga toilet din ya hada ruwa a bathroom yace ta zo,ba musu ta shiga cire kayanta,sosai ya kura Mata ido,domin surar ta ta tafi dashi,Dan Sam Bai kawo yarinyar takai haka ba,magana taketa Mai take fada Masa ta cire,Amma Ina ya shagala da kallon kirjinta,ganin hankalinshi ya tafi wani gurin daban yasata duba inda yake kallon.Aikuwa saita kwabe fuska tare dasa hannu ta Kare,sai a lokacin ya dawo cikin tunaninshi Amma ya shiga wani Hali,ji yayi tace,”shine kake kallemin kuraje na ko? To ai Dana fadawa Aunty Hama lokacin Da suka Fara fitomin sunamin zafi,Wai saita cemin sai sun Gama girma sannan aimin aiki,gashi har yanzu Basu Gama ba,klum ma dada kumbura sukeyi” ta karasa maganar kwalla na taruwa a idonta.

Sam yakasa cewa komai,domin koya yayi maganar ma ji yake bazata fahimta ba,Dan haka yayi shuru kawai.itama ganin yayi shurun saita hadiye kukan nata.

Wanka yayi Mata sosai,inda da dabara ya dinga tabata Wai koya Dan rage zafi,har Saida tace Masa itafa ta gaji da wannan wankan sannan ya Bari.

Bayan yasata ta shirya cikin Riga da wando jeans tayi kyau sosai,shi kuwa shi kadai yasan halin da yake ciki,haka ya daure tare da fadin,”zanje nayi wanka naci abinci,kafin Nan ki shirya malamin dayake koya Miki karatun islamiyya zaizo”

“Tab yaseen ba inda zani,malamin dayake Dan iska,harda wani cemin wai zai koyamin wankan tsarki,nufinshi ko fitsari nayi da Kashi sai nayi wanka,Bai San Ni bama shiri da ruwa ba,Ni kuwa tunda ya Fadi haka na mike nayi Masa Allah ya Isa na gudo,shine fa ya daina zuwa”.

Rasa abin cewa yayi kawai ya fice,ya barta tana ta shirmenta.

Yana shiga dakinshi ya Kira Hajiya Hafsa,cikin kankanin lokaci sai gata ta hauro saman kuwa,yayi mamakin ganin ta da fara’arta ta shiga yimasa barka da dawowa,ruwan wanka ta hada masa,da kyar yayi wankan,sannan ya nemeta Dan biyan bukatarshi,Sam Bata hanashi ba,Dan ita kadai tabarwa kanta sanin kudirin ta,Dan haka sosai ta tarairaye shi da dukkan kulawar data Dace.

******

Tun sassafe yasata ta shirya Dan shi zai ajiyeta makaranta,inda ta shirya 
Ta fito bakin mota tana jiranshi,Hajiya Hafsa ce tayi Masa rakiya,ganin yadda yake sauri yasata tambayar shi ko lfy yake wannan saurin?

Nan yake Fada Mata zai ajiye Nihila a makaranta ne bayason ta makara.kasa ce Masa komai tayi,shi kuwa yasa Kai ya wuce Bai ko damu da sanin mud din data shiga ba.

Yana karasawa yace Nihila ta shiga motar aikuwa ta shige gaba yaja suka tafi.


Sun Isa makaranta,Nan a mota yake fada Mata ta tsaya tayi karatu sosai, sannan banda kawayen banza,Nan ya Bata kudi ta bude ta fita,ta shige cikin makaranta.

Tana shiga ta shige aji tayi zamanta,inda wadda suke zaune kusa da kusa,ta kalle ta tare da yi Mata murmushi.itama mayar Mata tayi aikuwa ta mikawa Nihila hannu tace,” sunana Aisha sadeeq,Amma ana kirana da Ayusha”.

Dariya Nihila tayi,kafin tace,”Ni Kuma Nihila,Amma Daddy baby yake cemin”.


“Zamu Zama kawaye?”

“Eh mana,daga Nan fa Hira ta barke tsakanin su tun daga wannan Rana Kuma suka Zama kawaye sosai,domin ya zuwa yanzu, kowanne a gida an San sunan Dan uwan sa.


Yau sun tashi a makaranta, Alhaji baya gari,direba ne yanzu yake zuwa daukarta,an Riga zuwa daukar Ayusha,Dan haka suka karasa gurin motar Dan ta rakata duk da yau ba motar da aka Saba zuwa daukar Ayushan bace,suna karasa wa Ayusha tace,”sister leko kiga uncle Dina da nake fada Miki ankusa bikinsa”.

“Ina yini” kawai yaji ance,inda ya waigo Dan ganin me maganar,sosai ya kurawa beauty face dinta ido,ita ko tana gaisheshi Bata ko jira amsar shi ba, bare ta tsaya kallonshi ta hango direban ta,aikuwa ta kwasa a guje tana fadin” sai mun hadu gobe”.

Dariya Ayusha tayi,kafin ta kalli uncle din nata tace,”wallahi uncle inason Nihila kaga tanada kyau wlh”.

Bai Bata amsa ba illa ma juya sunan Daya shiga yi a ranshi,da kissima abubuwa da dama Akan yarinyar Dan ba karya tayimai sosai,sai dai daganinta ballagaza ce!


*Niko nace koma dai wace iri ce to matar aure ce ehe!*


_Alhamdulillah,Allah ya bani ikon dawowa bakin aiki,nagode da kulawarku gareni da hakurin da kukayi Dani,yanzu mun dawo bakin daga a kafta,_


*Alkalamin khady* ✍

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button