Uncategorized

HAJNA 27-28

 ♻️♻️♻️HAJNA♻️♻️♻️

*Bismillahir Rahmanir Raheem*

PAGE 27-28

*************************

A fusace ya nufi motar shi, dan Farween ya kawo mishi dab da maƙoshi, wani yawu ya haɗe da ƙarfi mai ɗaci a gurin shi, sannan ya saka wa motar key, tada ita yayi da ƙarfi, ya fito daga cikin ma’aikatar, shima me gadin gurin ganin Qaseem cikin fushi, yasa be ɓata lokaci ba ya buɗe mishi gate, tafiya yake yana shara gudu a kan babban titi, baya ji baya ganin, dan a yanayin da yake jin kansan in wani be yi wasa ba, tsaf ya kaɗe shi kowa ya huta.



     Ƙofar gate ɗin shi ya tsaya, horn yayi, me gadi ya buɗe masa, danna kan motar yayi ciki, be ma tsaya yayi parking dai-dai ba ya buɗe ƙofa ya fito, Hajna kuwa tana zaune a parlor taji tsayawar motar shi, da sauri ta tashi ba tare da ta tuna shawarar da Trisha ta bata ba, buɗe ƙofar tayi da gudu ta rungume shi, hannun shi ya sa ya ture ta da ƙarfi, sai faɗuwa naga tayi ƙasa, shi kuma wuce ta yayi ba tare da waiwayowa ba, da kallo ta bishi har ya shige gida, tashi tayi ta shiga ciki, ɗakin shi ta shiga, kwance ta same shi ya rufe idon shi, da alama ranshi a ɓace yake, a ranta ta ayyana ko me aka mishi, gaban shi ta zo ta durƙusa, takalmin ƙafar sa ta cire masa, sannan ta fara ƙoƙarin rage masa kayan jikin sa, yana jin ta amma yayi kamar baya ji, kayan da ta rage masa ta kwasa ta ba mai wankin sa, ta bar shi daga shi sai boxers dan ko singlet bata barshi da ita ba, dawowa tayi ta shiga toilet ruwan wanka ta haɗa mishi masu ɗumi, sannan ta dawo ta fara tada shi, dan ita duk tunanin ta barci yake, ƙafar shi ya saka ya ture ta, yanzun ma faɗuwa ta sake yi, a hankali ya tashi, da wani mugun kallo yake bin ta, kafin yace “kar ki kuskura ki sake yi min magana idan kika ga raina a ɓace, wai ke ana takura dole ne?, na faɗa miki ki fita a harka ta, haba! Yarinya sai kace mayya “, tashi yayi ya shige toilet, Hajna kuwa share hawayen fuskar ta tayi ta, tashi ta bar mishi ɗakin shi????, wanka yayi sannan yasha magani dan kanshi na mishi ciwo, ko minti uku be yi da kwanciya ba barci ɓarawo yayi awon gaba dashi.



A ɗaki na sami Hajna sai kuka take yi, toilet ta shiga tayi wanka, kanta yana mata ciwo sosai saboda kuka da ta sha, saboda haka tasha magani sannan ta kwanta, ta jima a kwance kafin ta samu barci ya ɗauke ta, sai da aka yi la’asar Trisha ta, tashe ta.



     Arwala tayi sannan tayi sallah, Qaseem kuwa ne tashi ba sai 5:30 da addu’a a bakin shi ya tashi, arwala yayi, sannan ya fara sallah, bayan ya gama yayi ta istigifari akan jinkirin da yayi na rashin sallah, dan Qaseem duk iskancin shi baya wasa da sallah.


