BA DON SHIBA HAUSA NOVEL

BA DON SHIBA 51-55

Page 5⃣1⃣ to 5⃣6⃣

WACE CE JIDDAH?

Malam salisu haifaffen garin zamfara ne a wani kauye da ake kira kiyawa,,matar sa ta aure guda daya ce tal halima tun auren saurayi da budurwa sai dai allah bai basu haihuwa da wuri ba,,har sun fara fidda rai da samun haihuwa allah maji rikon bayinsa sai ga halima da ciki,,lokacin da malam salisu ya samu wannan labarin ba karamin farin ciki ya shiga,,mutane ma na taya su farin ciki,,haka sukayi rainnn cikin nan da yake cikin mai laulayi ne sosai halima ta rame sosai tanajin ciwo a cikin jikinta amma bata nunawa saboda bata so hankalin malam ya tashi,,,a lokacin da cikin ya shiga watan haihuwa kuwa idan kaga halima sai ka tausaya mata domin ta kumbura ne ko tafiya dakyar take yinta,,,wataranar lahadi ta tashi da ciwon nakuda cikin dare,,,da sauri malam yaje ya kira ungozomar dake karban haihuwa a kauyen,,,koda suka zo tayi matukar galaiba ta domin ko numfashi bata iyayi sai da kyar,,,dabarun su na tsoffi ta fara mata amma haihuwa shiru azaba kawai take ci..malam yana daga kofar daki amma kamar shine ke haihuwan duk ya hada zufa,,har wajen asuba bata haihu a ba lokacin nan bambam cinta da gawa kalilan ne,,addu’a malam yayi cikin kofi sannan ya shigo cikin dakin,,ungozomar ce ta taimaka masa suka zuba mata a baki wani yana shiga wani na fitowa haka dai suka rinka bata har ta shanye,,,cikin abinda bai wuce minti biyar ba nakudar ta kara tasowa har tafi na farko azaba,,da sauri mallam ya fita ba zai iya jure kallonta cikin wannae halin ba,,,kamar jira take ya fita kuwa kan da ya fara fitowa sai kuma numfashin ta ya fara tsayawa,,,wani nishi tayi da karfi gaba daya yaron ya fado yana canyara kuka,,tunda halima tayi wannan nishin jikinta ya saki alamun ba rai,,daga waje malam ya fado cikin dakin ko ta yaron bai biba ya nufi inda halima take kallo daya ya mata yasan bata da rai,,,cikin tashin hankali ya fara girgiza ta amma inaaa rai yayi halinsa,,,,karar jin faduwar sa kawai ungozomar tayi wadda ke gefe rike da jariri tana jimamin mutuwar halima,,,,da sauri ta aje shi a gefe tayi waje ta kira makota,,,,kan kace me mutuwar halima ta zagayen garin kiyawa kowa nata jimami dan kuwa halima mutum ce ta gari ga son jama’a..masu kuka nayi masu addu’a nayi,,,malam kuwa tun faduwar da yayi bai farfado ba har sai da aka gama hada halima,,,Innalillahi wa inna ilaihir raji’un kalmar da yake ta maimata wa kenan kafin ya samu sassauci a cikin zuciyar sa…dakin da gawar take ya shiga ya tsugunna a gabanta addu’a yake kwararo mata yana nema mata rahamar ALLAH,,,,haka da aka binne ta ma sai da yayi mata addu’a yana hawaye kafin su dawo gida,,,,

haka aka cigaba da amsar gaisuwa har akayi addu’ar bakwai,,anan ne fa aka fara tunanin wa zaa ba muhammad sunan da malam ya sama yaron kenan,,,kowa yayi shiru alamun dai babu mai amasar sa,,,dan kuwa duk yan’uwan malam ne a wajen baida mahaifiya sai kannan uba da yayyen su,,,ita kuwa halima dama marainiya ce,,,,duk cikin su aka rasa wazai ce zai amshi yaron,,ganin haka da kawu iro ya gani,,yasa ya yanke shawarar aura mai ya’r sa TALATU kowa yayh1 na’am da hakan dan kuwa kawu iro duk shine babba a cikin su babu mai masa musu,,,,shima malam ba yadda zaiyi ne,,,a take a wajen akai komai aka gama abinka ga kauye,,,washe gari kuwa aka kawo amarya dakinta,,,

haka rayuwa ta cigaba da tafiya talatuwa bata nuna son muhammad sai malam na nan inko baya nan azaba yake sha kalakala a hannun ta,,,a haka suke rayuwa kullum tana tsanar muhammadu,,

lokacin da muhammadu ya cika shekara 25 tsufa ya kama mallam itama talatuwa haka amma duk da haka zuciyarta na nan da tsanar muhammadu,,shiko kyautata mata yake sosae domin yanzu sana’a yakeyi mallam ya bude masa provision a cikin kasuwar garin,,,ganin haka yasa talatu fara nema masa auren yar gidan kanwar ta ASABE,,,malam ya amince da hakan domin shi yana ganin talatu ba zata cuce shiba,,,

Asabe yarinya ce mara tarbiyya bata ganin kan kowa da gashi,,ba arabi ba boko sai ya yawon tallah da bin shagunan mutane,,,tuntuni take nunawa muhammadu so amma shi gani yake me zeyi da ita basu dace,,,kowa yasan asabe bata da mutunci indai zaka bata kudi tofah zata bika koma ina ne,,,dan bata dauki jikinta da daraja ba,,,da labarin auren ta da muhammadu ya shiga kunnenta kuwa farin ciki tayi mara iyaka,,,dama abinda ake nema ido rufe,,,

ba wani lokaci aka sa me tsawo ba,,,akai auren muhammadu da asabe,,sai rawar jiki take..shiko kallon ta kawai a wulakance domin kuwa bata kawo mai yancinta,,,haka zamansu ya kasance kadahan kadaran da farko asabe kamar zaayi zaman lafiya da ita,,amma ta fara fito da mugayen halayenta bai isa ya sata abu tayi ba ga rashin kunyar tsiya,,gashi bata zama a gida kullum tana hanyar gidan bokaye,,ana haka ta samu ciki farin ciki sosai takeyi shima muhammadu ba’a barshi a baya,,,lokacin haihuwa allah ya bata da namiji akuma ranar ne mallam salisu yace ga garin ku nan,,,muhammadu ya shiga damuwa matuka da rashin mahaifin sa,,amma haka ya fawwala wa ALLAH komae,,ranar bakwai ranar ne sunan muhammadu yace ba zaayi taro ba kuma zai maida sunan malam akan yaron,,,nan fa asabe tayi tsalle ta dire ta ce ba zaa sama danta wannan sunan ba,,magana har gurin manya amma suka goyi bayan asabe,,,haka muhammadu ya hakura tasa ma yaron haladu,,,tun daga nan fa haihuwa ta bude ma asabe,,bayan shi yara uku ta haifa duk mata,,indo,rabi,da ma,u,,,,yara sun taso kamar uwar su basu da kunya duk abinda sukayi sai dai asa musu ido dae kuwa baa dukan ya’ya’n asabe,,,

ana haka ne allah ya hada malam da fatima kallo ya mata alla ya jarabce shi da kaunar ta,,fatima yarfulani tallan nono takeyi ita da yayyenta d,,,fatima yarinya kyakkyawa er kimanin shekara15 bata da hayaniya ko kadan ga hakuri,,,muhammadu bai tsaya wani jinkiri ba ya gabatar da kansa a wajenta da iyayenta,,,,duk sun amice dashi dan haka yaje ya fadawa kawu iro……

da kamar wuya….

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button