Uncategorized

SAMEEHA F

_????SÂMÊÊHÂ????*_

              (F)


“Cikin wani tafke ken rafi Sameeha ta gan ta a tsakiya,rafin ya dare biyu sai janyota ake da baya Karta fada ramun ta gaba ma ana sake janyota dan ta fada ramun daya rabe gida biyu,”kamar an tashe ta daga barci,ta farka a firgice tana qoqarin yin Addu’a ina bakin sam yaqi buduwa sai nauyi da leɓan sama da na ƙasa da suka ƙara yi ta dubi inda Sameer ke kwance a gefen ta dan ta tadashi.

    Daa saurin ta tamiqe tana mai ja dab

aya ganin shirgegen qaton maciji nannade a kan gadon ya dora kansa tsakiyar jikinsa yana fito da harshen sa waje yana mai da shi kamar zai sareta nan da nan ta shiga ihu tana kiran ataimake ta,,da tayi niyar yin Addu’a sai bakin ya kuma rufewa kamar bata ta6a magana ba a haka har ta sulale qasa ta sume,ba ita ta farka ba sai da taji ana yayyafa mata ruwa me sanyi a jikin ta,a hankali ta buɗe idon ganin macijin tsaye akanta ya fasa kai yana ƙoƙarin yin kanta yasa ta kuma zabura ta miƙe a fusace momy dake kusa da ita tayi saurin saka hannu ta riƙo gam tana faɗin,””


“”Ɗiya ta kalle ni,ni ce momy me ke damun ki,ke Sameeha,Sameeha oh ni ƴasu na shiga uku da yarinyar mutane daga aure sai lalura ka dubi yanda take fusga kamar wata sabuwar kamu Sameer,ke Sameeha dube ni,ni ce momy………ina gaba ɗaya Sameeha ta fita hayyacin ta musamman idan ta dubi sameer dake tsaye yana ƙoƙarin kamata,da ƙarfi ta fusge hannun momy daga jikin ta tayi ɗakin ta da gudu ta banko tana numfashi sama sama lamarin daya sa tayi ƙasa da sauri jikin ƙofar tana zubda hawaye me ɗaci a zuciyar ta ta jima zaune a bakin ƙofar tana jiyo sautin muryar momy da Sameer dake mata kuɗa a kunne amma gaba ɗaya hankalin ta baya jikin ta,,,”a hankali taji wani irin sanyi me daɗi na shigarta lokaci ɗaya taji jikin ta gaba ɗaya ya sauya ƙarfi da kuzarin ta duk sun dawo bakin ta,ta buɗe da mamaki taji ta fara ambaton Allah,da ƙarfi ta cigaba da Addu’o’in da duk suka faɗo mata baki wani hawayen daɗi ya fara sauka a kuncin ta,ta fara kiran”””””


“”Umma,,Umma na …….Sameeha ke ta ambata tana kuka wiwi.



Sameer da momy tsaye suke suna jiyo sautin muryar Sameeha dake Ambaton Allah da ƙarfi momy tayi tayi Sameeha ta buɗe ƙofar Sameeha taƙi buɗewa tana gudun kar ta kuma ganin baƙin maciji jin data gani jiya da yau,ganin Sameeha taƙi buɗe ƙofar yasa momy ta dubi inda Sameer ke tsaye duk ya fita hayyacin sa sai magiya da kiran Sameeha yake ta buɗe taki fuskar sa kamar wanda yayi kuka ya gode Allah ta ce”””


“Sameet.


Sameer ya jiyo ya dubi momy.


“Bari naje wajan malam bashir ya taimaka da ko da rubutu ne abaiwa Ɗiya ta,wannan abun ina ganin kamar da shafar junnu.


Yauwa momy wallahi abinda nake nazari a raina ke nan kika rigani ko ni zanje na amso tunda na lura kamar ni ne bata son gani.


Aa kai ka zauna kaga idan kace zaka tafi taje ta fito ni ba ƙarfi gare ni ba da zan iya riƙe ta yanzu yanzu zan je na amso mata insha Allahu komai zai wuce,ka kula sosai kar ka bari ta fito ta fuce kaga ba zamu bar yarinyar muta ne da lalura ba kar kuma ka kira gidan su ka sanar mu ma zamu taɓuka muga duk yanda za’ayi kaji ka kwantar da hankalin ka My son Very Soon Sameeha zata samu lfy bari na faɗawa Zee kar ta tashi taga bana nan.


      Tom momy Allah ya kiyaye.


Amin,momy ta furta ta dito daga ɓarin Sameeha ko da ta koma nata ɓarin Zee na kwance ko alamar tashi batayi ba da sauri momy ta shirya ta ɗauki abinda zata ɗauka ta ɗauki key ta fuce daga gidan.



       Wata hanya momy tabi wace zata kai ta wani surƙun daji,bata jima da shiga ba ta samu waje tayi fkng moto ɗin ta cikin hanzari ta fito ta haura kan dutsen ta shige……….



      “”Gafar dai hatsabibi uban hatsabibai,gaisuwa gareka sarkin hatsabiban duniya…….””Ki dakata……..karki kuskura ki ɗara daga inda kike………akwai baƙin aljannu tafoyayyu daga nahiyoyi da ƙasashe daban daban,kakkausar muryar ta ambata chan kuma aka kece da mahaukaciyar dariya,momy kam daga inda take bata ƙara gaba ba,bata ƙara baya ba tsaye kawai tayi kamar soja har guntun mutumin mumuna ya bayyana akan buzun sa shi bai kai ƙasa ba,bai kuma kai sama ba,a tsakan kanin sama da ƙasa yake da shirgegen gemun sa daya kusa lulluɓe jikinsa gaba ɗaya,,”numfashi yaja kamar wani ɗan bunsuro ya dubi momy dake tsaye ƙiƙam ya ce””………..


“”Aikin ki na daf da lalacewa tun da har kina bari jiririyar ki ta iya shiga ɗakin ta ta rufe komai zai iya biyo baya,momy ta dubi Sarkin Hatsabibai tace.


“””Tsafi ya dafa maka tare da sa’a,”a ko da yaushe nayi iya bakin ƙoƙari na,na han……………….”babu wani ƙoƙari a cikin sharaɗan dana gindaya miki,akwai ɓoyayyun da suke ƙoƙarin rusa aikin mu akan jaririyar ki idan har kika cigaba da bari tana shiga wannan ɗakin to kuwa aikin mu na daf da lalacewa haka burin ki bazai taɓa cika ba mudin ana samun haka.


Bazan ƙara bari haka ta faru ba ya sarkin hatsabibai meye shirin mu na gaba dan kaucewa saɓani….



     Ga wannan ki tabbata kin bata tasha ta shafa ajikin ta sauran baya ni zaki ji,za kuma kiga aikin sa da idanuwan ki……….ɓata sarkin hatsabibai ya ɓace,momy kam da baya ta fito daga wajan ta dawo motar ta,ta shiga ta tada da sauri tayo gida……..




 



_*By*_

_*Maman Dr*_

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button