Yau kam har dare Qaseem na ɗaki daga sallah sai sallah ke tada shi kan gado, Trisha ya kira a waya “hello Trisha, i need coffee “ya faɗa yana kashe wayar, tunda taji ya faɗi haka tasan yau ba kanta, dan duk kaji boss ya nemi coffee to tabbas ta ɓaci, kitchen ta shiga ta haɗa masa dan dama kullum sai anyi, ɗakin shi ta shiga a hankali, sai yanzu na ƙarewa Trisha kallo, kyakkyawa ce, sannan tana da hips sosai, dirarrar macece, boobs ɗin ta ( dukiyar Fulani)  manya ne, amma ba sosai ba, fara ce ita amma ba sosai ba, tafiya take yi ko ina na jikin ta na girgizawa, zuwa tayi ta aje masa, “sir your coffee is ready “, juyawa tayi zata fita, “Trisha! I need u, more than the coffee u brought here” (Trisha! Ina buƙatar ki fiye da coffeen da kika kawo nan), “ina da abun yi yanzu, ka bari sai gobe “ta faɗa tana ƙara karkaɗa jikin ta, kallon yadda jikin ta ke motsawa yake yi, yana ƙara jin shauƙi da sha’awar ta har ranshi, yana son Trisha kuma yana so ya aure ta amma Trisha bata so tayi aure, wannan sana’ar ita ce gaban ta, gashi tsoron yake ya tilasta ta, yasan halin Trisha tsaf ta bar mishi gida, “plssss! Trisha “, ya faɗa, ko kallon shi bata yi ba ta fita, cup ɗin da ta aje gefen gado ya ɗauka, tunda ya ɗaura cup ɗin a baki bai sauke ba sai da ya shanye coffee ɗin tas, yana ƙarajin tsanar Farween a ransa, kwanciya yayi, tunanin rayuwa yake yi, tabbas yana mugun sha’awar Hajna, amma yanzu sai ya gama wasa da hankalin ta sannan sai dawo gare ta. 


  Hajna kuwa tunda tayi sallar isha’i ta kwanta barci yayi awon gaba da ita. 


************’


Wata mata ce zaune, wacce a ƙalla shekarun ta za su yi 36,kyakkyawa ce fara, sanye take da riga da wando gashin kanta yasha kitso ƙanana, masha Allah tayi kyau sosai, wasu yara nagani guda biyu sun zo, kamar su da juna ta ɓaci har ya kai ma ba’a bambance su tsabar kamar da su ke yi, da gudu suka faɗa jikin matar dake zaune akan kujera, murmushi ɗauke da fuskar ta tace “katrina and juliana, go and dress up well, we are going out for shopping”(Katarina da juliana kuje ku shirga zamu je shopping) , tsalle suka fara yi suna murna “momy will u buy me chocolate? “julia na ta tambaya (momy zaki siya min chocolate), gaɗa kai tayi tace “oya, u guys should hurry up” (kuyi sauri”, “ok momy” Katrina ta faɗa, murmushi matar da suka kira da momy tayi, sannan tace “ tell Elizabeth to also get ready, we are all going out together “(ku faɗa ma Elizabeth ta shirya itama, tare zamu fita), ds guda suka wuce, a ɗaki suka samu wata yarinya da shekarun ta za suyi 17 a duniya, da alama ita ce Elizabeth, Katrina tace “sister, momy is going out for shopping with us, u should also get ready, she’s going along with us “(sister, momy zata fita shopping da mu, ki shirya duk tare zamu fita”, tashi Elizabeth tayi ta shirya dan dama wanka ta fito shine ta kwanta, wata doguwar riga ta saka iya guiwa, gashin kanta ta gyara wanda yasha kalaba da attach, Katrina ta fara shiga toilet, tayi wanka, sannan Juliana, kaya iri ɗaya suka saka, jeans da t-shirt suka saka, sannan suka taje kan su, suka yi parking, Katrina tayi parking kanta tsakiya, Juliana kuma gefen kai, a parlor suka sami momy da Elizabeth suna jiran su. 




Anan zan dasa aya………….. ✍️


Haɗin gwiwar : Queen Nasmerh & Rabiatul Adawiyya 


ALQALAMI YAFI TAKOBI ✍️♻️♻️♻️♻️❤️❤️❤️❤️❤️❤️


????????️ *ZAMWA* ????️????

( _Zamfara writers _ )

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button